
Shakira..
3/22/22, 23:07 – Ummi Tandama😇: GIDAN MU..!
(Our House)
Book 1
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janaftyâ¤ï¸
*🅿�28*
Shigowar Mama cikin dakin yasa Inteesar ta kara nokewa kamar tayi barci ganin yanayin kwanciyar nata ne yasa Mama ta kalleta tana Fadin”Inteesar lafiya kuwa..? Yaushe kika shigo.?
Bata da yadda zatayi Dole tayi saurin goge Fuskarta ta Dago kanta Lokaci Daya da mikewa Zaune tana Fadin”Yanzu na shigo kina Bayi Mama..!
Mama tace”Eh ammh Lafiya naganki wani iri..?
Tafada Tana kallon Kwayan idanuwanta da Sauri tace”Bakomai Mama ina tafiya a Hanyane wani karo ya Shigarmin ido ammh ya fita..!
Mama tace”Ayyah hala mai Shegen yajinan Ido yayi ta Hawaye..Sannu in bai bari ba ina da wani mganin ciwon ido sai na Diga miki..!
Inteesar ta gyada kai Ita kuma Mana ta Nufi kwabarta ta Dauko hajibi ta Tada Salla bayan ta Shimfida Darduma Komawa Inteesar tayi ta Kwanta Lokaci Daya tana kamkame Kirjinta da Hannayenta,Tsoron ya Fara Sakinta sai dai yanayin Data Rumgume Imran yaki barin Tunaninta Data Runtse ido Shi take gani,Jikinta yana amsawa ko”ina ya Saki Kasala ya kamata.
Lumshe idanuwanta Tayi kamar mai barci nan kuwa ba barci take ba Fuskar Imran ke Gitta mata Cikin kowani yanayinsa,ba domin yau ya Ceceta ba kila da sai Buzunta ammh ya Sadaukar da Rayuwarsa saboda ita Bazata taba mantawa dashi ba.
Ta tuna sanda ta Rikeshi da cewar da yayi ta sakeshi,da yanayin kallonsa Sai da Tsigar jikinta tatashi afili sai da ta Murmusa ta Furta”He is so nice..Yana da Kirki sai dai kirkinsa Boyayye ne bakowa ke sanin haka ba..!
Tafada tana jin wani nishadi acikin ranta tama manta da Mama acikin Dakin sai da ta juyo tana Fadin mgana kike ne Inteesar. ? Kana ta tadawo Cikin Hayyacinta tace A”a Mikewa Tayi Daga kan gadon bayan ta Sauko a kasalance ta Fita zuwa Kitchen ta Duba Flaks taga ba ruwa sai ta kunna Gas ta saka So take yi tayi wanka ko taji Dadin jikinta.
Kan kujeran Tsugguno ta Zauna acikin Kitchen din Ta Zafga Tagumi Tana Tunanin Abunda ya Faru awanni kadan da suka Gabata Tsoro duk ya cikata ammh da Ta tuna Imran sai taji wani irin Sanyi aranta.
Ya nemi alfarman kada ta Fadama kowa kuma tayi mai wannan alfarman bawanda zai ji koda Daddy ne,sai dai tana ganin kamar Godiyar Datayimai yayi kadan ya kamata ta Fara Tunamin Hanyar da Zata kara Godiya Saboda yadda ya Ceceta Daga Mutuwa.
Sai da Ruwan ya tafasa ta Diba sauran ta Juye a Flaks,ta Dauka takai Tiolet ta saka Ruwan sanyi ta surka Daidai tayi wanka Dashi,Bayan ta gama ta Dauro alwala ta Fito ta shafa Lotion dinta ta saka Kayan barcinta Riga da wando masu Ruwan madara masu Taushi, Lokacin ana ta Kiran Sallar Isha”i a wasu maaallatan sai ta Shinfida Darduma ta Tada salla,ta idar kenan Lokacin Mama na Falo Kiran Umma ya Shigo wayarta Daman tana kan gado ta jawota ta Daga suka gaisa Ta Tambayeta Daddy tace bai riga ya Shigo ba bayan Tambayan Karatu sai ta bama mama Wayar daman ita Ummn ke nema bai wuce kan mganar Bikin Yar wajen Kawu bala Domin yazo tana ma Tunanin wannan Satin ne Anty Jamila,Inteesar suna Chart Sama sama suna gaisawa ba Sa”arta su bane ta Girmesu sosai ita da Nasara da ace Tana kaduna ne Zataje Bikin ammh yanzu kam datake Makaranta sai dai in sun samu Hutu ta koma suje suga Daki ita Nasara Tunda nan cikin Kaduna Zata zauna..
