GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL


Kaduna.

Tunda suka dawo Daga Dukku Inteesar ke shirin komawa makaranta Taso tafiyar nata ya Zama Alhamis Sai Daddy yace bari Asabar ko Lahadi sai ta Koma,bata so ba ammh bata da yarda Zatayi Ganin zaman gidan ya Isheta yasa taje gidan Nasara ta Kwana Daya gidan Ya Basheer ma ta Kwana Daya gidan su Inno ma Tayi kwana Daya Ranar Jumma”a tadawo Saboda Shirin Tafiya Umma ta mata Miya da Dambun kaji sai kayan Snkas Sai sauran Tarkace irin su madara Indomie da Complez wanda Zata tafi dashi sai kuma Dinkuna da Daddy ya Sake Dinkamata umma ma ta Dinka mata Kala Biyu duka guda Biyu iri Daya Munari tace takai ma Kala kala Daya sai ta bar wasu kayan nata agida ta Kara Dibam wasu kayan ta Hada da Sabbin Zata koma Dashi.
Suna waya da Hafsah tunda suka koma ita ke kiranta mai sonka ka soshi itama Tana kiranta Har ta bata Anty Fareesa su gaisa Ya Sa”ad kuwa shima ya Kirata sau Daya suka gaisa Tayi Saving din Lambarsa ya Sadam kuwa Kusan Kullum sai sun kirata shi da Anty Aneesa wai ko ta Shigo kano ne tace a”a Shi Ya Sadam din har kiran Daddy yayi yana Rokonsa Inteesar ta Dawo Gidansa da Zama Daddy ya basa Hakuri yace bazai yuyu inda take ma Duk gida ne ammh yayi mai Alkawarin Zai gayamata ta Rika Zuwa Weekend gidansa in ta Samu Dama da sukaji haka sukace ba komai.
Da Umma taji tace ai bakomai Tunda suna Garin Inteesar zata Rika zuwa Ita kanta Umma suna waya da Inna Maimunatu da ya”yanta Mami ce Sau Daya ta Kirata suka gaisa Sama Sama tace Tana Kotu ne Daganan basu kara mgana ba group kuwa su Ya Basheer suna Kokarin ingatansa Inteesar dai bata taba mgana ba Tana dai Shiga ta Karanta Sakoninsu,Ba Laifi su ya Sa”id suna Hira da dadddre haka in sun Dawo daga aiki Daddy ma yana mgan ba Sosai ba,Baffa Kabiru ne sai dai Turo Mrning Text da Gudnigjt ba wanda bai Ciki Harda Sajida ammh itama bata Taba mgana ba Sai Khamis ya taba mgana da Umaimah Shi khamis taji Ya Sa”id na mganar ya koma Wajen aikinsa Shiyasa aka jisa Shuru.

Inteesar Tafiyarta bai samu Asabar ba Sai Lahadi Da Sassafe Ya Basheer ya Tafi kaita banda Daddy ya tashi da Ciwon Kafafu sai kawai Yace Basheer ya kaita wannan karon ma sai da Inteesar Tayi kuka sai dai suna Daukan Hanya ta Warware suna Hira da  Ya Basheer har suka iso Misalin Karfe 11am na Safe suka isa Lokacin ko Shago Sagir bai Bude ba Tunda Daman Ranakun hutun mako bada Wuri yake Bude Shagon ba.
Sai dai Mama Taga almajirai na Shigowa da kaya sai ga Sallamar Inteesar Mama ta Fito Daga Daki ita da Sagir tana mata Maraba Rumgumeta Tayi Inteesar tana Cewa Mama nayi kewarki sosai.
Mama tace”Nima haka yata..ai tun jiya da Salaha tace zaki taho nake ta Zura ido..Tafiya bata yuyu ba sai yau..!
Ya Basheer Dake baya Dauke da akwatin Inteesar yace”Wlh Mama sai yau Allah yayi..!
Maraba ta shiga musu Sagir ya bashi Hannu suka gaisa suka Rankaya zuwa Falon Mama.
Bayan gaisawa da Tambayan Mutanen Gida Mama ta kawo musu Kunu da kosan Datayi yau da Safe Ya Basheer yasha kunun sosai Inteesar nema taci Kosan kawai.
Ya Basheer ya bama Mama 20k in ji Daddy sai Kayan abinci da suka zo mata Dashi Tana ta Godiya Inteesar kuma ana Ciki tana gyara kayanta Sai da Ya Basheer yayi Sallar Azahar yayi Shirin Tafiya Mama tayi tayi ya Ci abinci yaki wai bayaso yayi Dare Ahanya Hakanan sukayi sallama Har Bakin Mota Inteesar da Sagir suka Rakashi Sukayi sallama suna Dagamai Hannu har ya Fice Daga Layin sagir Shagonsa ya Shiga Tunda Yaransa Har sunzo sun Bude shagon sunyi Shara,ita kuma sai ta koma Cikin Gida.
Ashe Ya Basheer ba Gida ya dau hanya ba Gidan Ya Sadam yaje Daman ya gayamai zai shago kano Dawo da Inteesar makaramta da kwantance sai gashi agidan Chan suka Hade suna Hira Aneesa Tamusu lunch sukaci Sai Karfe 4pm ya bar gidan yadau Hanyar kaduna Sai da Inteesar din ta Kira Anty Aneesa ta gayamata yau ta Dawo
Shine take Fadamata Yanzu Ya Basheer ya bar gidansu Inteesar taji Haushi tace bai Fadamata zai biya ba data Bisa Aneesa tace haka yace ma Sadam dayace meyasa bai Dauko ki ya kawo ki kin ga Gidan ba Sai yace baya son ki batamai Lokaci ne.
Inteesar bataji Dadi ba ammh sun Rabu kan Insha Allahu Zata zo ko Cikin Weekend din da zai kama ne.
Suna gama Waya ta Kira Munari tace mata Ta iso Munari sai murna Kamar Zata Tsinkama Inteesar dodon kunne ta Kashe wayar Tana Mata Dariya

