GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Janafty
3/22/22, 23:06 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

    *🅿�23*

Inteesar Tafiyarta take cikin Natsuwa Kwata kwata bata ji takun Sawun Imran ba Ballatana ta Fahimci He is after Her,Saboda Shi Yana tafiyarsa Cikin Sassarfa da mazantaka irin na Jaruman Maza sai dai yana komai Cikin Natsuwa ne da baka isa yana Tafiya kaji takun Sawunsa ba Shiyasa bata jiba har ta iso gidansu Munari,Karamar kofar tana Bude ne Ta saka Hannu da Niyyar Bugawa sai Kofar ta dan Bude shiyasa ta saka kanta kai Tsaye ta Shiga gidan Imran Shima alokacin ya Mara mata baya.
Iro megadi bashi a Haraban gidan ya Kewaya.
Hankalinta yayi gaba kawai taji ansha Gabanta da Sauri Cikin Tsoro taja baya Jikinta ya fara rawa da ganin wanda ke gabanta ya Kafe ta da Idanuwansa yana More Kallonta Da dukkan zuciyarsa Sai alokacin yaji Salamar Daya Dade bai samu irinta ba wani Natsuwa da Farinciki suna kara Kwaraya acikin Ransa wanda ada yake jinsa kamar yana yawo asaman Gajimare,Duk adalilin rashin ganin fuskar Inteesar wanda ya kara Tabbarar mai da Asiri Inteesar tayi mai kuma yau sai ya Tabbatar da koma Miye,sai ta Hako shi Duk inda ta Binnesa.
Inteesar da gabanta ke Fadi saboda Ganin Imran taja baya tana Kara Rike Jakar Hannunta Dakyau Wuri Wuri Take da ido Tana Neman Hanyar Gudu Har ga Allah bata son ta Hadu Dashi gani take kamar yana mata kallon na riga nagama Dake.
Imran ya Lura da yadda take Neman Zurawa da gudu da Sauri yace”Don”t Ever Try it..Ranki zai baci in kika Gudu ban yi mgana Dake ba..!
Yafada Cikin Dakuna Fuska da Kakkusan Muryansa.
Miyau ta Hadiye da Sauri Kafin ta Sadda kanta kasa Tana Fadin”Ba..ba guduwa zan yi ba..Ina yini..?
Tafada Tana kallon kasa bata so ta Dago su kara Hada ido Jikinta wani iri yake mata kamar ba nata ba.
Karkace kai yayi yana Kallonta Cikin Nazari kafin taji yace cikin Kaushin Murya”Ina kika Binne asirin..?
Da sauri ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakin kalamansa tace”Asiri kuma..?
Tafada Lokaci Daya tana Zaro mai ido Kai ya gyada mata kafin yace”Eh asirin da kikamin wanda yasa nake son ganin Fuskarki koda yaushe..!
Yafada kai Tsaye domin shi daman Dan kai Tsaye ne Baya karya Domin ka so shi.
Inteesar ta saka Hannunta Guda a Kirji ta Dafe Lokaci Daya Tana Fadin”Ni nayi maka asiri..?
Ransa ne ya fara baci Cikin Dakuna Fuska yace”Eh kefa..Kina Nufin zam miki karya ne..?
Inteesar datsoro ya kamata sai Idanuwanta suka Tara kwallah Cikin kwalkwal take fadin”Wlh..Wlh..Allah ni ban yi maka asiri ba..Ni ban taba sanin ma a ina ake asiri ba..Kayi Hakuri..!
Sai hawaye Sharr duka Idanuwan Biyu Lokaci Tana Jan majina,Mamakinta ya kamashi ganin Daga mgana sai kuka yasa ya kasa ce mata komai.
Kanta na kasa ta shiga Furta”Ban yi maka komai ba..Wlh bansani bane..Bansani ba..!
Tafada cikin kuka Har tana Shan majina da Shessheka.
