GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Dariya Imran ya saka kamar ta basawa kafin yace”Meyasa kake Tsoron Mutuwa abokina..? Ka manta Zaka Mutu Dolen ka..’Sagir yace”Nasan zan mutu..Ammh ina Burin kafin na Mutu na ijiye masu min addu”a kai daman bana ta kai Tunda ka Riga ka auri Taba gatanan ma ahannunka baka da mtsala..”Yana jinsa bai yi mai mgana ba ganin sun bar anguwansu yasa Sagir yace”Wai ina zaka kai ni ne..?
Har ya Cire rai da zai yi mgana sai yaji yace”Gidansu Safiya zaka Kaini..!
Sagir yace”Safiya..? Wata Safiyan kuma..? Imran yace”Safiya Buhari alhassan..”Sagir sai da ya Dafa Kafadan Imran saboda Razana Cikin Firgici yace”Budurwan ya yusuf fa kenan..? Yafada yana Bayyana Firgicinsa Dariya Imran yayi kafin yace”Sakeni Matsoraci kada kasa mu Fadi saboda Tsoron ka..!
Sagir yace”Don Allah mu daina wasa me zai kaika gidansu..?ko Ya yusuf ya aike ka..?
Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin”Wazai aika ?Ni Imran..Kana shan kwaya ne..Ni zan aiki kaina malam..”Sagir yace”Me zakaje yi gidansu..? Imran yace”Ka Nuna min Hanyar Gidan mallam ba Tambayata zaka Tsaya kana yi ba..”
Cikin Tsoro da Fargaba Sagir yace”Zoo road gidansu yake..”Batare da bata Lokaci ba Imran ya take mashin Har suka isa Zoo road ba wanda ya kara mgana Sagir ke nuna Hanyar gidan,Cikin Lokaci sai gasu Kofar Gidansu Safiya wanda ke Dauke da Katon Get mai Ruwan Madara Daga ganin Zubin gidan zaka Fahumci suna Rufin asiri eh mana suna Dashi Mahaifinta Alhaji Alhassan Buhari Lacture ne A BUK Dake nan Jahar kanon Dabo.
Akofar gidan Imran ya Faka Mashin din nashi Sukasauka Gabadayansu Lokaci Daya ya Juya yana Bin Gidan da kallo yana Wani Shafa Sajensa ganin haka yasa Sagir yace”Imran Me zaka yi agidan su yarinyar nan..?

Imran bai mai mgana ba Illah Tabansa daya Kara Fitowa da ita ya Kunna mata Wuta sai da ya Busa Hayakin ya Fesar kana ya Sauke kallonsa kan Sagir yana Fadin”Bafa wani abu ya kawoni ba..Kawai Kashedi zan mai da kuma Umarnin Yayi gaggawan bama Yayana auran yarsa in ba Haka ba..”Sagir Daya Zaro ido yace”in ba Haka ba mene Imu..? Don Allah ka bari kada ka Shiga gidan Mutane ka Tada wata Rigima so kake amaimaita abunda ya Faru a gidansu Asma”u..? Ka Karya ma kawunta Hannun Daga karshe ba Yaya yusuf ka bari da Shari”ar ba ina amfanin wannan Rayuwar da kaKe saka Kanka acikine..?
Yana jinsa bai taka ba idanuwansa ma na Lumshe yana Zukan Taba yana Fesar da Hayaki,Sai chan yaBude Jajayen Idanuwansa yana kallon Sagir Lokaci Daya ya gyara Tsayuwa yana Fadin”Bazan karyamai Hannu ba..? GIDANMU fa ya zaga..? Ya kira Babana Mahaukaci..? Wlh Tallahi kowaye ya nunayatsa gareni ya zagi gidanmu ya kuma kira Babana Mahaukaci sai na Karyashi in ban Nakasaahi ba Sagir..”

Ya karishe Fada Cikin Daga Murya Idanuwansa sun Sauya Launi Ganin haka yasa Sagir ya Sausauta Cikin Lallashi yace”Naji Bai kyauta ba..Ammh me ya jawo haka kuma yau..? Imran yace”Raba yayana yayi da yarsa..Can u juz imaging ya yusuf na kuka fa saboda yarsa kuma sai naje gida na kwamta ina Murna..? Ina so ya gane ya Tabani Wlh zan mai gargadi in yaji Ruwansa in bai jiba Jikinsa zai gayamai ne ba Ruwana fa..”
Ya karishe Fada yana Zakuda kafadansa Lokaci Daya yana Fesar da Hayakin Taban Daya Zuka Harta Hanci ya Dumfari get din gidan Sagir ya Bisa yana mai magiya Cikin Takaicinsa ya waigo yana Fadin”Malam don Allah ka kara gaba..Haba nifa Gidan kawai na Bukata kuma ka Kawoni zaka iya karawa gaba Bai Dameni ba”Yafada kamar zai Dakeshi Sagir ya kallesa yana Fadin”Ammh ai har kofar Shagona kaje ka Dauko ni ko.?
Imran ya juya yana Fadin”Kuma Da ka gama Biyamin Bukata nace U are Free to go ko..? Sagir yayi Kasake yana kallonsa Har ya Taka Jikin Get din yayi Knooking Sai gashi megadi ya Leko Domin ganin Waye Hayakin Taban da Imran ya Fesamai ya Faramai Maraba Baya yaja yana Fadin”Bawan Allah meye hakan..?
Yafada ya kare ma Imran kallo wanda ya tsaya kyam Hannunsa Daya cikin aljihunsa Dayan kuma ya Rike da Tabarsa yana Busa sai da Lumshe ido ya Bude kana ya Sakarma Megadin wani kallo kafin yace”Alhassan Buhari yana Ciki..?
Megadi ya zaro Ido Jin sunan Megidansa kai tsaye ya Tsorata ganin yanayin Imran din Shiyasa yayi saurin cewa”Eh..Eh..yana ciki bai riga ya Fita ba..”
Imran yace”Gud..Shiga kace mai yana da Bako a waje..”da sauri megadin ya juya zai tafi Imran yace”Ji mana..! Cikin kaushin Murya Jiki na rawa ya juyo yana Fadin”Na”am yallabai..”Domim a Tsorace yake gani yayi kamar in yayiwani gardama Imran zai Fito da wuka Domin kallonsa yake kamar wani Dan Daba Duk da yayi Mishi kama da Yusuf Saurayin Daya Daga cikin yaran Gidan Jikinsa bai saki ba.

