GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Janafty..
3/22/22, 23:13 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?3

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Daganan aka tashi zuwa sallah,Mazan gabadaya masallacin kusa da gidan Daada sukayi sallah wanda Tsohon masallaci ne Tun marigayi Alkali Hamisu dukku nada rai.
Bayan sun dawo aka Hadu a falon zaman cin abincin da Baba Asabe ta girka da Taimakon su Zainab, suka kamallah komai,Daada da ya”yanta suna cikin Dakinta sun kule kansu,suna Hirar yaushe gamo Daada Tana Zaune su Abba sun Zagayeta Farinciki ya cikata yau Allah ya cika mata Burinta malami ya dawo cikin Ahalinsa,Tana kallonsu tana Sharan Kwallah ta gefen Hannunta Cikin bayyana Farincikinta,ko abinci ma nan ciki Baba Asabe ta kawo musu yara yaran ne ke Falo suna cin Abinci.
matasan mazan kuma Haraban gidan suka Fita Baba Asabe ta Kawo musu babbar Darduma suka Shimfida suka Zauna suna cin Abinci banda Imran Wanda yake gefe zaune kamar Dole jakarsa Har Lokacin Tana Sagale a bayansa yaki yarda ya ijiyeta.
Lokacin da aka kawo abincin da Yusuf yamai mgana sai yace bazai ci ba su Sadam mamakinsa ya ishesu ganin Tun suna Kano basu ga Imran yaci komai ba Ta yaya mutum zai Rayu ba abinci.
Haka Sadam yayi ma Yusuf wannan Tambayar Lokacin da suke cin Abincin Mirmishi kawai yayi yana kallon Imran dake chan gefe kan wani Dakalin gini da aka yi domin Zagaye Fulawowin haraban gidan kafin ya Daga ido yana kallon Sadam yace”Abinci bai damesa ba..Sai ya kwana ya Wuni haka bai damu ba..!
Sa”id na kai Lomar Shinkafa yace”Tab..Kuma lafiyarsa kalau..?
Wannan karon Sagir ne ya kada kai yana fadin”Shi yafi bama Ruwa Muhimmanci fiye da abinci..Sai kuwa Busa Hayaki..Abu na karshe Fruit da kila dasu daya ci ko bada yawa ba..!
Kowa kai ya jinjina suna kara mamakin Imran na wani Lokaci daya suna Juyawa suna kallonsa shi kuma Tunda yaga haka jikinsa ya basa Mganarsa akeyi,Daman Haushin Sagir yake ji yadda ya wani Sharesa ya shige cikin su Sadam suna Hira kamar sun Shekara tare,Sai faman aikamai da Harara yake yi shi kuwa baima bi ta kansa ba cin abincinsa kadai yake yi suna Hira Sama sama.
Imran da ya gaji da zaman hakan nan ba wani abun tabawa ya Dauko Karan Sigarinsa dake cikin Aljihun wandonsa ya kunnata ya shiga Zuka yana Fesar da Hayaki Ya Basheer ya kallesa yana Fadin”Ikon Allah shi kuma nashi Abincin kenan..?
Gabadayansu suka juya suna kallonsa shi baima san sunayi ba Idanuwansa suna Lumshe ne yana jin Dadin yanayin Dayake ciki.
Sadam ne yace”Gaskiya ya kamata Yusuf ayi wani abun da zai sa ya rage shan wannan Hayakin ko saboda Lafiyarsa..!
Yusuf yace”Ina ta rokon Allah ya yayemai shanta kamar yadda Allah ya Doramai shanta Lokaci Daya..!
Jin ya Fadi haka yasa suka amsa da Ameen Tunda ya ambaci Allah ai ya gama komai.
Gefe kowa ya koma ya Fiddo wayarsa Lokaci daya suna Taba Hira,Yusuf dashi da Sadam ne suke ta Hiransu Yana bashi Labarin group dinsu na WhaApps nan da nan yace ga Lambarsa ya sakasa shi kuma Basheer dashi da Sagir suke Hiransu Sa”id yana saka musu baki Lokaci bayan Lokaci.
Sun juma suna Hiransu kafin Hauwa ta kira Basheer a waya ya tashi zuwa Gefe suna mgana sai Hiran ta Koma kadan saboda Shima Sa”id ya maida Hankalinsa kan wayarsa ne ganin haka yasa Sagir ya mike ya isa Inda Imran ke Zaune ya gama Busa Hayakin ga Sauran Sigarin nan a kasa Daya gama ya Taketa,gefensa ya Zauna yana Fadin”Abokina ka dinga shiga Mutane don Allah..!
Kamar ma baisan yana Wajen ba kansa na kallon gefensa sai chan yace”Ai shiyasa naga kai ka shiga Cikin su ka manta dani..!