Sai jikinsa yayi sanyi ganin yadda take kuka da Sauri yace”Ke daga mgana sai kuka..? Stop it kada wani ya fito yace ni na Dake ki..!
Jin haka yasa ta fara share Hawayenta Tana Kara jam majina Kafin ta Dago Tana Fadin”Ka yarda ban maka asiri ba..? Wlh ban san ma inane ake asirin ba..In Umma taji wannan mganar Gobe in na koma Gida Zata min Fada ni kuma bana son Fada..!
Tana kallon kwayan Idanuwansa Tana mgana Sai kuka kuma Sharr ta Kara Rike Jakarta Tana kuka,jikinsa sai ya Saki ya kasa Dauke ido Daga kanta Haka kurum yau karo na Farko yaji bai kyauta ba yasa wani kuka,Yau yaji Bai kyauta ba Daya Tareta da wannan mganar gashi tayi kuka ko Daga ganin yanayin mganarta bata san komai ba.
Cikin Sanyin murya yace”Bazata ji ba..Kuma bazata miki fada ba..!
Yafada karo na Farko Cikin Sigar Lallashi Jin haka yasa ta Sauke Numfashi Tana Fadin”Ka yarda ban yi maka komai ba..!?
Tafada Tana Kallonsa Kallon Dayajisa Cikin wani yanayi,Kai ya dan kauda kafin yace”Eh..Share Hawayen ki .!
Yafada yana Kokarin Saisaita kansa Domin yanajin kamar ya Fara Fita Daga asalin Imran din sa yana komawa kamar bashi ba.
Jin abunda ya Fada yasa tayi Saurin Saka Hannu ta Share Hawayenta Shi kuma yana ta kallonta tana Dagowa suka Hada ido da Sauri ta Sadda kanta Kafafunta na rawa.
Aransa kuwa ayyana Shagwaban yarinyar kawai yake Daga mgana sai kuka..?
Baisan Dalili ba kawai yaji yana ce mata”Gobe..ina zaki..?
Bata Dago ba tace”Gida..yau mun gama Exams..!
Cikin wani yanayi yace”Ina ne gidan naku..?
Kanta na kasa Sitll tace”Kaduna..!
Tsam yayi yana Kallonta jin Zuciyarsana so taji Rashin jin Dadin Tafiyarta bai san sadda Bakin sa ya Subuce ya Furta”In kin tafi sai yaushe Zaki Dawo..? inteesar ta Dago cikin mamakinsa Tana Kallonsa sai kuma ya Hade rai yana Tunanin meke Damunsa .?
Kai ta Rausaya Kafin tace”Hutun Sati uku garemu..So kila bai fi na kara 1 week ba kafin na dawo..!
Har tagama mgana bai ce komai ba Idanuwansa na kallon Gefe yana Tunanin yadda zai iya Zama har na Tsawon wata Daya kafin ta Dawo
Cikin Idanuwansa yake kallonta Kafin yace”Ki dawo alokacin da kukayi Resuming..? Promise..?
Yafada kai Tsaye yana Sakarmata Duka Idanuwansa wadanda suka Sake Rikita taji bazata iyamai gaddama ba. Da sauri tace”Tom..!
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Bata Hanya batare da yayi mgana ba Kanta na kasa ta fara Tafiya shi kuma yana Gefe ya Harde Duka Hannunsa a Kirjinsa yana Binta da kallo yana ji kamar in tatafi shikenan kamar an Daukemai wani gafara,kamar ya Hanata Tafiya baisan yaushe ne ba..? Sai dai kallonta na mantar dashi Dukkan wani kuncin Duniya.
Kamar ance ta Waiwayowa tana Juyowa suka Hada ido,Da sauri ya Dauke kansa ita kuma sai ta Murmusa kawai ta Tura Kofar da zai sadata da Falon Gidan tana jinta Cikin yanayin Data ke Tsintar kanta indai Tana gaban Imran.
