GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Cak yaTsaya yana kallonta ganin haka yasa tace”Eh Anty Safiya Budurwan Ya yusuf…Itama..Itama..”ITAMA ME NE.! ya katseta Cikin Tsawa da Bala”i Yusuf ya kalleshi ganin yadda Munari kerawan Jiki yace”Kai fa Sakarai ne..Itafa macece kayi mata ahankali mana..”Jajayen Idanuwansa ya sakarmai kafin ya Bushi Hayakim Taba ya Fesamai yana Fadin”Ai tama fika Jarumta malam..’Yafadamai yama kallonsa karamin tsaki yaja ya Mike yana Fadin”Kada ka sake naji ka taka kaje gidansu Safiya kaji ma nagaya maka..”Daga hakaya juya zai tafi Imran ya Daki Kirjinsa Har sai da yayi kara Lokaci Daya yana Fadin”Itama sunce baazasu baka ba saboda muna Rayuwa agidamu bamu da Mace aciki..? Abban mu ya Haukace ni kuma ina Shaye Shaye ko..? Itama sun kara hanaka keman duk da Tarin Nasabarka Kafa fini Hankali Da Tunani meka rasa da zaka Dinga Neman aure ana hanaka..?
Yusuf ya tsaya Cak yana Jin wani Kukan Zucci Cikin Sanyinsa yace”Bamu rasa komai ba Face KWARIN ZUCIYA..”
Da mamaki Imran da Maimuna ke kallonsa bai waigo ba ya Cigaba da Fadin”Mun rasaa kwarin Zuciyan da zamu karbi kaddaranmu mu Cigaba da Rayuwarmu Tamkar kowa..Tunda Kaddaran nan ta Fadamana muka rasa komai Abba ya Koma haka Imran ka koma yadda kake ni kadai ne nake kokarin Tsayuwa da Kafafuna din ma na gaza Domin Kune kwarin gwiwata da komai nawa Domin ku kadai ne ahalina anan Duniya..”Ya karishe Fada Yana Sharan kwallah

Imran ya Busa Taba mai tsawo Har sai da Hayakin ya Cushemai Zuciya ya Fara Tari da Sauri Yusuf ya Nufeshi yana Fadin”Kagani ko..?kaga irin Sakarcin ka ko..?baka da Lura ne ka rika Zuka a hankali mana Tunda ta zama ibadarka..”Da hannu ya Dakatar da Yusuf kafin ya Bude Manyan idanuwansa da suka kara zama Ja saboda Hayakin Daya taso mai Daga kai ya Nuna kansa yana Fadin”indai Ni IMRAN wanda ABUBAKAR MALAMI ya Diga kwansa ZUWAIRA Ta Haifeshi adoron Duniyanan sai na Aura maka Safiya..Ko Ubanta ya yarda ko bai yardda ba don Uwatai..”Yafada yana kara Nuna kansa da kuma Dukan Kirjinsa kafin ya Take Taban Hannunsa ya Murjeta da kafansa ya wuce yana wani Tafiyar Takama yusuf ya Shiga kwalamai kira yana Fadin”Imu..? Imu me zakayi kada ka kaje ka Karya mata Uba kamar yadda kayi ma Kawun Asmee fa..!
Imran na jinsa Mirmishi kadai yayi a Hankali ya Furta”Ka bani Shawara ya yusuf Tanque..”Yafada Lokaci Daya yana Shigewa Dakinsa Yusuf ya Dafe kansa yana Fadin”Munari meyasa kika gayamai..? Kin fi kowa sanin zai je yayi act din sa Stupit kamar yadda ya saba..!
Marairaicewa Tayi zatayi mgama ya Dakatar da ita da Fadin”Muje mu karya na kai School kin makara..”Da sauri ta Mike tana Fadin”Nayi missing din Lecture din Dr Sa”idu..”
Dinning suka nufa ya zauna Tayi Serving dinsa Tea kadai ya sha da Soyayyan Dankali itama haka basu jima ba suka tashi Daki ya koma ya Dauki key din Mota Ita kuma ta kwashi Littafanta da Jakarta da mayafinta suka Fito Haraban gidan Sun Shiga Motar kenan Yusif zai yi Rivers sai ga Imram ya Fito ya Tsuke Cikin Riga da wando Duka bakake ya saka P.Cap ga wani Bakin katon Gilashi Daya kwafa fuskarnan ba Annuri Kafarsa Sanye Cikin wani Bakin Booth din Takalmi yana ganinsu yayi kamar bai gansu ba,Bakar mashin dinsa Roba roba Dake fake a Haraban gidan ya Hau Lokaci Daya yayi mata Key ya Tada ita yana Zuba Hon Iro megadi Dake Tsaye Daman Tuni ya wangale get din sanin Hali Yanzu sai yasha mari Imran bayason Jira sai da ya Fice Daga gidan kana suka Fita suma suna Tafe Yusuf na Tunanin kada Imran yaje gidansu Safiya yayi musu Haukanshi har ya sauke Munari bai da walwala Daga nan Gida ya Dawo saboda Abba,ammh Gabadaya Zuciyarsa bata Natsu da Fitar Imran ba yasan sa Kaifi Daya ne in yace Zai yi Abu sai yayi shi yaso kiran Safiyan yaji ko yaje..?Sai kuma ya fasa Domin Cin Zarafin Da babanta yayi mai Jiya bai fatan ta sake ma ganinsa Har Abada.