Munari kuwa Daman Tana Dakintane itama tana gyara Kayanta da mai wanki da guga ya kawo ne Sai gata ta Fito da gudu Tana Murna Abba Dake Falo Shi da Ya Yusuf suna Hira kan Yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare a kasar nan Gefe daya kuma suna kallon NTA news na Karfe 4pm.Anty Safiya kuma na Kitchen Ta fito tana Tsalle.
Abba ya Kalleta yana Fadin”Munarin Abba meyafaru ne..?
Jikin Abba ta Fada Tana Fadin”Abba Intee ta tadawo..!
Tafada tana Washe baki karaf sai a kunnen Imran Daya Fito Daga Dakinsa sanye da wani 3Quater wando mai Ruwan madara Jikinsa ba Riga da Farko Daya fito yaso ne ya isa ga Munari ya bata wani Kyakyawan mari da sai ta kusa suma kan Ihun banzan Datake musu acikin gida sai dai sunan dayaji ne ta ambata ne yasa ya Tsaya Cak ya kasa Karisawa,Saboda yadda gabadaya Kirjinsa ya amsa Harda gangan jikinsa..
Abba dake Mirmishi ya shafa kan Munari yana Fadin”Ah Dole kiyi murna..Aminiya ta dawo ko..?ai sai tashi aje ayi mata sanu da zuwa..Nima kice ina mata barka da Dawowa..!
Da sauri Munari ta Mike tana Fadin”Yanzu kuwa Abba..Ya Yusuf ina Anty Safiya..?
Yace”Tana Kitchen..!
Gudu ta kwasa Zuwa Kitchen din tana Kiran sunan Anty Safiyan  Abba da Ya Yusuf suka Bita da Kallo Abba yace”Allah ne ya Hada kauna Tsakanin Munari da yarinyar nan yadda suke son juna Kamar wasu yan”uwa.!
Ya yusuf yace”Sosai Abba Daman haka Rayuwa ta gada..Wani abokin ko kawa sai ya koma maka kamar wani Dan”uwanka..!
Abba ya jinjina kai yana Fadin”Gaskiya ne..tashi muje masallacin naji ana ta kira tun Dazu..!
Atare suka mike Daidai Lokacin da Imran ya koma Ciki da kallo suka Bisa Kafin su girgiza kai suna mai addu”a cikinsu ransu fita sukayi Daman sunyi Alwalarsu sun Fito da Niyar tafiya Masallaci ne labarin wani Hari da yan kiddaping suka kai kauyan Zamfara yaja Hankalinsu.
Sun Fita ba Dadewa Imran ma ya fito Bayan ya saka Jallabiya ya Nufi Masallacin Zuciyarsa sai Zafi take yi maimakon yaji sanyi Tunda wacce yake jiran da neman ganin ta Dawo sai dai ta sabamai alkawari Shiyasa yaji bama yasan ganinta.
Tasan Wahalar Daya sha Saboda rashin ganinta..? Tunda Lokacin komawarsu makaranta yayi yake Duban Hanya saboda ita a Shagon Sagir yake wuni ko zai ga Dawowarmata ammh Shuru Sai ranar yaji Munari na Fadin ba Satin zata Dawo ba Tundaga Ranar yaji Ransa ya gama baci ya tsani ayi mai alkawari a kasa cikamai baisan Dalili ba Yaji baya son ganinta kwatakwata Duk da kuwa yadda Zuciyarsa ta azalzalu da son ganinta din.
Suna Dawowa masallaci Munari ta Shirya tatafi Gidan su Sagir chan suka Hade Inteesar da sai Murna chan ta Shantare sai bayan mganariba Inteesar ta Rakota dauke da Sakon Umma Munari nata Godiya suka rabu kan sai gobe da safe Munari zata Biyo ma Inteesar su shiga makaranta.

Shakira…
3/22/22, 23:07 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1

Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janafty❤️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button