Mama da Umma sun Dade suna mgana suka rabu kan Maman Zata taho Kaduna Tun Ranar alhamis sai kuma Bayan Biki in Allah ya yarda da Zata dawo,bayan sun gama Wayar Umma ke fadama inteesar wacce ta Hada Complex tana sha Inteesar ta bata Fuska wai bazata iya Zama ita Kadai ba..
Mama tace ba Damuwa in bazata iya ba sai ta koma Gidan su Munari har ta dawo Sagir ne kuma Tana Tunanin Shima Ranat asabar zai shigo Kaduna Daurin auran sai ya Jirata su dawo Tare Sai da Inteesar taji haka kana Hankalinta ya kwanta.
Da wuri ta kwanta Saboda bata Cikin Natsuwarta ta Dade barci bai kwasheta ba Tana Tunanin Abunda ya Faru kuma koda barcin ya kwasheta Cike da mafarkinsa Kala kala Abun har ya soma bata mamaki.
Da safe har ta ma manta da Zencen zuwa Gidan Ya Sadam wayar sa ya tasheta Daga Barci yace ta shirya zai Shiga asibiti in yagama abunda yake yi Zai Taho ya Dauketa Dole ta Mike ta yi Sharan Daki ta gyara ta wanke Tiolet ta gyara Tsakar gida,Mama kuma ta gama Abun Karyawa kunu da kosai sa ta sha kunun da Buredi ita,kana ta Juye ruwan Zafin da Mama ta Cika Flaks dashi tayi wanka Bayan ta Fito ne ta Dokama Munari kira Lokacin ma barci take bata tashi ba Sai da ta mata Kira Biyu ana ukun ne ta Dauka Tana Muryan barcin Inteesar ta Auna mata Zagi tana Fadin tatashi ta Shirya Ya Sadam ya Kirata jin haka yasa Dole Munari ta Mike.
Falo ta Fita taga ba kowa yau Lahadi Ya Yusuf suna ciki Dakin Abba ta Shiga ta Iskeshi yana ta Karatun Qur”ani sai bata kateshu ba ta Fito ta Shiga Kitchen ta fere Dankali ta Dora Ruwan Zafi kana ta Fito ta dan gyara Falon itama ta Share ta goge ko”ina kana ta koma ta Soya Dankalin ta soya kwai sai ta Dafa Ruwan Tea,ta jera saman Dining ta shige Dakinta ta fada wanka a gurguje ta Shirya,Daman Inteesar tace su saka Kayan da Umma ta Dinkamusu shi ta saka ta Sagalo Mayafin kayan Sea green.
Har zuwa Lokacin ba wanda ya Tashi,Tea ta Hada ta sha ta Hada da Dankalin kana ta koma Dakin Abba ta Iskeshi ya gama Karatun yana Zaune kan Darduma yana jan Cashaba ta Duka ta gaisheshi ya amsa mata yana Shafa kanta Nan take yagamai Zata je gidan Mama Inteesar ta Kirata Abba yayi mata Fatan Dawowa lafiya ta Fice Tana Fadamai Ta Hada Breakfast tun dazu yace mata Allah yayi mata albarka ta amsa da Ameen bayan tace mai in Anty Safiya ta fito ya gayamata ta tafi yace tom.
