GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina godiya Masoyana na Nesa dana kusa Masoyan Imu da Intee Suma sunce suna Godiya sosai Allah ya saka da alheri..

Shakira…
3/22/22, 23:05 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

           🅿�20

Inteesar da Munari na wucewa Imran ya Fito daga cikin Shagon Sagir ya Tsaya a kofar Shagon ya Fito da Sigari Guda Daya ya kunnata ya Cigaba da Zuka yana Fesar da Hayaki.
Sagir ne ya Fito Daga Cikin Shagon Nashi Ya isa kusa da Imran yana Kallonsa Cikin Wani yanayi kafin ya Rausayar da kansa yana Fadin”Yau Kuma a waje ake son Busa Hayakin..?
Imran bai ma nuna yasan da Wanzuwar Sagir a wajen ba Ya cigaba da Busa Hayakinsa,Sagir ya kara Kallonsa yana Gyada kai kawai.
Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace”Kawai yau naji ina son na Busata a waje ne..!
Sagir yace”Dahaka kake yi da baka Takurama yaran Shago na ba..kasan dai Tun Fara zuwanka Shagon nan Kake Takura musu ko..?
Imran ya wani Mele baki Lokaci Daya yana Sauyama Sigarin nasa Hannun Zama kafin yace”I know..!
Sagir ya kallesa Cikin mamaki kafin yace”Ka sani kace..?
Imran sai da ya Fesar da Hayakin Daya Busa kana ya Bude baki yace”To ni zan Hana Zuciyarsu yin Abunda Tagama Da Gangaar jikinsu ne..Ban isa na sa su soni ba..Ban isa na Saka musu Ra”ayina ba sai dai na Isa na Hana su yin Abunda ni zai zama Takura gareni..!
Sagir na Shirin mgana Imran ya Katseshi da Fadin”Har da kaima ai na Lura kamar na Takura maka ko..?
Sagir yace”Ai ni ba tun yanzu ba ka Dade kana Takura ma Rayuwata..!
Imran ya tsaki karamin Tsaki yana Fadin”Halin Dan adam kenan yanzu da ban rika zuwa ba sai kace naki Karban mganarka yanzu kuma ina Zuwa kana neman gayamin mgana..!
Yafada Cikin nuna jin Haushinsa Da Sauri Sagir yace”To daka karbi mganata Ka fara koyan Sana”an ne. ? Tunda ka Fara zuwa baka komai sai dai ka Zauna kana bin kowa da kallo in ka gaji ka Busa Hayaki gayamin me ka Koya..? Imran ya saki kayattacen Mirmishin da yakan Dade bai yisa ba
Kafin ya bude baki yace”Waya Fadamaka ban fara koya ba..? Tun yaushe ai ma nayi nisa da Fara koyon Dinki!
Sagir ya wani kalleshi a karkace kafin yace”Bangane ba..? Ta ina ka Fara Koyon..?me kuma ka Fara Koyan..?
Imran yace”Abunda Kake koyama Mutane mana Inace ba yanka Dinki bane da Hawa keke da Dinkawa bane..?
Sagir yayi Dariya yana Fadin”Sannu Mallam Riga maasllaci To ai ba Haka kaga kowa na Koyon Dinkim ba balle kace..!
Imran yace”Ai ni sunana Imran..Kuma Dabam nake da kowa..Kaganni nan da Kwakwalwata nake Koyon Abu bana da Bukatar Rubutawa ko Gwaji..!
Sagir ya kallesa kafin yace”Uhm..wai me ma ka karanta ne a makaranta..?
Imran na kallon Sagir Cikin ido kafin yace”Daman na taba Fada maka nayi Karatu ne..? Sagir yace”Ko baka Fadamin ba yanayinka da Tsarinka na Masu Ilimi ne sai dai in baka son Fadamin..Dama nine na Daukeka Abokina kuma Dan”uwana kai baka Daukeni ba Imran..!
