
Ko Tak Imran bai ce mai ba sai ma Tabarsa Daya kara Zuka ya Daidaici Fuskar Alhaji Alhassan ya Sakarmai Hayakin da sai da yayi Baya Cikin Firgici yana kallon Imran wanda yayi Mirmishi ya Dagamai Gira yana Fadin”Ya akayi..? Ka tabbatar yanzu.? Ba Wani Dogon Surutu ya kawoni ba..Miye Dalilinka na Hana yayana Auran yarka..? Ya fada Cikin Tsuramasa Idanuwansa Kamar yana Bashi Umarnin yayi mgana Alhaji Alhassan mamaki ya kara kamashi Sagir kuwa yana Gefe bai yi mgana ba sai addu”a yake aransa kada Alhaji Alhassan ya Fadi wata mgana kan Gidansu ko Mahaifinsu yanzu ayi mara Dadi kamar yadda Kwanaki ya Faru da abokinsa KB a Shagonsa Suna Hira sai Imran yazo wajensa Bama dashi ake Hiran ba Cikin Labarin ne Kb ya sako mganar wani Mahaukaci su dai basu yi Aune ba sai Hakorin Kb da Jininsa suka gani a kasa Imran ya Naushemai Baki da sunan wai Dashi yake da Abbansa yake kwatance Fadan da yaso har Hukuma ta Shiga Ciki Shi yayi ta bama Kb Hakurin har ya Hakura ammh da Imran yaji cewa yayi Duk wanda ya bama Kb Hakuri ya Hakura Uwarsa taci Uwatai.
Shiyasa yake ta Tsoron kada Hakan ta kara Faruwa yasan Imran kamar Yunwar Cikinsa zai iya komai ga Duk wanda ya aibata GiDANSU.
Alhaji Alhassan da Ransa ya gama Baci ya Fara Fada da Bambami yana Fadin”An hanashi din..? Nace an hanashi din Zaka aura masa ita ne..?ko yarka ce.?Ina ce Ni na Haifeta kuma ba wani iko da ita ba.? Ko Uban wani ya Haifamin ita ?..”Ya Karishe Fada har kumfar Miyau na Biyo bakinsa.
Imran Dake zukan Tabansa ya Dakata yana kallon Alhaji Alhassan kafin yace”Ammh dai Uban da ka zaga ba namu Uban ka zaga ba ko..? Yadda yayi mganar ne yasa Shakkarsa Ta Shiga Alhaji Alhasan ya juya kai Baiyi mgana ba Mirmishi ya saki kafin yace”Nagane..Ba Dogon Turanci nace kamin ba Malamin Kimiya da Fasaha Dalilinka kadai zaka Fadamin..”Alhaji Alhassan yace”In Kaji Dalilin sai kuma yaya..? Nace sai kuma Yaya..?
Imran ya Zakuda Kafafa yana Fadin”Sai yaya kuwa..? Iyaka in Dalilin bai min ba na saka Ka Dole ka Kira yayana ka bashi Go Ahead kan ya Turo magabatansa..”Zaro ido Alhaji Alhassan yayi kafin yace”Ni..? In hada Zuru”u da irin Mahaukata Irin Tantiranci..uwa uba ga Rashin asali da Nasaba Gidanku ba Tarbiya ba kwaba Domin Tunda kuka zo garin nan Daga ku sai Mahaifinku albarkan zaman mace ma agidan baku samu ba kuna Zaune kara Zube sai ni Saboda bani da Tunani na Dauki yata na bakku.? Ai sai kimata da Mutumcina ya…!
KAIIII…!Ihun da Imran ya Kwatsa kenan Lokaci Daya ya Daga Hannunsa sai Sauke ma Alhaji Alhassan wani Naushi wanda inda ya samesa sai ya Raunana Domin Tabbas Hakoransa na Gaba sai sun watse sai Dai Sagir ya Ceceshi Daga Hakan Ya Tare Imran Da Rikoshi da Karfinsa yana Fadin”Imran..Imu..Ka bari Don Allah..Kada ka Tabashi Don Allah..”Yake fada yana Rikesa da kyau ganin yadda yake wani Fizga Idanuwansa sun kala sun ji Jajir Tuni jijiyoyin kansa suka Daga haka yake sakin Hucin bakinciki da Hannu yake Nuna Alhaji Alhassan Dayayi gefe Tun Hargagin Imran yana maida Numfashi Cikin Muryansa mai Cike da Amo yake Fadin”Who is He da zai Fadi wata banzar mgana kan Gidanmu.? Shidin banza waye shi..? Wlh da barni da yanzu Bakinsa ya Cikada Hakoransa da Jini Kai har kana da Bakin mgana Kayi gaggawan bama Yayana Dama in ba Haka sai na Fallasaka agaban iyalanka gasunan suji su kuma Fahimci wani irin Uba ne Allah ya basu..”Ya karishe Fada yana Nuna su Safiya da sukaji Hayaniya Daga Haraban gidan suka Fito kuka kawai take Tunda Taga Imran duk bata taba ganunsa tasan sunan abakin yusuf kuma daga mganarsa ta Fahimci ko waye shi.. kanwarta Tasleem Tana Ta lallashinta Hajiya Mero kuwa Mahaifiyarsu kallon Imran take Tana kuma Kallon Alhaji Alhassan da Tunda yaji mganar Imran gabansa ya Fadi kardai yasan Sirrinsa na Neman matan Dayake yi..? In ko hakane ya Shiga uku Gwara ya basu auran Safiya daya Fallasa wannan Sirrin wanda Bayyanarsa zai yi Sanadiyar Kimarsa da Darajansa da Mutumcinsa da kuma aikinsa Dayake takama Dashi