Sai da Imran ya Busa Hayakin Tabansa kana yace’In yabukaci sanin waye kace mai IMRAN ABUBUKAR MALAMI ne…Kanin Yusuf Abubukar malami..”Ya karishe Fada yana wani Shafa Gemunsa,lokaci Daya yana Lailaya Taban Hannunsa,Da gudu megadi ya juya yana Fadin”To yallabai..”Sagir Dake gefe Tagumi kawai yayi aransa yana ta addu”an Allah ya kauda Fitina yaso ya kira Ya yusuf ya gayamai ko zai yi wani abu sai ya Tuna Lambarsa Tana Karamar wayarsa ne kuma ya manta da ita agida saboda Sauri.

Megadi Har Falon gidan ya Shiga Daidai Lokacin Alhaji Alhassan ya Fito Zai Fita Matarsa Hajiya Mero ta rakosa Megadi ya Zube yana Fadin”Alhaji kana da Bako.”Cikin  mamaki yace”Bako..? Daga ina kenan..? Megadi ya Kaskastan dakai yana Fadin”Yace ace maka Imran Abubukar malami ne kanin yusuf..”Alhaji ya kalli Hajiya Mero Cikin Fushi yace”Kin ji ko..? Wannan kanin Shashan yaron chan ne da SAfiya ke ta kuka Tun jiya kan nace Bata bashi..”Hajiya Mero ta karkace kai Tana Fadin”Takadirin yaron nan dai kaninsa da muka samu Labari Alhaji..? Yana Saba Babbar Rigarsa yace”Shi mana..Bari naje Shima nayi mai Fata Fata kamar yadda nayi ma Yayansa Jiya..Ni ba karamin Mutum bane da inaji ina gani zan Hada jini da Dangin Mahaukata da yan iska..”Jakarsa ta Briefcase ta mikamai tana mai Allah ya kiyaye ya Fice yana Fada Megadi Daman Tuni ya Fice kada kai Tayi Ta koma Ciki Tana Ayyana abubuwa da Dama kan Al”amarin.

Yana Fitowa Haraban Gidan ya mikama Direbansa Jakar yana Fadin”Ina yake..?Megadi yace”Yana Daga Wajen get Alhaji..”Karamin tsaki Yaja yana Fadin”To ya shigo mana..Ko ni zan Biyo sa ne..? Yafada da Dan karfi Har Imran da Sagir sai da sukaji Domin ya Taho gabda Get din ne balle ma Alhaji Alhassan irin Mutanen ne marasa mgana Cikin Natsuwa ga Sakin Murya.
Megadi ya leko waje yana kallon Imran yace”Yace ka Shigo yallabai..’Mirmishi Imran ya saki kafin ya Saki Taban Hannunsa ta Fadi kasa ya saka kafa ya Murjeta Megadi ya wangalemai karamar Kofar ya Shige Sagir na ganin Haka ya bi bayansa Suna Shiga Haraban Gidan suka Hada ido da Alhaji Alhassan wanda ke Tsaye yana gyara Babban Rigan Jikinsa Lokaci Daya yana kare ma Imran kallo Daga sama Har Kasa
Shi kuwa gidan yake Kare ma kallo afili ya Furta..”Nifa ba ganin kyale kyalen gidanka ya kawoni ba..Mgana nazo muyi kan Abunda ya Shafemu Alhaji..”

Ya Karishe Fada yana Kafeshi da Jajayen Idanuwansa Lokaci Daya ya Zura Hannu cikin aljihu ya Dauko Tabarsa ya Kunnata hayaki ya Fara tashi Alhaji Alhassan Dake tsaye Bai yi mamaki ba Daman ya samu Labarai Dadama kan Imran din a Fusace ya Tako zuwa gabansa yana Fadin”Kai wannan wani irin Shashancin ne..? Kashigo Gidana kana Min Shaye Shaye..? Yafada Yana wani Kunfar Baki Domim ba Laifi Alhaji Alhassan akwai Fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button