Sagir ya Fada Cikin Wani yanayi Da Imran yaji wani iri,Baki ya Mele kafin ya Saki karan Sigarin Dake hannunsa Data kare,Ya saka Rufaffan Takalminsa ya Take ta Kafin ya Laluba Aljihun wandonsa ya Dauko Wata ya saka Lether ya kunnata Sagir Duk yana kallonsa Kai ya Girgiza kafin yace”Don Allah ka Rika Dagama Shan Sigarin nan kafa..Ba Saboda Komai ba sai Saboda Lafiyarka Imu.!
Imran yayi kamar bai jisa ba sai da ya Busa Hayakin yaji sa ya ji Daidai kana ya Fesar da Hayakin har zuwa Fuskar  Sagir wanda ya kauda kai yana Fadin”Bana son Wulakanci fa..kan Fuskatane wajen Fesa Hayakin Sigarin naka..?
Imran ya karkace kai yana Fadin”Kila..!
Daga haka ya Tsuke Bakinsa Sagir ya Bata Fuska yana Fadin”Au kila ko…?Nagode ai ba sai ka ganni ba ballatana kamin Wulakanci..!
Ya juya zai koma Shagonsa yaji Muryan Imran din yana Fadin”Ka Tambayeni Mena karanta a makaranta ko..?
To Accounting na Karanta Nayi Degree na Farko Har zuwa Master..!
Sagir Daya Dawo da Sauri lokaci Daya yana Zaro Ido Cikin Mamaki yace”Are u Serious..!?
Imran bai bama Tambayarsa Muhimmanci ba yace”A University of Ibadan IU,nayi duka Karatuna..!
Sagir da mamaki bai gama Sakinsa ba yace”To meyasa kake Zaune baka Nemi aiki ba..? Ko baka samu bane..?
Imran ya wani kallo Sagir a Dakune kafin yace”Nayi aiki da Gt Bank Reshen Jahar Lagos a baya..!
Sagir ya kara Sandarewa da mamaki Baki ya Bude Kafin yace”Kai din nan Ashe ma”aikacin banki ne Ban taba Sani ba Imran..!
Imran yace”Bagashi ka sani ba yanzu..Sai me..?
Sagir ya Dafasa yana Fadin”To meyasa ka bar aikin ka..?kenan in Hasashena ya Zama gaskiya ku a Lagos kuke kuka Dawo nan da Zama..!
Imran ya kalli Cikin Idanuwan Sagir kafin yace”Eh..!
Daganan bai kara cewa komai ba ya Cigaba da Shan Sigarinsa yana Fesar da Hayaki Sagir da ke Tsaye yana  kallonsa Cike da mamakinsa Sosai akan Fuskarsa Kafin ya kara Gyara Tsayuwa yana Fadin”Ammh Tambayar Data Dade tana DAmuna ban samu amsarta ba..Shin Meya Baro ku Dachan Lagos din kuka Dawo nan..? Kuma meyasa kabar aikin kazo nan ka Zauna baka da aiki sai Shan Sigari..!
Imran kamar bazai ce komai ba sai chan yace”Is a long Story..!Kila zaka san Dalilin Watarana Ammh Not Now..!
Sagir ya Bude baki zai yi mgana kenan ya hango Inteesar Tana Tahowa Cikin Natsuwarta Kura mata ido Yayi yana Tunanin kila Daga gidansu Imran Take ganin inda Sagir ya Shagala da Kallo ne yasa Imran Shima ya Waiga yana kallon inda yake kallo,Daidai Lokacin da Inteesar din ta Iso kofar gidan Tana Dago kanta sai Cikin na Imran kamar ko yaushe alokaci Daya Zuciyoyinsu suka Buga alokaci Daya gaban Inteesar ya Fadi Ras Data ganshi,Abun kuma Daya kara Bata mamaki ganinsa Dauke da Sigari yana kallon Cikin Idanuwanta yana Zukan Hayakin yana Fitar da Hayakin ta Hanci ta baki sai ta kara Jinjina al”amarin Tana Shirin Saka Hijabintata Toshe hancinta Ta Tuna da Abunda ya Faru sai tayi Saurin Maida Hannunta da Gudu gudu ta Shige Cikin Zauren Gidansu Sagir Tana maida Numfashi.