Sai da ta shige kana ya Sauke Idanunsa ya koma Kan Mashinsa Dinsa Dake Fake a haraban Gidan ya Haye Samanta Aljihun wandonsa ya saka Hannu ya Dauko kwalin aspen da Lether ya Kunnata ya shiga Zuka so yake yaji baya Tunanin Inteesar ballatana Gilmawar Fuskarta ko son ganinta so yake ji He don”t care in Tatafi sai dai ina Hayakin na Shiga Cikinsa Kamar baya saka Komai gabadaya komai ya Tsayamai Cak Mood dinsa ya sauya yana so yayi Tunanin kan karan kanshi ammh ya kasa Kowani Dakika yana jin Tsorom Tafiyarta na Tsawon kwanaki bazai ga Fuskarta ba.
Bai san adadin Lokacin Daya Dauka yana Zaune yana Busa Hayakinsa ba Har sai da Ya Yusuf ya Dawo Daga Wajen aiki,Har mgana yayi mishi Imran din ya Daakuna Fuska ya Kaida kai ganin haka yasa ya Girgiza kai kawai ya Rataya Jakar Briefcase dinsa ya Nufi Cikin Gida aransa yana Tunanin zai samu Abba da Mgana ya Lura Imran abubuwansa basa Raguwa sai ma Karuwa da sukeyi.
Afalon yaci karo da Inteesar Munari ta Rakota Da ita da Anty Safiya sai Abba Dake zaune Sallama Tayi Musu Abba nata saka mata albarka.
Kallonta yayi yana Fadin”Me sunanki na gaskiya..?
Inteesar na Mirmishi Cikin Ladabi tace”Sunana MARYAM Abba sunan Kakata naci wacce ta Haifi Daddy na shiyasa yake kirana da Intee har sunan ya Bini..!
Abba ya Kalleta Cikin Dattakonsa yana Fadib”Masha Allah ai nima sunan Mahaifiyata Gareki..Daga yau kin tashi Daga yata kin koma Uwata..Allah yayi albarka..!
Inteesae bakinta Har kunne tace”Na zama Maman Daddy da Abba kenan..!
Su Munari nata Dariya ta gaida ya Yusuf ya amsa yana Kallon Safiya yace”Naga kamar kuna Sallama ne..?
Da sauri Munari tace”Gobe zata koma Gida Hutu ya Yusuf.!
Tafada Cikin nuna Rashin jin Dadinta Kada kai yayi yana Fadin”Ayyah..Munarin Abba zaki bari da kewa…Anywhy..Allah ya Kiyaye Hanya muna gaida kowa da kowa..!
Abba ma ya Karbe da cewa”Kice ina gaida Daddyn naki..In Allah ya Nufa zamu hadu..!
Inteesar tace”Zaiji Abba..Ka manta bakace agaida Umma ba..Umma Sarkin Fada..!
Tafada Tana Tura baki Munari ta Zungureta tana Fadin”Ke kuma Sarkin Shagwaba da Laifi ko..?Dariya suka sakamata Anty Safiya ta Mikamata Leda Hannunta Tace takai ma Umma Turaruka ne Dana Daki da Humra Inteesar ta Karba Bakinta Har Kunne Sallama sukayi ta karbi Jakar Hannun Ya Yusuf suka Nufi bangaransu Itama Daganan tayi ma Abba Sallama ya Bita da Allah ya Kiyaye hanya Ana gabda da kiran mganariba yasa ya tashi ya Shiga ciki Domin ya Dauro alwala,ita kuma Munari ta koma Bedroom dinta ta Dauko Mayafinta ganin ba kowa afalon yasa Inteesar ta Fice zuwa Haraban gidan ta jirata Hannunta Dauke da Ledoji guda Biyu Daya Sakon Anty Safiya ne Daya kuma na Munari ne kaya ta bata Da Hijabi Sabo ne bata taba sawa ba ya yusuf ya Dinkamatashi itama ta bama Inteesar in ta koma Kaduna in ta gansu ta Tuna da ita.
