
Safiya kuwa suna Cikin Hira da Abba Barci ya kwasheshi sai ta Kyaleshi ya Huta Daman barcin yana da kyau Sai ta Fada Kitchen taga Abunda Zata Dafa ta iske Nikakken kayan Miya a Cikin Fridge sai ta Dauko tace bari Tayi White rice da Miyar Kaza Tunda Taga akwai kazan Har da Ganyen Kabeji,nan da nan ta kunna Gas Din Duka Guda Biyu ta Dauko Tukunyar ta Fara aiki Cikin Natsuwa da Kwarewa aranta Tana Sakama Mommy Albarka Data Koyamata Aikim mata da yau Da aure ya kawota Wannan Ahalin da suke Bukatar Taimakonta bata san yadda Zatayi ba.
Tana Cikin Aikin ne Taji Abba na kiranta da Sauri ta Dauraye Hannayenta ta Fito Tana amsawa Abba ya Kalleta Lokacin Daya mike Zaune yana Fadin”Barci ne ashe ya Kwasheni.?
Safiya tace”Eh Abba..Nace ai gwara ka Huta Saboda mgungunka ne Akwai na Barci..!
Abba ya kalleta kafin yace”Badai wani aikin kike ba Daugther…?
Safiya ta Dukar Dakai tana Fadin”Ba wani aiki bane Abba abiincin da Za”aci nake Dafawa Munari taje makaranta In ta Dawo ta gaji kuma Ai Zaka ta zama da yunwa ne kai da kake Shan mgunguna..!
Abba ya Girgiza kai yana Fadin”A”a gaskiya Dana sani bazan bari kiyi wani aiki ba..Jiya fa aka kawoki gida nan..Sam bai kamata ba Da baki Damu Dani ba ko Tea sai ki bani nasha..Nasan yusuf bazai shigo hakanan ba..!
Mirmishi kawai tayi tace”Bakomai Abba..Miye amfanina na..? Indai ka Daukeni Tamkar Munari to ka samun Albaeka kawai..!
Cikin kada kai yace”Shikenan Daugther Allah yayi miki Albarka Allah ya jikanki Kamar yadda kike jin kaina..!
Cike da Farinciiki ta amsa da Ameen Kafin tace”Bari na koma na karisa Abba..!
Ya amsa mata da To shikenan afito Lafiya,Cikin Sauri ta koma ta Cigaba da aikinta Cikin Kwarewa.
Cikin Lokaci ta kamallah Daidai Lokacin Dataji ana ta kiran Sallar Azahar Aranta ta kudiri Niyyar Dawo da Farincikin wannan Ahalin,Ta Lura Daga Yusuf din Har Imran din ba wanda ke Zuwa Masallaci Bin Jam”i,Da sun Shigo Shikenan Ballatana su Rika Tafiya da Abba Gaskiya Hakan bai kamata ba,Suna Musulmai Ya zama Wajibi su Rika Sallar Cikin Jam”i Zata Gayama Yusuf Gasikiya su gyara Sallarsu.
Sai da ta kamallah komai ta Juye komai a Flask,ta yanka Ganyen sai dai Bata Hada ba ta bari sai Zuwa anjuma,bata bar Kitchen din ba sai da Ta Goge komai sai Ta Fito Taga Abba Baya Falo Kila ya Shiga Ciki yayi alwala ne itama sai ta Shiga Daki ta Fada Tiolet Tayi wanka Saboda Girkin Datayi Tazo ta Sauya kaya Dole zata gayama Mommy A hada mata kayanta Waje Daya in sukaje ita da Yusuf Zata Taho da Abunta wata Doguwar Riga ta Samu ta saka Kirar Armani ta Saka Mayafinta Ta Tada Sallah Tana Cikin Sallar ne taji Abba na Knooking Din Kofa Lokaci Daya yana Kiran sunan Imran Tanaji yazo ya Bude Abba na Mgana bataji me yake Fade ba sai taji Abba na Buga mata Kofa Lokacin ta Sallame sai tazo ta Bude Abba ta Gani Harda Hulansa da Casbaha yayi mata Mirmishi yana Fadin”Daugther na taso Imran nace ya Rakani Massalaci Shima mu Fara Salla Cikin Jam”i Kamar yadda kikace..!