Imran ya Bita da kallo Cikin mamaki kafin ya Saki karan Sigarin Hannunsa Zuwa kasa ya saka Takalminsa ya Take ya murjeta Lokaci Daya yake Fadin”kalli yarinyar chan saboda Ta Rainani..In ta ganni tana guduna…Kamar Taga wani Dodo. ?
Sagir Dayake Lura da abunda ya Faru yace”Ba Dole ta rika Gudunka ba..Taji Labarin kana Sumar da Mutun indai ya Shiga Hannunka..!.
Imran yayi Tsai da idanuwansa da suka Kamkance suka Sauya Launi Saboda Busa Hayaki yace”Ina sumar wa..? Uban wa na taba Duka Har na Sumar dashi..?
Sagir yace”To ni ina zan sani..?Nima ita ke Fadamim..!
Imran da Ransa ya Fara Baci yace”Mganar banza..!
Daga haka kawai ya juya cikin Takunsa na Sassarfa da Jarumta ya Fara Tafiya Haka kurum yaji Zuciyarsa na tafasa Sagir ya Bisa da Kallon Haka kurum yake Tunanin Hanyar da Zai Taimakama abokinsa wajen Dawo da Rayuwarsa ta Baya ta Inganta yabar wannan Rayuwar Dayake Ciki.
Shikuwa Imran koda ya karisa Gida ko Gani Dakyau bayayi saboda Tsabar Bacin rai,Yana Shigowa Falon ya Fara Kwalama Munari kira Cikin Tsawa da Hargowa.
Abba na Tsaye a Falon yana gyara Zaman Hulan kansa da Casbaha a Hannunsa,Fitowarsa Daga Dakinsa kenan ya Dauro alwala yana Jiran Yusuf zasu tafi masallaci Imran ya Shigo Cikin Fushi shiyasa bai ma lura da Wanzuwar Abba a falon ba.
Yusuf ya Fito Daga Shashensu Safiya na Bayansa Cikin mamakin wannan Gigitattaciyar Tsawan da Imran ke amfani da ita Wajen Kiran Sunan Munari Daman shima yana Shirin Fitowa ne su tafi masallaci da Abba.
Ya yusuf ne Da suka Bayyana a Falon ya Kalli Imran yana Fadin”Lafiyanka..? Me Munarin Tayi maka kake mata wannan kiran..?
Ko Kallonsa bai yi ba illah Daga Murya Da yayi yana Kallon Safiya yace”Where is She..?
Cikin Launin Bacin Ransa da Tuni Muryansa ta Sauya Cikin Sanyinta Tace Tana Kallon Yusuf”Tana Dakinta..!
Bai Tsaya ma Mgana ba ya Fara Taku Zuwa Kofar Dakin Munarin yana Fadin”Wlh kinjin Rantsuwa Daya ko..Kika bari na Taka kafata Daga Inda Nake baki Fito ba.. sai na Tabbata da na Miki Dukan da Ba suma zaki yi ba sai kin ji Kamshin Lahira yadda Zaki ji Dadin ba wata Labarin ina Sumar da Mutane..!
Yafada Cikin Fushi Lokaci Daya Jijiyoyin Kansa suna Tashi Radau Kirjinsa na wani Tashi yana komawa Yusuf ya Kallesa ya koma yana kallon Abba Da yayi Tsaye kawai yana kallon Ikon Allah.
Munari Da Tun Fitowarta Daga Tiolet Taji kiran da Imran yake mata Tasan Yau Kashin taya Bushe Tsoro ne ya Hanata Fitowa,Tana Tsaye Tana Rawan Jiki dana Zuciya Jin abunda yace ne yasa ta Ta Sadakar ta Fito Domin ta Tabbata Zai aikata Abunda yace Ba wanda ya Isa ya Hanashi Mganar sa kamar Kaifi Tokobi ne in yasara sai tayi yanka..