Yin wannan Tunanin yasa Jikinsa na rawa ya matsa kusa dasu Imran yana Fadin”Kaga ba sai an kai ga Haka ba..ku Turo mgabatanku Shikenan Tunda kun nace itama ta nace sai shi..”Yafada yanawani fiki Fiki da ido na marasa gaskiya Sagir Sai da Dariya ta kusa kamashi Imran kuwa Hannunsa ya Fizge Daga na Sagir ya Tura Hannu a aljihunsa ya Dauki kwalin Tabansa Har ya karar da ita Saura Daya ya Daukota ya Jefar da kwalin ya Jawo makunni ya kunnata ya Zuka ya Fesar da Hayaki kana ya kalli Alhaji Alhassan da Jajayen manyan Idanuwansa yace”Ka kira Yayana ka sanar dashi yanzu..NAN..! Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Alhaji Alhassan yace”Yanzu kuwa..Insha Allahu..”Yafada yana rawan Baki Imran bai Saki Fuska ba ya Taka Hargaban Safiya bai Taba ganinta ba sai sau Daya da Yusuf ya taba nuna masa hotonta duk da bai wani kalleta ba sosai ba,da Jajayen idanuwansa ya kare mata kallo Daga sama Har kasa Tasleem kuwa bayanta ta Labe Tana Toshe Hanci Daya lura da ita tsawa ya Daka mata yana Fadin”Ke….’jiki na rawa ta Dago kanta tana kalleshi cikin Dakiya yace”Ni sa”an ki ne da kike ganina kina Tushe Hanci..? Maza Bude Hancinki kafin ki Tunzurani na Targaki yanzu agaban Iyayenki..!”Da Sauri Tasleem ta saki Hancinta Tana rawan Jiki ta kamkame Bayan Safiya Da kanta ke Duke Tana kuka Hajiya Mero kuwa gum Tayi da bakinta batayi mgana ba Duk da itama warin Tabae ta isheta sai dai ba Halin mgana ganin yanayin Imran din ya Firgitata ta tabbata ko ita ba Shakkarta zai yi ba balle ma Dataga Shi kanshi Alhaji ya Saduda
Safiya ya kallah kafin yace”Bhabi..Stop craying…Kin auri Yayana kin gama..See u sai mun Hadu a GIDANMU..”ya karishe Fada yana wani Mirmishi kafin ya Zuki Tabarsa ya Fesa musu Hayaki kana Lokaci Daya ya Juya yana wani taku Daya Bayan Daya yana wani Rangaji ya Fice Daga gidan Sagir ya maramai Baya Megadi ya Bisu da Allah ya Kiyaye sai da Alhaji Alhassan yaji tashin Mashin din Imran kana ya iya Motsi Juyawa yayi yana kallonsu Kafin ya Fara Bambamin kunya.
“Tsayuwar mu kuke yi kukama..? Ai sai ku shiga Cikin gida…Ke Safiya ki kira shi yaron kicemai ya Turo manyansa Tunda irin Gidan da kika Zaba kiyi Rayuwa kenan ke kika sani..”Daga haka ya Saba Zaman babbar Rigarsa ya nufi Motarsa Direbansa ya Budemai Bayan Bakar prado dinsa ya Shige yana jin Zufa na ketomai Kafin Direba ya Shiga Bangaran Direba yayi Rivers Ya yi Hon megadi ya wangale get suka Fice sai alokacin Safiya ta Juya Cikin gida da Gudu Tana Dariya da kuka Tasleem ta Mara mata Baya kana Hajiya Mero da Jikinta ya gama yin sanyi da al”amarin Data gani.
Imran kuwa Har ya maida Sagir bakin Shagonsa bai ce mai kanzil ba sai da ya ijiyesa kana Sagir ya kallesa yace”Mama Tana ta Cigiyarka..”Imran yayi Mirmishi kafin yace”Kace mata Zan shigo Gobe..”Daga haka ya Bama Mashin Dinsa wuta ya wuce ya bar Sagir da binsa da kallo har ya Bacema ganinsa bai koma Shagon ba ya Nufi Gidansu Dake Jikin Shagon nashi Domin ya Dauko wayarsa da Littafansa ya Shiga makaranta.
Yana Shigowa Falon ya ci karo da Yusuf sai washe baki yake Cikin Murna ya Sarke Hannayensa yana Fadin”Bro..Wai me kayi ne..?Yanzu Safiya ta kirani tace Abbanta yaje na Turo Manya..Am so Suprise Mutumin Daya gama Rantsuwan jiyanan bazai taba bani Auran yarsa ba sai gashi yau da kanshi yace na Turo manyana..”
Mirmishin Jin Dadi Imran ya saki ganin Dariya a Fuskarsa Dan”uwansa Hannunsa ya Zare kafin ya Dafa Kafadarsa yana Fadin”Imran kaifi Daya ne..Yana Cika Duk Abunda yace..So sai ka Fara Shirye Shirye ka kusa Zama ango akalla bayan Wasu Shekaru zamu samu wata mace zata karu acikin GIDANMU..!