Safiya ta Fadada Mirmishinta kafin Tace”Ka kyauta Abba..Adawo Lafiya..!
Tafada Tana Hangen Imran Din Daya Sanya Wata riga sai dai ya Sauya Wando Dogo ya Sanyo karo na Farko da Abba zai Fita da Kafarsa Tun Bayan Dawowaarsu kano gwarama Imran yana Tsayawa masallacin kusa da Gidansu Sagir yayi Sallah in dai yana Waje in ya Shigo kuma Shikenan Ammh yau da Abba ya Bukaci Haka sai yaji Shima Zakwadin Abun Acikin Ransa ya kuma Kuduri Niyyar Daga yau Dagashi Har Abba da Yusuf indai suna Gida Masallacin Kusa da Gidan su Sagir zasu Rika zuwa Sallah acikon Ransa yana Kara Taya Yusuf Murna Na Samun mace irin Safiya aransa yana Ayyana Bata Dauko halin Tsohon najadun uban ta ba.
Har suka Fice Bakin Safiya yaki rufuwa Waya ta Dauka zata Kira Yusuf Saima taga Kiransa Da yawa ya Kirata Kila Tana Kitchen ne,Nan da nan tabi bayan kiran sai dai bai Daga ba sai ta kyakeshi sai Zuwa Chan ya Kirata ta Daga Cikin Farinciki yana ma Tambayanta ina ta Shigene ita kuma Saboda Murna tana Fadamai Abba yau ya Fita masallaci Shi da Imran Yusuf Yana Office dinsa kenan Shima Dawowarsa Daga masallacin Ma”aikatansu kenan yakai goshinsa kasa yana Jeromaa Allah Godiya Farinciki Sai da yayi kwallah yama kasa Mgana Cikin Muryan Sanyi da Farinciki yake Fadin”Tanque…Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki albarka Shigowarki Gidanmu Haske ne..Daga yau kin tashi Daga Babe na kin Koma Noor!
Cikin jin Dadi tace”Nagode My Dear..In zaka Dawo ka Taho da Jaridun da Littafan da mukayi mgana..!
Yace”Insha Allahu..Mai zan Taho Miki Dashi..?
Da Sauri tace”Bana Bukatar komai Illah Son ganin ka Dawo Cikin Koshin Lafiya..!
Cikin Annuri yace”Shikenan Sai na Dawo Take Care Of Ur Self..Zan Taho muku da Abinci..!
Da Sauri Safiya tace”Daga jiya kagama Siyan Abinci My Dear.
bai samu ce mata komai ba Farinciki ya Cika ransa Daganan sukayi Sallama.
Banganran Abba kuwa kamar Sabon Mutum haka ya koma yau ya Fita Waje yaga anguwan Dayake Rayuwa,,Iro megadi yasha mamaki ganin Imran da wani mai kama dashi da Yusuf Baki ya sake kawai Domin bai Taba Zaton akwai wani agidan ba Sai dai ko ba”a Fadamai ba zai iya Cewa Mahaifinsu Imran ne Daman suna da Uba..? Shifa ya Dauka Daga su Sai su acikin Gidan,Dayake Yusuf ne ya daukosa Gadi,Shima din Security din Ma”aikatansu ya ma mgana Shine ya Samo mai Iro,ba Saboda komai ba sai Saboda Abba suna Fita su barsa Shi kadai ga kuma Gida watarana Ake ji Tunda yanzu Mutune bana Allah.
Abba ya bama Iro Hannu suka Gaisa Cikin Fara”a Ganin kallon da yake ma Abba ne yasa Abba yamai Bayani da kansa Mamaki ya Cika Iro Cikin mamakin yace”Ammh Ranka ya Dade Alhaji ban taba ganin ka Fito ba Tunda Nake agidan nan..?