Cikin karkarwan Jiki ta Fito Daman Kofar tana Bude ne tun Shigar ta bata Rufe ba Haka ta Hade Hannayenta Saman Cikinta Tana Fiki Fiki da ido Har sun Fara kawo Ruwa Saboda Tsoro Tana Hango Kanta Bayan ta Shiga Hannu Ya Imu yana Kwallo da ita kamar Yadda yake Fadi.
Bata gama Karisowa gabansa ba ya Daka mata tsawa Cikin Kakkausan Murya yana Fadin”Kina jina ina kiranki Kina banza Dani Don Ubanki..?kin Raina ni ko..?Ko ni Sa”an Wasan ki ne.?
Ya Karishe Fada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya yana jin kamar yasaka Kafa ya bata wani Bugun da sai ta Suma nan take..
Munari Data Rude ai sai ta Zube gabansa ta Fashe da kuka tana yi tana Kamkame jikinta Waje Daya.
Abba Dake Tsaye ya Daga Baki yace”Imran kada ka Daketa Nace..!.
Ammh Imran bai ma san Abba na Mgana ba Bacin rai ya Rufemai ganinsa da Jinsa.
Cikin Kufuluwa ya Kalleta yana Fadin”Wannan kukan naki bazai Hanani Sauya miki kammani yau acikin Gidan nan ba..Wane ne ya Baki Izinin kawo wannan yarinyar Gidan nan..? Kuma Waya baki Izinin da Zaki Kulla kawance da ita Da Har Zaki Rika bata Labarai akan Gidanmu..? Iskancin naki ma bazai tsaya kan Wanda kika Raina ba sai kin Tsallako kaina ko..? Saboda ban taba Yima Fuskarki Dameji ba Shiyasa Har kike da Bakin Fada ma Wata Mara Kunyar yarinyar Chan ina Duka Har sai na Sumar da Mutum ko..?
Ya Karishe Fada da Tsawar data Gigita Munari Ta Fara mgana Cikin kuka.”Ni..Ni…Wlh..Ban..Fada..mata ko..!
Ai bata kai karshen mganarta ba ya Daga Hannu ya Wanketa da wani Lafiyayyan marin da sai da ta Kife ya kuma saka Kafa yayi kwallo da ita ta Fadi chan gefe sai da kanta ya Bugu da kujera ji kake kum,Wanda ta saka Dole Munari ta saki marayan kuka Tana Fadin”Wayyo Allah na Ya Imu don Allah kayi Hakuri..Abba..Ya yusuf Ku Taimakamin..!
Take Fadi Tana kuka Abba bai Motsa ba Shima Ransa ya Baci Yusuf ne ya Riko Imran din Cikin bacin rai ganin yana Shirin kara Bin Munari ya Taka da Takalmin kafarsa,Safiya kuma Baya taja Tsoro ya kamata gashi Tana son Isa Wajen Munari Tana Tsoron kada Itama ya Illatata.
Ya Rikesa Sosai yana Fadin”Imran Wht is your Problem ne..Abba na maka Mgana ka maidashi Banza..? Me tayi maka kake Dukanta kai baka jin kunyar Dukan mace..? Macen ma Kanwarka Wacce baka da kamarta..?
Imran ya Kallesa Idanuwansa Jajir kafin ya Kwace Jikinsa yana Fadin”Ina mgana tana cemin baa Haka ba..?Zan mata karya kenan ko..! Ni ina Wasa da ita ne zata Rika bama Wannan yarinyar Labarin ina Sumar da Mutane..? Yusuf Let me Tell ur wani Abu bana son na Bata ma wani Rai Shiyasa bana shiga Shirgin da ba nawa ba..Nima na Tsani ka batamin Raina Saboda BANA SON RAINA YANA BACI..!
