
Gidan Abba cike da Mutane sai godiyar Allah haka Mama da Sagir suka zo sukaji Abun al”ajabi Sagir yace Wlh ranar daya fara ganin Daddyn Intee sai da ya ga yamai kama da wani sai dai ya rasa ta ina zai kama kamannin,Ashe ashe suna kusa da Danginsu basu sani ba Mama sai mamaki take ashe Abba yaya yake wajen Mijin kanwarta Salaha Allah ne abun godiya,duk da Sun shiga rudanin Dalilin wannan lamarin sai dai basu ce komai ba suna da Tabbacin yadda wannan ya fallasa to sauran Dalilan ma Zasu jisu in Lokaci yayi.
Sai murna ake da Farinciki ana maida Zence,Sadam kuma Tuni ya Hau WhatApps ya shiga Group din Marigayi Alkali Dukku ya bada Sanarwa da gargadin kada wanda ya Kira Daada ya fadamata sai Gobe kowa da kowa za”a hadu a Dukku.
Basu an kara ba sai dai sukaji kiran Sallar Isha”i kana zaman ya tashi Matan suka Shiga ciki domin gabatar da Sallolin da suka Subuce musu mazan kuma suka Dauro alwala suka Ja Sahu anan Falon Yusuf yayi musu limanci Abba da Sadam da Sagir da Imu suna Binsa abaya wanda Har zuwa wanna lokacin bai ce komai ba yana so ne sai an zo gabar da zai tanka yanzu ba Lokacin mgana bane.
Bayan sun idar ne aka sake Fitowa aka Hadu afalo ana jiran sauran Baki,saboda Murna ba wanda ya Nemi abinci sai Imu daya Shige daki ya Busa abarsa,abu daya ke sashi Farinciki zuwa Biyu ayau dinan Shine na Farko yaga Inteesar Cikin Farincikin da bai Taba gani ba na Biyu yau din Ranace da zai Rama wasu abubuwa da suka Shude shekarun baya yana Fitar da Hayakin Taba yana Mirmishinsa na saman Lebe Lalle ya yi Shuru shekaru uku da suka gabata ammh awannan gabar ba wanda ya isa ya hanashi mgana koda Abba ne da kansa.
Safiya ta Kira Mommynta tana Fadamata abunda ke faruwa jin haka yasa Hajiya Mero murna tana farinciki ko banza Alhaji Alhassan zai ji kunya Daga yadda Safiya ta bata Labari Dangin yusuf din ba mutaenan banza bane suma wasu ne Ita ta roki Hajiya Mero da ta saka yan aiki suyi musu abinci mai yawa saboda baki abama Direba ya kawo da Sauri Hajiya Mero ta amsa mata suna Sallama ta Fita zuwa Kitchen tana bama masu aiki Umarni kafin ta afito Ta Nufi Dakin Tasleem ta Fadamata wannan abun Farincikin.
Sa”id shi ya fara iso Tunda shi yafi kusa,yana Shigowa ya Kira Sadam shi yamai kwantace cikin Lokaci sai gashi ya ya iso shi da Yusuf suka Fita Tarbansu.
Sa”id ya Rumgume Yusuf suna Murnan ganin juna,da iyalansa yake tafe Harda Hafsah dataji Labari tace sai tazo itama.
Dukkansu suka Dumguma zuwa Cikin gidan sai ga Sa”id sun Rumgume da Abba suna murnan ganin juna Fareesaatu ma ta gaisheshi ya amsa yana Daukan ya’yansu na Karshe ne Abubukar takwaranshi kafin ita faresan ta Karisa Wajen matan ana ta gaisawa Hafsat suka Rumgume juna da Inteesar,bayan ta gabatar da junansu da Munari suka Rumgume suna Murnan Haduwa da juna Anty Safiya Tana ta ina ta sakasa dasu,mama da Sagir suna nan zaune suna ganin ikon Allah..
Sa”id kam shi sai da ya Rumgume Imran ammh yaki tabasa shi baima Tsaya Wani lura da lamarinsa ba.