Sagir yace”Ah to tunda kai baka san shiga mutane ni sai naki shiga..!?
Imran ya waigo yana kallonsa yace”Eh saboda ni na gayyatoka..!
Yafada Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska Sagir yace”Eh ai ban ce bakai ka gayyatoni ba ammh su Ya yusuf ne fa ba wasu ba balle kace..!
Imran yace”Ya yusuf din shi kadai ne..? Wadanchan ba wasu bane..?Sagir ya saki baki kafin yace”Su waye wasun..? Chan fa duk yan”uwanka ne Imu..!
Baki ya tabe kafin yace”Eh ammh ai ban saba dasu ba..! Sagir yace”To ta ina zaka saba dasu baka Shiga cikin su ba..!
Imran yace”Ashe kuwa bazamu taba Sabawa ba indai sai na Shiga cikinsu..Kai ni ko Ya Yusuf a wasu Lukutan ban son zama dashi nafi son zama ni kadai..!
Sagir yace”Allah ko ya rabamu da zaman kadaici..Sai kayi ta zama ni dai sai na shiga cikin mutane..!
Yafada yana Shirin mikewa Imran ya dago kansa yana Fadin”Baka isa ba..Dawo ka zauna..!
Sagir ya kallesa kallon Mamaki kafin ya Girgiza kai yana Fadin”To Ubana Tasiu..Ko Uwata Amina..!
Yafada yana komawa ya zauna cikin dan bata Fuska yadda Sagir ya Fadi mganar ne ya bama Imran Dariya Har sai da ya washe fararan Hakoransa a waje wadanda bakasaifai ake cika ganinsu ba Sai ga dariya Lokaci Daya mai Sautin da Har sai da ta bayyana Su Sadam dake gefe suka Juyo suna kallon Abun mamaki
Sadam ya kalli Sa”id shima ya kallesa Kafin su kalli Yusuf Sadam yace”Kai ashe yana Dariya..Tun haduwarmu ko Mirmishinsa ban gani ba sai yanzu naga yana Dariya..!
Yusuf na Dariya yace”Yana Dariya mana..Ammh Tana da Wahala kaga yayi irin wannan Dariya bakomai ke Burge imu ba ballatana ya sakashi Dariya haka..Yafi yin Mirmishin Fatar Bakinsa in hakan ya zama kamar in muma mgana dashi haka..Irin wannan Dariya kuwa da Sagir kadai yake yinta ko dani in na Tsokaneshi..!
Gabadaya kai suka Jinjina Basheer ya kada baki yace”Allah mai iko..!
Sadam yace”Kuma mai Mutane kala kala..!
Dariya suka saka gabadayansu Sa”id yace”Tunda munsan Halinsa sai mu ci mganin zama dashi..Azauna Lafiya In ji Sadam daya Karishemai suna mganar suna kallonsa yadda yake Dukan Kafadar Sagir yana Dariya shi kuma ya saka Kafa ya Taka takalminsa yana Hararansa.
Lura da yayi suna kallonsa yasa Dif ya Dinke Dariyan tasa ya koma ya Hade rai kamar yaga Mala”ikan Daukan Rai su abun ma sai ya basu Dariya suka koma suka cigaba da abunda sukeyi Lokaci Daya suna Hira sama sama Shima din Hirarsu da abokai suke shida Sagir wanda Rabin Hirar Sagir ne Sauran mganar Imran din duk Gatse Gatse ne cikin yanayin mganarsa.
Sai da aka Kira mangariba suka tashi Daga wajen nan zuwa masallaci shima sai da su Abba suka Fito ne suka Tasasu zuwa masallacin basu koma Dawo gidan ba sai da sukayi Sallar Isha”i abunda yakara bama su Daddy mamaki Imran da Jakarsa yaje masallCi ya ijiye ta agefensa da zasu Fito ya Dauko kayansa mamakin hakan Yasa sai da Daddy ya maganta suna Hanyar Dawowa ya cema Abba”Shi Imran bai yarda da kowa bane..?
Abba yace”Saboda me kace haka..?
Daddy yace”Duba fa kagani Tunda muka iso bai sauke Jakar nan ba Duk inda zashi da ita yake zuwa..!
Abba yayi yar Dariya yana Fadin”Kyalesa in ya gaji zai samu waje ya ijiyeta..!
Yafada yana bayyana Dariyansa Shima Daddy dariyan yayi kafin su Wuce suna cigaba da mganarsu Baffa Kabiru kuwa yana baya yana ta gwada Kiran Khamis bai samesa ba sai ya Turamai sako.