Yafada Cikin hargowa Lokaci Daya yana Wani Buga Kafarsa ya Cigaba da Fadin”Zan Cigaba da Dukanta Har sai ta Suma sai taji dadin bada Labarin ina Sumar da Mutane..ina na kara ganinki da wannan Yarinyar sai na Illataki..Nonsesses kawai..!
Daga haka kawai ya Daga Kafa ya wuce Fuu zuwa Dakinsa ya Shiga ya Banko Kofa ji kake Bam! Kamar zai Ballata Abba ya Jinjina kai kawai ya kasa cewa komai Yusuf ya Kallah wanda ya Daga Munari Dake ta kuka ya kalli Safiya yana Fadin”Kamata Don Allah..!
Da Sauri ta Riketa Tana mata Sannu Cikin Tsausayawa Abba ya Juya yana Fadin”Mu tafi masallaci Yusuf..!
Ba Musu yabi bayan Abba suka Fice ita kuma Safiya ta kama Munari zuwa Dakinta sai da suka Shiga ta Rufo Kofar take Fadin”Kema munari me ya aike ki bama Intee wannan Labarin gashinan yaje kunnunsa yanzu..!
Munari na kuka Tana Dafe da goshinta Inda Har ya Sumtuma tace”Wlh bansani Ba Anty Safiya..Bansan zai ji Labari ba da ban Fada mata ba..!
Safiya tace”To ita ya akayi ma ta gansa Har ta Fadamai..?
Munari na Sharan Majina tace”Bazai zama ita ta Fadamai ba..Sai dai in Tayi Zencen da Ya SAgir ne shi kuma Cikin mgana ya Fadamai kuma zai kawo nice..Daman ga Haushin Abunda Intee tamai Duka ya Hada ya Huce akaina Da kuma Haushin kawancen da muka Fara da ita Saboda yamin kashedin kada na yarda nayi kawa da kowa..Anty Safiya Taya zai ce kada nayi kawa ni ba Mutum bace da bana son Farinciki..?ko kuwa shi ba Abokin garesa ba Shi wa ya Takuramai..?
Ta Karishe Fada Cikin kuka da Tsausayinta ya kama Safiya ta Rumgumeta ta bata baki DAkyar ta Lallasheta Tayi Shuru,Ta Dauko man Zafi ta Shafa mata agoshinta Bayan ta Sake alwala ta Fice ta barta Tana Kokarin Tada Sallah Itama Shashenta ta Shiga Domin ta gabatar da Sallah aranta Tana Tunanin Duk iya Hasashenta kan Imran ya Wuce Yadda Take Tunani ko take Tsammani.
Su Abba basu Dawo ba sai Bayan Sallar Isha”i suna Fitowa Daga masallaci suka ga Imran ya Fito yana Saka Takalmi ya Sauya Kaya Daga Riga da Wando Zuwa Wata Bakar Jallabiya Sagir ne ke mai mgana yayi banza Dashi ya wuce kamar zai Tashi Sama Dashi akayi sallar mangariba Duk da Raka”a Daya ya samu sai ya Rama Sauran ya Tsaya Har akayi Sallar Isha”i yana Sahun baya ne Shiyasa su Abba basu Lura dashi ba.
Sagir ne ya gaisa dasu Abba.
Abba ya Dafa Kafadansa yana Fadin”Ka Rabu dashi Yau Zuciyar tasa ne tatashi Har gobe da wannan bakar Zuciyar sai wayi gari..!
Sagir ya Kada kai yana Fadin Allah ya kyauta da haka sukayi Sallama ya Nufi Cikin gida Duk da ya Damu yana Tunanin kan mganar Daya Fadamai n in bai Kuskure ba komai zai Dawo kan Munari ne Domin zai ce ita ta gayama Inteesar Tuna Haka da yayi ne ya Dafe kansa yana Fadin ya Illahi me na aikata ne..? Nafi kowa sanin Imran in Ransa ya baci kamar Mahaukaci yake..Kada yaje ya Duke yar Mutane fa..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button