Tana Tsaye tana Mirmishi Gefe Daya Tana ayyana gobe i uwar haka tana Jikin Daddynta tana Zubamai Shagwaba kamar an ce ta Waiga sai taci karo da Imran zaune kan Mashin dinsa karan sigari a hannunsa idanuwansa suna Lumshe yana Busawa Hayakin yana Fita ta Hanci ta baki.
Tsam tayi tana kallonsa,tsausayinsa ya kamata ganin yanayinsa wanda yasa bata san sadda ta taka zuwa gabansa ta Tsaya ba ganin har ta Tsaya bai Lura da ita ba yasa ta san yayi nisa Cikin yanayin Dayake ciki.
Kawai sai ta saka Hannunta guda Daya ta Zare Karan Sigarin Dake hannunsa Daidai Lokacin daya Ware Idanuwansa akanta.
Dam! Gabansu ya Buga atare, Suka kurana juna ido Cikin Bugawar Numfashi da Muradi mai girma,
Ita ce tayi Saurin Janyen idanuwanta Saboda tana ji kamar Kafafuwanta bazasu iya Daukanta ba
Cikin Sanyinta tace”Ka manta na Fada maka Ita shan Taba Illah take ga Lafiyar Dan adam..?
Ko ka manta na taba Fada maka Shan Taba bata dace dakai ba..?
Har tagama mgana yana kallon Dan bakinta ko Kiftawa bayayi ita bata ma Kara Kallonsa ba ta Saki Taban a kasa ta Mutsuketa Tana Fadin”Bazan barka da ita ba..Bani na aljihunka i know akwai wasu aciki..?
Tafada Cikin Kamewa Lokaci Daya Tana Mikomai Zararan Hannayenta..
Galala yake Bin Hannun nata da Kallon Mamakinta na kamashi Cikin Dakiya ta kara Fadin”bani na aljihunka nace…Kadai san nasan ba wannan bace ita kadai ba ko..!?
Dariyarta ma yake yi acikin Ransa yana mamakin yau rana ta Farko da Mace ta Tsaya gabansa Tana bashi Unarni haka.
Yaji bama zai iya yimata gaddama ba Ya saka Hannu a aljihu ya Dauko Kwalin Taban ya saka mata a Hannu Harda Letthe din gabadaya.
Kwalin tabi da kallo kamar tana kyamkyami nan da nan Zuciyarta ta Fara tashi Daman Daurewa take,Da Sauri ta Bude ledan hannunta ta Watsashi aciki Tana yamutsa Fuska tace”Kamar itace abincinka..? Bantaba Ganinka baka shan Taba ba sai sau Daya..Plz ka bari In ba so kake Huhunka ya samu mtsala ba .!.
Tafada Tana kallon Gefe domin bata so ya Fahimci bakinta ya Cika da Miyau..
Mirmishi ya Sakarmata mai kara Har sai da ta Dago Tana kallonsa Cikin mamakinsa Saukowa yayi Daga Mashin din yana Fadin”Ban ce miki Daman zan daina sha ba..!
Inteesar ta gyara Bakinta tace”To yanzu kayi min alkwarin zaka Daina shan Taba..!
Kallonta yayi kafin yace”No..Ni bana haka ba. bazan yi miki alkwarin da bazan cika ba..Zan daina shanta Duk Ranar da Allah yace..!
Mamaki ya kamata ta Kada ido Tana kallonsa yace”Yes bana yima Mutum alkwarin da na san bazan cika ba..kuma bana so nima ayimin alkwarin da baza”a cikamin ba..Kuma ni bana karya agaban mutum saboda ya soni..Ina Fadin gaskiyatane gaban ko Waye Allah ne kadai nake jin Tsoro ba Mutum ba..!
Daga haka kawai ya wuce ta yana Tafiya Cikin Sarsassafa kafin taji yace”Kada ki sake ki mana Amai Gida..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button