
“Kana ina ne..? Plz ka dawo cikin gida Dare yayi..’!!
Tunda ta Turamai take jiran amsarsa ammh Wajen Fin Minti goma bata gani ba,Sai ta kara shiga damuwa Kiransa tayi Har sau uku bai Dauka ba Hankalinta taji ya kara tashi ta Mike Tsaye tana Tunanin ta Fita ne tagani ko kuwa A”a..?
Imran yana Cikin kukan Zuccinsa dana Sarari yaji Shigowar sako acikin Wayarsa kamar ya Share sai yaji ya kasa ya Dago kansa bayan ya Zaro wayar daga aljihun wandonsa ya Duba sai yaci karo da Sakon Inteesar wani Dum yaji acikin Zuciyar sa Ransa ya kara kuna yana Tunanin me Zata fadamai ita datake kuka Saboda Mganar Daddy..? Karamin Tsaki yaja ya goge ma sakon nata wanda ta Turo ammh ya kasa goge duka Sakonninta Haka kurum yaji bazai iya ba..
Wayar na Hannunsa take ta kira yaki Dauka sai da ta gaji da kira ta Hakura kana yaji Kamar bai kyauta ba ita Kadai ta damu dashi da Halin dayake ciki Shiyasa ya Turamata sako.
“Ki daina Damuna plz ki kyaleni..’
Haka ya Rubuta mata tana Daga Tsayen Taji shigowar sakonsa Hannunta Har rawa yake wajen ta Duba Tana ganin Abunda yace taji Hankalinta ya kara tashi a Fili ta Furta”Yana cikin damuwa Ransa ya baci.Kuma shi kadai a waje..!
Tafada Wasu Zafafan Hawaye na Biyo kuncinta batasan meke damunta Taaudsyin Imran da wani abu acikin Kirjinta da batasan ko na miye ba suka Rinjayeta ta Fito Daga Dakin Tana Sanda,Falo ba kowa shiru Duk an kashe Haske,dakuna ko”ina akulle Su Abba Tuni sun gama Tattaunawa Da Daada ta Sallamesu sun nemi makwanci Ba motsin kowa,Ahankali ta Fara takawa bayan ta Dan Taba Wayarta Haske ya kawo saboda ta rika ganin gabanta Har ta samu nasaran Ficewa Daga Falon Tunda kofar a Bude take ba”a Rufeta ba.
Tana Fitowa Haraban gidan ta Fara waige waige Karaf kuwa ta Hangosa kan Mota ya Cusa kansa Tsakanin kafafunsa Allah sarki kalleshi shi kadai Haka ta fadi acikin Ranta tanajin wani Feeling dake taso mata Daga kasan ranta kan Imran da har yau ta kasa Tantance Menene hakan..?
Jikinta a sanyaye ta Fara takawa zuwa Gabansa bai ji tahowarta ba sai dai mganarta kawai yaji.
“Ya imran..!
Tafada Cikin karyewan muryan Data Shake a kuka da Sauri ya Dago shima Rinannun idanuwansa ya Sauke Cikin nata gabadaya sai da Jikinsu ya amsa Hade da Bugawar Zuciyarsu,mamakin ganinta ya kamashi Saurin Dirowa yayi Daga saman Mota yana Fadin”Ke meya Fito dake yanzu da Tsohon daran nan..?
Yafada Lokaci daya yana Duba Agogon Fatan dake hannunsa yaga 1 saura na Dare ido ya sakamata ganin Ta faramai Hawaye Cikin Bacin ran data karaman ganin kukan ta ya Daga Murya yana Fadin”Wayace ki Fito..? Nace wayace ki fito..?..
Yafada Cikin Tsawan data Fashemai da kuka Tana fadin”Wajen..ka..nazo..!
Tafada Cikin muryan kuka Zuciyarsa ZAfi take da kukanta shiyasa Ransa ke kara baci Cikin Tsawan ya kara cemata”Ban ce ki kyaleni ba..Ni bana Bukatar kowa I don”t Need Anybody..Ki wuce ki koma Cikin Gida Tun kafin Raina ya baci na saka miki Hannu anan Wajen..!