Koda ta Fito Daga Gidan nasu 10 ne da wani abu na Safe,batayi wani Tafiya sosai ba ta iso Gidansu Sagir a kofar gida ma ta Ganshi yana mgana da wani suka gaisa ta shiga Ciki ta iske Mama na gyaran Wake a Tsakar gida ta Rankwafa ta gaisheta Ta amsa mata Cikin Fara”a Tana Tambayanta Mutanen gidan nan ne mama take Fada mata Zataje bikin Diyar yayanta kaduna Kafin ta tafi zata zo tama Abba Mgana Inteesar zata zauna dasu kafin ta Dawo Munari baki kamar ya Tsinke saboda Murna…
Haka ta shiga ta iske Inteesar ta Shirya itama cikin irin kayanta tayi kyau sosai.
Zama gefen gado Munari tayi Tana Fadin”Ke Mama tace zaki dawo gidanmu kafin ta dawo Daga kaduna..!
Inteesar na Saka Sarka a wuyanta Tace”Eh nima jiya take fadamin..Bazan iya zama ni kadai ba,Ya Sagir ma Ranar asabar zai tafi Daurin aure..!
Munari tace”Wai bikin waye za”ayi a kaduna..?.
Inteesae tace”Bikin Anty Jamila Diyar Kawu Bala shine babba a Dakin su Mama..!
Munari tace”Allah Sarki Shine ke bazaki ba ko..!
Hararanta Inteesar tayi kafin tace”Sai na bar miki karatun nawa kenan ko..?
Munari batace komai ba Tana Dariya,Suna Hiransu Sama sama har Inteeaar ta gama Shiryawa,Tana so ta Tambayi Munari Imran sai ta kasa sai chan wata Dubara ta Taso mata ta Kalli Munari tana Fadin”ya su Abba..? Ina Anty Safiya da Ya Yusuf ina Dan Rigiman gidan ku Ya Imran..?
Munari tace”Ban hadu da kowa ba yau sai Abba..Kinsan yau Lahadi su Anty Safiya basa Fitowa da Wuri..Ya Imran kuma ina Tunanin ya Fita Jogging Tun dazu har ya Dawo..!
Inteesar tayi shuru Tana Tunanin tama manta yana Fita Da Safe Motsa Jiki,Data fita ko kofar gida da Safe ne taga ko Zata gansa..? Wata zuciya tace ki gansa a saboda mene..? Da sauri ta ba kanta amsa saboda in karamai Godiya ya Ceci Rayuwata.
Daganan bata kara cema Munari komai ba ganin sun gama Shiryawa yasa ta daga waya ta Kira Ya Sadam sai dai wajen kira Hudu bai Dauka ba Sai ta Kira Anty Aneesa take Fadamata Tana jin haka tasan aiki yayimai yawa a asibiti in tace su jirasa zasu kai wani Lokaci kawai sai tace su Fito su samu mai adaidaita su Kirata su bashi tamai kwantace in suka zo Zata Biyasa
Haka kuwa sukayi bayan sun ma Mama Sallama suka Fice wajen 11am naSafe suna Fita Kofar gidan bakin Shagon Sagir suka ci karo da Imran yana Tsaye sanye cikin Riga da wando na Jc Mai ruwan ganye ya Tusa duka Hannuwansa cikin Aljihun wandon,Kafarsa sanye cikin wani Takalmi mai kama da Silifas Gefensa Sagir ne kamar suna mgana ne Munari ce ta Fara ganinsu ita Inteesar nachan tana Kokarin gyara Zaman Karamar Jakar Dake hannunta
Yafito Inteesar tayi tana nuna mata Imran Lokaci Daya Tana fadin”Mun shiga uku Intee Ya Imran..!