Ya kukaji salon wannan Mikakkiyar Tafiyar tamu..? Bamu ce komai ba bamu Fara Wannan Tafiyar ba har yanzu..Ku yi Kyakyawan Sharhi bayan kun yaba kun kuma danna min Kararrawar Voting ni kuma nayi alkawarin Sanya ku nishadi da wannan Labarin mai amon Sautin tafiya da Zuciyar mai karatu..!

Comments
Share
Vote
10/02/2022
Shakira…
IWA
3/22/22, 23:02 – Ummi Tandama😇: GIDANMU..!
(Our House)
Book1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

DEDICATED TO:
Aisha alto(Sisinah)
Chubado muhammad(Uwar dakina)
Yahanasu Soupnass(Qawalli1)
Kausar salis(My jika)
Rahma Ladingo(Dota)

            *🅿�2*

“Daga gidansu gangarawa yayi Chan kasan Layinsu bai tsaya ko”ina ba sai Kofar wani Shago mai Dan girma inda aka Rubuta DA KUDI AKE NEMAN KUDI TAILORING CENTER ababban Allon Dake kafe a kofar Shagon.

Yana Tsayawa ya zura hannu Cikin aljihun bakin Wando Dake Jikinsa ya zaro Tabarsa da makunninta ya kunnata ya Busa ya Fesar da Hayaki Cikin Shauki kafin ya Danna Hon din mashin din da karfi kamar Zai fasa ma Mutane Dodon kunni.

Shigowarsa Shagon kenan yana Duba yaransa da kuma Sallahu wasu Dinkuna da zai basu yana da Lacture karfe 10am cikin makaranta zai shiga yana Cikin yima Babban yaransa Auwal mgana sukaji wannan Gigigitaccen hon din Imran ya cika musu kunni Dafe kai yayi Lokaci Daya ya juyo yana kallon Kofar wajen inda suka Hada ido suna kallon Juna.
Karamin Tsaki yaja kafin ya juya yana kallon Auwal yace”Don Allah Auwal kuyi kokari ku gama Kafin Dare..Yau da Daddare Hajiya zata aiko Direbansu ya karba..”Auwal ya gyada kai Daidai lokacin da Imran ya kara Danna Hon din da karfi,kansa ya kara Dafewa Cikin Takaici ya Furta”Ya illahi..”Auwal Dake Dariya yace”Oga sai fa ka Fita..In ba Haka zai cigaba ne kasan Halin yan kayanka..”ya karishe Fada yana Dariya shi da Sauran yaran Shagon wani Daga chan yana kan keke yana Dinki yace”Imran kenan..Abokin Oga ko nace Amini ayi Fada aShirya hukuma sai da Lallashi..!

Yana Jinsu bai yi mgana ba sai dan Mirmishi da yayi ya Taka ya Fice Daga Shagon yana Fitowa ya kallesa yana Fadin”Kai wai meyasa kake hakane..? Ko yaushe kazo waje sai ka bada alamun kazo..”Imran ya kalli Abokinsa SAGIR,ya zuki Tabansa ya Fesar da Hayakin kafin cikin Wata murya mai cike da gadara yace”Da kudi ake neman kudi Abokina..Taken ka kenan..”Karamin Tsaki Sagir Yaja kafin yace”Naji..Ya akayi ne..?Ya jikin Abba..?
Imran ya Sauke Kafarsa Daya Dora Saman karfen Mashin kasa yana Fadin”Lafiya..Hau muje..”Sagir ya wani kallonsa ShekeSheke kafin yace”Na hau muje..? Ina kuma..? Idanuwansa ya sakarmai Kafin ya wana Mashin Din tayi Jinjin cikin Dakiyarsa yace”Malam ka Hau muje nace ko..’?

Yafada Cikin alamun ya Fara Fusata Shima Sagir din Cikin Zafinsa yace”Ni kuma nace na hau muje ina..? Wani Wawan Harara ya Jefeshi Dashi kafin yace”Zan je na kai kanka ne Domin nayi Cininkinsa..”Karamar Dariya Sagir yayi kafin yace”Ina karyanka Wlh..Kaina yafi karfinka..”Wani mirmishin Rainin wayau Imran ya saki kafin yace”Naji..Ka hau Muje kafin Raina ya baci..”Sagir yace”Muje ina wai..?Nifa daga ganni nan Lacture gareni makaranta zan shiga..”Imran yaji kamar ya Kifamai mari Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Zati ya kalli Sagir yana Fadin”Zaka hau ko bazaka Hau ba..?
Yafada yana Tsareshi da Jajayen Idanuwansa Sanin Halinsa yasa Sagir din ya Taka ya Hau Bayan Mashin din Dariya Imran yayi kafin yace”Da kada ka hau kagani..”Sagir yace”me zaka iya..?Kai dai Nayi niyar Hawa kawai malam..!
Imran bai yi mgana ya Taka Mashin suka Fara Tafiya Gefe Daya kuma yana Tuki yana Busan Tabansa da Dayan Hannunsa Sagir na Baya yama kasa mgana,ganin yana ta Tsula gudu yana neman kadasu yasa ya Tanka.”Kai malam in ka Shirya mutuwa ne ni ban Shirya ba..fakani gefe ka saukeni sai kaje ka Tari Mutuwar kai kadai ba..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button