Abba ya Murmusa kafin yace”Eh ai Tun Dawormu bani Da Lafiya Likita ke Zuwa Gida yana Dubani..!
Iro yace”Kwarai kuwa anyi Haka..Likita kuwa na zuwa Lokaci Bayan Lokaci Ai bansani bane Sannu Alhaji Allah ya kara Lafiya..!
Abba ya amsa da Ameen Imran kuwa Gaba yaci yana Fadin”Abba an fa Tada Sallah..! Abba yabi bayansa yana Fadin”Mu zamu Tafi Masallaci..!
Iro yabi su da adawo Lafiya har suka Fice yana mamaki da Karin Al”ajabi A fili ya Furta”To wannan wani irin Cuta ce ashe Mutum Fin Shekarq bai Taba Fita ba..? Kuma naga Kafarsa Lafiya lau Oh..Ni iro..!
Haka yayi ta Fadi mamaki dai yaki Barinsa.
Haka achan masallaci ma Bayan an Idar da Sallah Sagir yaga Abba da Imran Daga Baya Dayake da suka Zo an Tada salla har anyi Raka”a Daya sai suka Tsaya Baya Tunda gaban ya Cika Bayan an idar suka Rama Sallar Farkon Abba na Zaume Bakinsa yaki Rufuwa sai da ya Share kwallah Mutane kuwa basu Damu ba Duk da basu Taba ganinsa ba suna Tunanin baki ne a anguwan Tunda ai Gari da Yawa Sagir ne har Zai Fice yaga Imran sai Chan yaga Abba Cikin mamaki yazo ya gaida Abba ya amsa mai Cikin Sakin Fuska Yana Fadin”Sagir ko..?
Sagir ya gyada kai Abba yace”Mu je Wajen masallaci..!
Mikewa sukayi suka Fice Abba kuma ya Tsaya gaisawa da wasu Daga Cikim Masallacin Sukuma suka Fita Waje Sagir ya kallesa yana Fadin”Abba ya samu Lafiya har ya Fara Zuwa masallaci..Na tayaku Murna Abokina..!
Imran ya jinjina kai batare Da yayi mgana ba sai ga Abba ya Fito suka kara gaisawa da Sagir,yana Tambayan Mama yace ya gaisheta,Tare suka Jero har Zuwa Bakin gidansu Sagir din ganin ya Tsayane yasa Abba ya Tambayeshi nan ne gidansu yace Sagir din ya nuna mai Shagosa Abba ya saka albarka Daganan sukayi Sallama ya koma Shagonsa Cikin Mamaki acikin Ransa yaji Dadi Sosai.
Safiya na Jera Flaks,kan Dinnig Su Abba suka Shigo da Fara”anta Tayi musu Maraba Imran dai Bai ko kalleta ba ya nufi Hanyar Dakinsa sai yaji Tace”Arm nace ba..!
Ya juyo yana kallonta Tacigaba da Fadin”Nace ga abincin fa..!
Imran ya kalleta kafin yace”ke kikayi Girki da kanki..?
Mirmishi Tayi batace komai ba Abba Dake Zaune yace”Ni kaina sai da na Hanata ta Dage sai tayi..!
Imran bai ce komai ba bayaso yayi mata gaddama Saboda karamcinta sai ya Kada kai yace”Later Zan ci..!
Kai ta kada mai Shikuma ya Shige Dakinsa Shirya komai tayi kan Dinning din Harsu Filet sai da ta Jera Ta je gaban Abba ta Durkusa Tace mai ga Abinci chan Abba ya rasa bakin mgana sai saka mata albarka yake karon Farko Daya Taba Zaman Dinning,ba kan gadonsa yaci Abinci ba Ita Safiya ita ta Yi Serving Dinsa ta Hadamai Cowslow daidai wanda Zai ci,Ta Daukomai Ruwa da Lemo Zata Tafi yace ta Zauna itama ta Zuba taci Duk da tanajin kunya ta kasa ma Abba Gardama Dole ta Zauna itama taci Sosai Abba yaci Abincin Sosai acikin Ransa yana sakama Safiya albarka.