Bayan sun dawo Mazan da iyayen nasu Falon Daada suka yada Zango Imran dai wani Daki ya samu ya Shiga ya ijiye Jakarsa yayi wanka ya saka Jallabiya ya kwanta yana Hutawa achan Falo kuma Baba Asabe Tuwon Shinkafa Tayi da Miyar Zogale yan matan suka Tayata dasu Anty Safiya aikuwa kowa yaji Dadin Tuwon nan sosai Daada Farinciki ya cikata ganin Ahalinta Zaune Waje Daya sai dai bata ga Imran ba yasa ta juya tana kallon Sagir Tunda ta gansa shi ya saki Jikinsa Cikin su Sadam tunda damab ba Bare bane Tace”Sangiru ina Abokin ka Imrana Shi kadai ne yayi saura bangani ba..?
Sagir ya kalli Daada yana Fadin”Daada yana cikin Daki ya kwanta..!
Daada tace”To baka fadamai ya Fito yaci Abinci ba..!
Yusuf ya karbe mganar da cewa”Daada ki kyalesa in yana Bukata da kansa zaki ga ya fito..!
Daada Tayi Shuru Tana Tunani Inteesar dake gefe itama ta Damu Tun dazu bata gansa ba Har sako Ta Turamai yana ina..? Yace mata gashi goye a bayanta ya saka mata bakar mgana Daganan ta kyalesa sanin bazai Biyemata ba.
Kokarin Mikewa Daada Take Tana Fadin”Ai baza”a kyalesa ba Yusufa ni bari naje da kaina na Fito dashi..!
Ba yusuf kadai ba Kowa da kallo ya Bita na mamaki,Da Sauri Inteesar ta Mike ta isa kusa da Daada ta Riketa ta Mike Tsaye dakyau Inna Maimunace tace”Yauwa jeki Daada..Kila in ya ganki ko kila ya Fito ya zauna cikin yan”uwansa..!
Sadam yayi karaf yace”Mom Wlh Tsausayi yake bani Duk da haka Allah yayi sa ammh akwai ciwo fa rashin Shiga Mutane..!
Kafin Inna Maimuna tace wani Abu Inna Bintalo ta tabe baki Tana Fadin”Sai kace Wani yaro Daada da sai kin je kin Lallaso yaci abinci..? Ai yunwa bata da sabo da yajita Zaki ga ya Fito..!
Kamar Mami Asma”u na Jira ta kada kai Tana fadin”Umh ai nama kasa mgana Binta..Gardin Namiji ba yaro ba Ana damuwa dashi sai wani Lallabashi akeyi kamar shi kadai ne jika kwara Daya Tal..!
Tafada Cikin jin HUshinta wanda sai da Abba ya Dago yana kallonta ya Kada kai baice komai ba Hakama Daddy yana Jin Takaichin Yadda Mami take Shiga mganar da ba nata ba,kuma Yaya Kabiru na zaune bazai Tsawarta mata ba.
Daada bata ce komai ba ta kalli Sagir Tana Fadin”Sangiru wani Daki Kaga ya Shiga..?
Mikewa yayi yana Nuna mata Wani koridi Lokaci Daya yana Fadin”Dakin farko Daada..Muje na rakaki..!
Da sauri Inteesar tace”A”ah Zauna abunka Ya Sagir zan rakata da kaina..!
Jin haka yasa ya koma ya Zauna ita kuma Inteesar ta rike hannun Daada suka Nufi Koridon Kowa ya Bita da kallo Mami Asma”u harda Hararan kasan ido aranta tana Fadin Tsohuwar nan akwai rigima ba wanda ya kara mgana kowa ya cigaba da cin Abinncinsa.
Yana kwance Ringingine yana kallon Rufin Dakin ya saka Duka Hannuwansa Biyu yayi Filo dasu idanuwansa sun kankance kamar mai jin Barci Su Inteesar suka Shigo Dakin bayan sun kwankwasa Lokaci Daya da Sallama.
Bawai bai ji bane yaji Mamaki ne ya kamashi na waye zai zo ya Damesa bai kawo ma su bane duk a Tunaninsa Sagir ne yasa ya Juya baya kawai bai ko Dago kansa ba.
Daada ta Murmusa tana Fadin”Nine baka san gani Imrana..!
Jin muryan Daada yasa ya Dago kanta yana kallonta karaf suka Hada ido da Inteesar dake kallonsa Ido Cikin ido.
Lamgwabe kanta tayi kamar zatayimai kuka Saurin dauke kansa yayi Lokaci Daya yana Mike Zaune yana Fadin”Daada..!
Kafin Daada Tace wani abu Inteesar Tayi Saurin cewa”Daada ta damu baka ci komai ba Shine tazo da kanta..!
Kura mata ido yayi yana kallonta Daga sama Har kasa sanye take da Doguwar riga mai Ruwan kasa Kirar Armani mai Roba ta dan manne mata ajiki sai ta saka Vail din Rigar ta yane kanta dashi Zuciyarsa taji tana Bugawa yasa yayi Saurin kauda kansa Kafin ya Zuro fararan kafafuwansa kasa ya Sauko Daga kan gadon ya isa ga Daada yana Fadin”Daada ai ba sai kin taso ba..bana jin cin komai shiyasa..!