Akwai salloli agabansu yasa Safiya taja Fareesan zuwa Shashenta Sa”id kuma Da Sadaam Yusuf ya sauke su Tsohon Bedroom dinsa
Ba Dadewa sai ga Direban gidansu Safiya da kololin Abinci manya manya Daman Tun tasowarsa Mommy ta Kira ta fadamata to da iro ya shigo yana Fadin an kawo sako tasan kwanan zencen iro kuwa sai Raba ido yake tun sanda Bakin Motoci da Mutane keta shigowa gidan nan Abunda bai taba gani ba so yake yaji ina ba”asin Lamarin..!
Anty Safiya dasu Inteesar suka Taimaka mata suka Shishigo da kololin Abinci zuwa Kitchen da suka ce a zo aci abinci ba wanda yabi takai ana Jiran isowar su Daddy.
Karfe tara da rabi na Dare goma Saura su Daddy suka shigo Anguwan gadon kaya,Dayake susan gidan Zuwan bai musu Wahala ba.
Abba najin Dan”uwansa ya iso baima Tsaya ba ya fice zuwa Haraban gidan Tunda ya fito Daddy dake gaban Mota ya kyalla ido ya gansa ya balle Murfin Mota ya futo suka Nufi juna suka Rumgume sai kuka,Sauran duk suka Biyosa abaya banda Imran daya na chan Dagachan gefe…
Yusuf da Basheer suka Rumgume juna suna Murna Inteesar ta Rumgume Umma cikin Murna kafin suka Rankaya zuwa cikin gida..
Abba da Daddy suna Rike da Hannun juna ganin kamar mafarki ne nan aka Shiga gaisawa da juna Umma ta Rike Mama suna kara mamakin wannan al”amarin ta Rumgume Munari tana jinta kamar Inteesar,suka gaggaisa da Su Sadam da matansu da Ya yusuf da Anty Safiya Imu na gefe chan Saman Dining ya Harde Hannayensa saman Kirjinsa yana kallon kowa Daya bayan Daya ba ma wanda ya Damu dashi.
Sai da Daddy ya tambayesa ne kana aka fara Waigen waigen nemansa chan aka gansa Zaune Daddy bai jirasa ba ya Mike ya isa garesa yana Fadin”Asshe ashe..Imran din da Inteesar ke bamu labari ashe jininta ne yayanta ne Salaha..!
Gabadays kowa sai mamaki daman Inteesar na basu Labarin Imran ne Ita kuma sai kunya ya kamata ta Noke bayan Umma Tana Leken Imran da Daddy ya Rumgume abun mamaki yadan Saki Ransa kadan sai dai suna Hada ido da Inteesar ya Hade rai bayan ya Harareta aranshi yana ayyana Rainin da yarinyar nan tamai.
Daddy ko awa daya basu yi da isowa ba Baffa Kabiru suka iso suma da kwantancen suka iso Gidan Abba.
Tundaga Haraban gidan Mami Asma”u ke karema komai na Gidan kallo acikin ranta Tana fadin ashe yama samu wani jin dadin Rayuwar duk da yabar komai nashi abaya.
Shima Abba da Daddy da sauran Mazan suka Fito Tarbansu Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Abba Shar dashi Cikin Koshin Lafiya ya Zata zai gansa duk ya lalace ne saboda Halin Rayuwa hakama Mami Asma”u take kallonsa kamar bashi ba ya kara Kiba ya samu jin dadi ya bar Mijinta na Wahalan nemansa.
Duka suka Dunguma zuwa cikin Falon a karo na ba adadi.
Baffa Kabiru yayi mamakin ganin Yusuf da Munari da Imran dey look so nice daga gani basu da Wahala ko daga Gidan da suke ciki Dukkansu sun gaisheshi banda Imu dayayi kamar ma bai ganesa ba Yana daga chan inda yake Zaune Hannayensa a Harde yana Kallon kowa sama da kasa.
Mami Asma”u sai bin kowa take da kallo Mamaki bai kasheta ba sai taga Matar Yusuf Safiya abun ya kara bata Haushi Bata Damu da yaran dake Wajen ba ta Bude tace”Ba shakka..Abban Sajida kuke chan kuna Wahalan nemansa bakwa barcin kirki Daada kuma na chan Hawan jini ya kamata tana kwana kuka Saboda Tunanin dan”uwanka Shi kuma yana nan ya samu Sabuwar Rayuwa da Sabon gida.ba shakka..!