Ya karishe fada yana so ya Danne Abunda yake ji yana Tasomai Daga kasan Ransa.
Ita kuwa kuka kawai take Ta saka Hannunta taja Hijabinta ta Toshe Bakinta ganin in ta Cigaba da Tsayiwa yana jin kukanta Zuciyarsa Zata Tsawartse saboda Bacin rai yasa ya nuna mata Hanya yana Fadin”Oya your way here..Kije chan ki cigaba da kukan naki ba sai kin zo kin fadamin ba..Nima bazan ce a auran mik…!
Bai gama Mgana ba yajita kikam ta Fadomai jikinsa da wani irin karfi Ta Rumgumesa kamkam kamar wani zai kwace mata shi Lokaci Daya tana kara Fashemai da kuka.
Jinta Cikin jikinsa da yadda ta kamkamesa sai ya sauya komai yaji sa Cikin yanayin dayake shiga duk sanda Jikinsu ya Hadu waje Daya kukanta ya sakamai Rauni jin Dumin jikinta ya sakashi jin wani yar acikin jikinsa Tuni Zuciyarsa ta Bude ya Farajinsa kamar bashi ba,Zuciyarsa ce ta Rinjayesa yajisa ya saka Duka Hannayensa ya Rumgumeta kamkam shima atare suka ja Numfashi Cikin Bugawar Zuciyarsu alokaci Daya.
Shima indaizai Fitar da Hawayen Dayaji Dadi ya fita tsawo shiyasa kanta ya tsaya saman Faffadan kirjinsa Shi kuma ya nannadeta da Hannanyensa a saman kanta ya aza kansa ya sauke Numfashi.
Cikin muryan kuka Inteesar ke Fadin”Kada ka kara fadin haka ya Imu..!Ni bazan taba gudunka ba Har Abada..!
Kalamanta Daki daki ke shiga Cikin kunnuwansa,Yana Rike da ita cikin Wata irin Raunanniyar murya yace”A”a..Bana so naga ina sakaki kuka..Kiyi Hakuri Daady bazai aura Miki Dan iska kuma dan Shaye shaye ba..!
Yafada yana kara jinta ya Riketa kamar itace Salama acikin Rayuwarsa,Rikon yayi mata Zafin Dayasa sai da ta saki yar kara sai kuma Lolacin ya Farga da abunda ya aikata da Sauri ya Saketa ya mtsa baya yana Kokarin Daidaita kansa
Inteesar kallonsa take Cikin wani yanayin Da takasa gane ma kanta ta Bude baki Zatayi mgana kawai ya Ja Hannunta Lokaci Daya suka Fara Tafiya zuwa Cikin Falon Daada.
Ta kara yunkurin mgana ya waigo yana jan Bakinsa”Shiiii…!
Alamun tayi Shuru Dole ta maida bakinta ta kulle sai dai idanuwanta suna kan Hannunwansu da suke Hade Waje Daya tana jin wani irin Babban al”amari acikin zuciyarta Idanuwanta ta maida kansa yanayin Tafiyarsa kadai Zaka Fahimci maza na inda suke..
Tunaninta ya katse ne sanda suka Shigo Falon,sun shigo kenan Sajida Data Fito Daga Kitchen ki shi ya Fito da ita Daukan Ruwa kuma ta Kunna Hasken Falon idanuwanta Kur akan Hannun Inteesar dake cikin na Imran Cikin Faduwar gaba take Binsu da kallo.
Imran kallo Daya yayi mata bai kara ba Ita kuma Inteesar gabanta ne ya Fadi,tuna yanayin data gansu kada ta Zargesu da aikata wani abu.
Ta bude baki zatayi mgana kenan ya Saki Hannunta yana Fadin”Ki kwanta..And Stop craying ok..!
Yafada yana Tsareta da Idanuwansa masu cike da bacin rai.