Ranar Wuni yayi afalo Salla kadai ke Tadashi Safiya na Tare dashi suna Hira Kamar sun saba.
Yana bata Labarin Kazar kazar dinta kamar Asma”u Safiya Taji Rauni ya kamata ganin Abba na kuka ita Tayi ta Lallashinsa Tana kara Numamai Mutuwa ta Allah ce addu”a kadai suke Bukata,Abba ya Share Hawaye yace”Hakane Daugther Allah yayi miki albarka..!
Daga yau Addu”a ne Tsakanina da Matata da ya”yana Allah ya jikansu..!
Safiya ta amsa da Ameen.
Sai yamma Munari ta Dawo itama ganin Abba haka yasata Farinciki taRumgumesa Tana Murna ya gayamata yau Har Fita yayi Yaje masallaci,Kuma Duk Sanadin Safiya Munari ta Rumgume Safiya Tana Fadin”Thank u Bhabi..!
Munari bakinta yaki rufuwa ganin Dinnig Da kololi Shake da Girki ta Buga Tsalle Saboda Murna Abba nata Dariya sai kuma tarufe baki Sanin Halin ya Imu kada ya jita kuma ya jitan bai dai Fito ba Tsaki yaja acikin Ransa yace”nonsesss..!
Sai da taci ta Koshi Tana Santi
Daganan Munari ta jata Dakinta,Suka Zauna suna ta Fira tana ta Bata Labarin Makaranta Sai da aka kira mangariba ta barta ta koma Dakinta ta Sake wanka,Ta fito Tana Sallah Yusuf ya Shigo Gidan
Ya Tarar da Abba da Imran suna Masallaci.
Bai gama mamaki ba sai da yaga Aikin da Safiya Tasha Da Labarin da Abba ya bashi na Safiya yadda suka Wuni Hira yau ya ma kasa mgana Saboda Farinciki.
Yau agidan Rana ta Farko da suka Hadu Saman Dinning suka ci Abinci Munari da Safiya sun kara Shiga Kitchen sun yi Ferfesun kayan Ciki Imran Shima ya Fito Ferfesun Yaci kadan Yasha Ruwa ya koma Daki Abba Dai yaci Sosai,Da Yusuf da Munari bayan sun gama Suka koma Falo suka Dasa Hira Yusuf ya Dauko Jaridun Daya Siyoma Abba masu yawa Tundaga na Watan Daya gabata sai Littafan addini su azkar,Muwada Malik,Buhari da Musulim
Da Qur”ani izifi Siitin Karami na Karatu Abba ya Karba yana ta Godiya Safiya tace Saura Medicated glass Wanda Abba zai Rika sakawa in zai yi karatu Saboda karamai karfin gani.
Yusuf yayi na”am da Mganar Hatta Abban ma Saboda Zama Waje Daya Raunin Idanuwansa sun Ragu.
Da Sallar Isha”i Abba da Yusuf da Imran Tare suka Fita Masllaci Sagir Sai da ya bama Mama Labari Bakinsa yaki Rufuwa ita kanta Mama tayi Farinciki,Inteesar na gefe Tana Latsa Wayarta bata Saka musu baki ba Tunda ba da ita suke mgana ba.
Yusuf kuwa sun kwana Farantama juna Rai shida Safiya sun Riga sun zama Daya ya gama Gudartama Ransa Cikin Satin nan da anyi musu Albashi Zai Kwashe ya Dauketa suje ta Zabi Furture,da Zasu zuba ashashen da Zasu Zauna,Sai kayan sawanta Bayaso Wani nata yazo ya ganta tana Zaune a Dakinsa Hakan bazai mai Dadi ba Wlh Iyayenta sun gama mai komai da suka Kawo mai Haske acikin Gidansu.