Daada tace”a”a kana jin yunwa sai dai in bazaka ci ba..Ko Tuwon ne baka so sai Maryama gatanan ta dafa maka wani abu ammh ai zama da yunwa bai da wani amfani Imrana..!
Imran yasa mezai ce Inteesar ya kallah ta Dagamai gira Hararanta yayi kafin yace”Daada..!
Bata bari yace wani abu ba tace”In baka son zama cikin mu sai ta kawo maka nan Dakin ba shikenan Damuwar ba..!
Kansa ya shafa kafin yace”Zan ci muje Saboda ke Daada..!
Taji dadin haka ta shafa kanshi Tana Fadin”Allah yayi maka albarka..!
Ya amsa da Ameen yana kallon Inteesar dake danne Dariyarta Hade rai yayi yana Fadin”Ke..Dariya kikemin ko..? Yarinyar nan kin rainani saboda banta Sauya miki kamanni bane shiyasa..!
Daada Tayi gaba bata jisu ba Inteesar tayi Raurau da ido kafin tace”Am sorry badakai nake yi ba..!
Bai tsaya ce mata wani abu ba ya Nuna mata Hanya da Hannunsa Dole ta wuce sum sum shi kuma yabiyo bayanta Duk Takunta yana Kallonta kamar kuma da Zuciyarsa take Tafiya Har zuwa Falon Daada.
Suna Fitowa kowa ya Dago yana kallonsa Shifa ya Tsani kallo wani Lokaci Fuskar nan ya Hade ba Fara”a su Abba kadai yace ma sannunku sai Inna Maimunatu Inna Bintalo baima Lura da ita ba yasa bai gaisheta ba Yana Shirin karisawa Kusa da Daada ya Zauna yaji Tana Fadin”Ni kuma Kashi nayi maka agado  da ko sannun bansamu ba..!
Shifa bai ma zata dashi take ba yazauna kusa Daada yana dan Wurga Idanuwansa,Yaji Abba yace”Imran ka gaida Goggonka Binta gatanan..!
Yafada yana nunata Sai Lokacin ya Dago yama kalleta Wani Kallo ta sakarmai shi kuma yayo mata kallon Kyahuwa..,? Irin to me ya Hadasu da zata mai wannan kallon Dakyar ya iya ce mata Sannu goggo..!
Ta Bude baki zatayi mgana Daddy ya Dakatar da ita da Fadin”Badai ya gaisheki ba..? Ku rika kama Girmamku Binta wadanan yaran fa Kamar ya”yanku suke..!.
Jim haka yasa tayi Shuru bata da tacewa Shiko Imran ko ajikinsa.
Daada tace munari ta sakamai Tuwon bai yi mgana ba ya Nannade Hannun Jallabiyan Jikinsa ya saka Hannun a Filet din Daada ya Debo Tuwon yakai Bakinsa da Bismillah kowa da mamaki yake kallonsa barin ma Abba da Ya Yusuf da Sagir da Munari da Inteesar sai dai bamai San sunayi ba Ya hade ransa ya cigaba da cin Tuwonsa Daada Ranta Fes tana kallonsa Tana Sakin Mirmishi Aranta Imran in ya Gutsiro Tuwon sai ya Tura gaban Daada kamar wata yarinya haka ya dinga mata sai dai ta Dauka tace cikin Taruwar Hawaye tace”Allah yayi maka albarka Allah ya jikan Zuwaira..Kullum kukanta Daada Yaushe Imu zai sauyane..? Yayi kaza yayi kaza Baya son zama cikin yan”uwa yau data na Raye data zo ta ga Imranu yana cin Abinci kwano Daya Dani yana Gutsiromin Tuwo saboda yasan na Tsufa baya so na Wahala..,!
Da karfi Tayi mganan dayasa kowa yajita sai aka koma ana kallonsu Cike da mamaki Abba Farinciki ya cikasa shi da Ya Yusuf Imran kuma baima Kalli kowa ba bai wani ci mai yawa ba ya Zare Hannunsa ya Mike Daada ta Kallesa Tana fadin”Har ka koshi kenan..?
Kai ya gyada mata bai yi mgana ba ya Wuce zuwa Kitchen ya wanke hannu ya Dauko Ruwa Gora guda Daya yazo ya wuce ya koma Daki abunsa batare Dayace ma Kowa komai ba Daada sai Mirmishi take ita Kadai Mami Asma”u na Binta da Harara kasa kasa itafa bata Kaunar taga Daada na nuna ma wani Jika so da kulawa in ba ya”yanta ba akomai tafi so su kasance sune kan gaba da kowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button