Tana kallon Sajida dake kallonsu tama kasa gaba ballatana Baya bakinta ya kasa Motsi ganin haka yasa kawai ya Juya ya nufi Koridon da zai sadashi da Dakin da ya ssuka cikin Tafiyarsa ta Sassarfa da Jarumta Daga Intee Har Sajida ba wacce ya kara kallah,Bakinciki ne fal acikin Ransa,Yana jin wannan yarinyar ayadda yake jin Zuciyarsa Zai iya Kasheta bai Huce ba baima san kallonta Shiyasa yayi wucewarsa kada ma ya kara ma kansa Bacin rai.
Sagir kadai ya iske a Dakin Yayi barci Ashe sama sama ne karan Bude Kofa ya Farkar dashi da mamaki yake kallon Imran wanda ko kallonsa bai yi ba ya Tura Kofar Tiolet ya shige ya Bango kofa.
Sagir ya Sauke Numfashi kafin ya koma ya kwanta bai jima a Tiolet din ba ya Fito Dagashi sai Gajeron wando Jikinsa na Digan Ruwa Daga gani Wamka yayi,ko mai bai shafa ba ya Watsa kayan daya Cire nan kan gadon yaja Filo ya yada kan Cafet ya kwanta Ringine Ruwan jikinsa na Diga a inda yake bai Damu ba saima Hannayensa Daya goya saman Kirjinsa yana Sauke Numfashi Sama sama.
Sagir Harda Tashi Zaune yana Lekensa yana kallonsa yayi kamar bai gansa ba sai ma ya juya bayansa Kawai yana kara Hade ransa kamar bai taba Dariya ba.
Afalo kuwa Inteesar ce ta fara wucewa Dakinsu batare data kara Kalln gefen da Sajida take Tsaye ba,Sai da ta shige ta Rufo kofa kana ta Sauke ajiyar Zuciya tana goge Busasun Hawayen dake idanuwanta,Jikinta yayi wani irin sanyi haka ta karisa gefen Hafsah ta koma kwanta Tana jin wani yanayi a tare da ita Runtse ido tayi Ba domin tanajin Barci ba sai Domin Tana Fatan ya Dauketa,Hankalinta ya kwanta Tunda ta gansa kuma ya Dawo Cikin Gida Sai dai Hankalinta ya tashi da kalamansa,
Shi a zatonsa tana kuka ne Saboda Abunda Daddy yace..?Baisan tana kuka bame saboda Tsausayinsa da wani Lamarin data kasa gane Wani yanayi ne? Menene yasa Kirjinta ke Nauyi kan Imran..? Meyasa bata son bacin ransa? Zuciyarta na Zafi in ta gansa Cikin damuwa Bata san Dalili ba sai dai ta Danganta haka da Dan”uwanta ne sannan akwai sanin juna Tsakaninsu tun kafin su gane su din Ahali Dayane.
Sajida kuwa Har Inteesar ta Shige ta barta Zuciyarta bata gama Dokawa ba,Idanuwanta na hango mata gilmawar magijin Hannaun Inteesar Cikin na Imran dinta Zuciyarta taji tana Dokawa da karfi datayi Tunanin kodai soyayya suke yi..? Kai ina badai so ba sai dai in wani abun to kodai kodai..!.da sauri ta yanke wannan Tunanin domin ya kusa sakata ganin Jiri to ammh in ba ko Daya meye sukeyi Cikin Dare ko wa yayi barci Hannayensu Cikin na juna..?
Bata damai bata wannan amsar Shiyasa cikin Sanyi jiki ta karisa Cikin Dakin Data Fito,Dauke da goran ruwan Data Dauko Daga Kitchen Mami Tayi barci duk da Kila bataso ma Tayi barcin ba sai dai ai shi ba”acin bashinsa Umma ma kan Darduman data gama sallah Tayi barcinta Ita da Mami ne suka Hau kan gadon….
Lallabawa tayi ta Haye gado ta kwanta Tana kokarin Daidaita Tunaninta kada Zargi ya shiga Cikin Zuciyarta ya Dagulamata komai..