Da sauri ta Dago Tana kallonsa Shima Daidai Lokacin Daya juyo suka Hada ido Dukkansu sai da sukaji Zukatansu sun amsa Ajiyar rai Imran ya Sauke na Samun Natsuwar zuciya daya ganta haka Tun jiya Daya koma Gida ya kasa Barci Saboda Tunanin Halin da Inteesar ke ciki Tun da Safe ya Fito Joging har Kofar gidan nan ya zo ya Tsaya ko zai ganta Shuru,bai ganta ba ya kasa Natsuwa yana so ya ganta ya Tabbatar da baatayi ta kuka ba kuma Lafiyanta kalau ya koma Gida ya kasa Natsuwa,Abakin Abba yake jin Munari bata gida tazo wajen Inteesar zasu anguwa yana Fadama Ya Yusuf da Matarsa Shiyasa ya Fito Domin ya ganta ya samu Sukuni yana ganinta yaji kamar anyimai gafara.
Itama anata Barayin hakane wani Sanyi Sanyi taji yana Shiga Jikinta Basar da su yayi ya Dauke kai kamar bai gansu ba Sagir ne ya gansu ya Saki Fuska Inteesar ta kamo Hannun Munari suka karisa gabansu Dukkansu suka gaisheshi Sagir ne kadai ya amsa su Gogan kuwa sai ma Dauke kai kansa da yayi kamar bai gansu ba nan kuwa,ya gansu yana ma ta Satan kallon Inteesar ne ta Gefen ido.
Har suka wuce suka Fara Tafiya zuwa Bakin Titi yana Kallon Gefensa baya so Sagir ya Fahimci ya Bisu da kallo sai da suka dan Dade da wucewa kana ya Hangesu Daga chan suna Tafiya Kadafa da kafada da Munari sun rike hannun juna acikin ransa sai da yaMurmusa yace”Ji besu kamar wasu yara..Kaya iri Daya kuma sun wani rike hannun juna..!
Shikadai abun ke bashi Nishadi,ganin ya Riga ya ga abunda yazo nema yasa Sagir namai Hira sama sama yake jinsa Daga Karshema yace mai Zai je gida sukayi sallama Daganan Sagir ya Koma Cikin Gida shi kuma ya Nufi Hanyar gida.
Suna zuwa bakin Titi suka Samu mai adaidaita suna Shiga Anty Aneesan na kira bayan ta dauka take Tambayanta suna ina ne..?
Tace suna cikin adaidaita sai tace ta bashi wayar ta mikamai ta mai kwantace yace ya gane wajen gasunan yanzu zai kawosu,nan ya mikama Inteesar tace mata sai sun iso.
Sun dauki Hanya kenan Wayar Inteesar tashiga kara tana Hannunta ne Tana Dagowa taga lambar mai Kiran ta Saki wani Siririn Tsaki batayi Sarving din Lambar ba ammh nacin Kiran Dayake mata yasa ta Haddaceta Saboda bata so ya Kira ta Daga..
Haka ake ta Kira bata Dauka ba Munari Dake gefenta tace”Wai hala baki ganin ana ta Kiranki ne..?
Inteesar ta tabe baki kafin tace’Ina gani bazan dauka bane..!
Munari tace”Eyye ko an yi sabon gaye ne Shine ba”a son Daga wayar agabana..!
Inteesar ta Harareta tana Fadin”Allah ya kyauta wannan ya Zama Saurayina..Ya khamis ne Dan Baffa Kabiru na Abuja Tunda mukaje Dukku lokacin nan ya nace min ya Samu Lambata ban huta ba yayi ta Kirana ni kuma Wlh bai min ba sam..!
Munari tace”To miye aciki Don ya Kiraki ku gaisa..!?ai ba cewa yayi yana sonki ba Besty..!
Inteesar tace”In na bashi Dama haka zai ce..Ni kuma bai burgeni ba Asalima Haushi yake bani..!
Munari tace”Kedai kowa ma sai kice yana Baki Haushi..Naga mijin ki kuwa..kilama Gajere ne baki mai Katon kai da..!
Inteesar ta katseta da Fadin”Ba Ameen ba Muguwa insha Allahu Mijina Ba kamarsa yarinya..!
Dariya Munari ke ta mata ita kuma ta sha mata kunu gashi Khamis din yaki Daina Kiranta sai kawai ta Kashe wayar In sun isa ta kunna Kila in yaji Tana Kashe ya Hakura.