Take fada kanta Tsaye tana gyara Zaman gilashin idanuwanta Kowa sai da ya Kalleta Abba ya Murmusa yana kallonta yace”Barrister Asma”u Tafida kina nan da Halin nan naki kenan..!
Kallonsa Tayi cikin ido kafin tace”Dr.Abubakar Hamisu Malami ashe baka manceni ba..!
Tafada Lokaci Daya tana dan Sakin Dariya ganincyadda aka Sako mata Ido Mirmishi ya saki Cikin natsuwarsa yana Fadin”Ban manta dake ba..!
Yafada Lokaci Daya Daddy da Baffa Kabiru suka Bisa da kallo komai nashi bai sauya ba Hatta mganar Abba da Tafiyarsa kana gani zaka san baida Hayaniya Ballatana Fada.
Imu na gefe yana jin Abunda Mami Asma”u tace aransa yace anzo wajen ya ganeta Sarai duk cikin matan Baffaninsa yafi saninta da kowa saboda Lokacin da Su Anni suka Rasu suna Dukku duk zuwa da ita ake zuwa ta kuma Taya Mijinta aibata Abba agabansu abaya in sunyi sunci riba wannan karon sai ya Tabbatar musu da ba wanda zai kai Labari..
Kafin suci abinci sai da su mami Asma”u suka gabatar da Salollin dake kansu aka baje afalo aka ci Abincin da Hajiya Mero ta aiko dashi Abinci kala kala sai wanda ka Zaba.
Bayan sun gama ne yara yaran suka Kwashe komai zuwa Kitchen aka kara zaman Hira Abunda yabama Mami Asma”u mamaki Imu ne ganin kowa yaci abinci bandashi da Daddy yayi mgana sai Abba yace haka yake bayason cin Abinci Tana gani daya tashi Zai shiga Dakinsa kamar Hararanta ma yayi kafin ya shige.
Tasan yaron abaya da Tsaurin ido bata Taba Zaton Abunsa yakai haka ba.
Isu isu ne zaune afalon Mama da Sagir tun zuwansu Daddy ba Dadewa sukayi musu sallama zuwa gida mama tace sai da safe.
Ana ta Hiran yaushe gamo Inna Bintalo ta kira har sunyi mgana da Abba ita da megidanta suka Rabu kan sai gobe in sun hadu a Dukku.
Baffa Kabiru ya gyara Zama yana Fadin”Malami ka samu Lafiya sosai..?
Abba na Mirmishi yace”Alhamdulillah..!
Baffa Kabiru ya jinjina kai yana Fadin”Alhamdulillah duk da akwai mganganu da yawa a bakina ba Lokacin Fadansu bane yanzu sai In allah ya kaimu gobe mun isa gaban Daada..!
Abba ya gyada kai baice komai ba Baffa Kabiru ya cigaba da Fadin”Gobe sai ka shirya kaida iyalanka..Damu gabadayanmu zamu isa Dukku da yardan Allah..!
Kamar daga sama sukaji Muryansa cikin Amo da Cikar Kaushin kamar yadda ya saba.
“Ba inda Abba zai je..Kuma muma bazamu mu biku ko”ina ba..!
Gabadaya falon aka juyo ana Kallon Barayin Inda mganar ta Fito.
Imran ne tsaye a kofar dakinsa ya Sanya Hannunsa guda daya cikin Aljihun bakin wando dake jikinsa Hannu Daya kuma Tana kan bakinsa yana Rike da Karan Sigarinsa.
Bai damu da yadda ido ya dawo kansa ba ya lumshe manyan idanuwansa kafin ya Bude su tas kan Baffa Kabiru Lokaci daya Hayakin daya zuga ya Fesar dashi ta Hanci ta baki zuwa Saitin Fuskar Baffa Kabiru.
Gabadaya Falon jikin kowa yayi sanyi,ido kowa ya Fiddo waje cikin mamakinsa da ganinsa acikin wannan Halin Banda Abba da ya yusuf da suka Dafe kai cikin Tsantsan Takaichi da bacin rai.