GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari Daddy bai samu Biyowa ta nan Kano ba,Saboda zai yi baya Ya yusuf da Abba da Imran suka Samesa a kaduna,Su Munari suna ta Barci koda suka tashi Tuni sun kusa isa kaduna Domin 6:30am suka Fita Suna Dawowa Sallar asuba Tunda Tafiyan Motace zasuyi Dukkansu sun Tsani hawa jirgi Tun Faruwar Lamarin Daya Faru.
Da kwatace da komai sai ga Abba agidan Daddy farinciki kamar me Wajen Daddy ya kama Abba da su Yusuf ya Rumgume Umma kuma Tana ta ina ta saka dasu,Basheer ma yazo Dayake Har dashi Za”ayi Tafiya za”a Tafiyu iya Tafiya shiyasa Dole su nemi Wanda zai taimaka ma Yusuf da Driving Tunda Imu dai ya Dade bai Taka Mota ba.
Sai da suka karya kana suka Mika Hanya,Wajen 10am na Safe Umma ta Bisu da Allah ya Kiyaye Hanya Yusuf ke Tuki Imram na Gidan gaba Basheer da Abba da Daddy na Gidan Baya sai da suka Tsaya suka cika Tankinsu da mai suka Dau Hanya Da guzurin Abinci su da kayan Snak a bayan Booth Wanda Umma tayi musu tunda Tafiyace ba kadan ba kila su da isa sai Cikin Dare ko da asuban Gobe.

Shakira
3/22/22, 23:15 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?11

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Basu isa cikin garin Lagos ba sai Misalin 3:30am na Dare suka isa,Saboda Shigar Dare sukayi ga Gajiya yasa suka kama Hotel suka kwana suka warware gajiya sai da garin Allah ya waye bayan sun yi wanka sun yi breakfast kana suka Dauko Hanya zuwa Ainihin gidan su Imran wanda suka barsa Shekaru uku da wani abu.
Abba da Yusuf Rauninsu yafi bayyana ammh banda Imran wanda ba wanda ya isa ya bayyana wani Hali yake ciki.
Duk da sauye sauye ya karu a Birnin na Ikko basu manta kayattaciyar anguwan masu hannu da shunin da sukayi Rayuwa ba wato Victory inland ba.
Gidansu na nan yadda suka Barshi Katon get garkame da katon kwado Sai dai saboda Dadewa get din duk yayi kura yana sun Rufe wajen alamun dai ma mallaka Gidan sun Dade basa rayuwa acikinsa.
Ba wanda ma zai iya Tuna ina key din kwadon yake Lokacin da suka Rufe gidan suka Tafi suna cikin yanayin da ba baza su iya su iya gane komai ba.
Sai da Yusuf ya shiga Cikin gari ya samo mai yanke kwado aka zo aka yanke shi aka Bude gidan suka Shiga Ciki.
Allh Sarki Rayuwa Duk mai Imani Dole ya koka ma wannan Ahalin Gabadaya Haraban gidan ya Cika da Kura kyakyawan Marbels din Dake Shinfide a Haraban gidan ya cika da Ciyayi duk sun bushe Flowers duk sun bushe sun mutu murus Yana duk ya Lullube ko”ina ga Motocin su na Zamani guda Hudu reras,Na Abba dana Imran dana Nura sai na Yusuf gabadaya sun Lalace sun yi kasa Saboda ajiya Tayoyinsu sun Faffashe ba kyan gani sun yi kura Har sun gaji sun Fara Kokewa saboda Zama Waje Daya,Domin kana ganinsu Zaka Fara Tunanin da wahala su tashi Har su iya Moruwa koma sun Morin sai sun Dade a gareji suna cin uban kudi.
Kuka Abba keyi Reras sanda suka Shiga Ainihin Falon gidan ba Kurar Daya bata gidan bane Damuwar ba yana Tuna each and Single Moment da suka gudanar acikin wannan kayattacen Gidan shi da iyalansa da Matarsa sai gashi komai ya Zama Tarihi.
Abubuwa Dadama agidan nan sun Lalace kama Daga kayan kallo Frigde da Sauransu kujeru ne sai gadaje basu yi komai ba ammh duk wani kayan Wuta ya gama aiki gidan yayi kura yana Duk ya Rufe ko”ina sai da Basheer da Yusuf suka rika saka Sanda suna Cire inda Zasu Taka.
Wasu Kofofin Dakunan ma Sun ki Budewa sun kame sai an kira masu Cire Kofa Imran ya shiga Dakinsa yana Kallon kowani kusuwar Ya Duba Cikin Wardrope dinsa da Gabadaya kura suka mamaye ka’ina kyawawan Suit dinsa na kamfanoni Dabam Dabam da ke shake Cikin Wardrope din Duk sun gama sauya kala Kama Daga Takalmansa na Kowani kamfani masu Tsada da yarari duk sun sauya kamanni da Dadewa da kura komai nashi acikin Perfect ne Lokacin yana amsa sunansa Banker Imran Abubakar malami ba yanzu da komai ya sauya ba shi kanshi yaji Tahowar kwalla yayi saurin kauda kai bai bari Hawayen ya Zubo ba yasa Hannu ya Dauke kwallarsa.
Haka bangaransu Yusuf da Abba Suna Bin ko”ina da kallo suna Hawaye Daddy da Basheer suna ta basu baki,Basu iya ko zama ba saboda ba Wajen zama suna dai Tsaye suna Zagaya Ko”ina na Gidan suna kallo Suna Tunawa da Rayuwar baya.
Daddy ya fara kawo shawaran bazasu Tafi su bar gidan nan hakan nan ba Zai kara Lalacewa Tunda ba su da Sha”waar kara Rayuwa aciki sai dashi Abba yace bazai Taba saida wannan Gidan ba Har Abada Ko ya Mutu ga Yusuf ga Imran ga Munari gidane mai Dimbin Tarihi zai barsa Kila ko watan Watarana Su rika zuwa Hutu ko kuma Yanayin Rayuwa zai iya maido da Daya Daga Cikin su Imran nan garin Tunda suna da Muhallin Abubuwan bazasu yi wahala ba Kowa yayi na”am da mganar Abba ammh sai aka Fara Tunanin yadda za”ayi Daddy yace Dole kafin su koma a samu wadanda zasu Zauna agidan nan da sunan gadi su kuma Rika gyarashi suna kula Dashi Domin barinsa ahaka shine Jidali.
Suna cikin Hakane sukaji Sallama Daga Kofar Falon gabadayansu sun ji mamaki Abba ne da Daddy suka Fita Haraban Gidan Ikon Allah Abba kawai ke Fadi na ganin Abokinsa Amininsa Dr.Isa Ali Argungun Abokin aikinsa ne shima Lecture ne a nan Lagos Universty,Sai dai shi yana Shashen Kimiya da Fasaha ne Wato Computer Science sannan kuma Makota suke da juna Domin gidansa da Gidansu Gida Dayane Tsakani sun yi Zaman Amana sosai da Amintaka Duk garin Lagos Abba bai da aboki kamar Dr Ali argungu Matarsa Hajiya Barira Kawar Anni ce Lokacin tana Raye,Sannan karamin Dansa Ibrahim Khalil,ma”ikacin Banki ne shima Tun alokacin da shi kadai Imran ke gaisawa Sama sama abota dai wacce bata Zama Takura ba yayinda shi Khalil ke aiki da Firstbank nan Reshen Jahar Lagos shi kuma Imran yana aiki da GT bank suna Haduwa Lokaci bayan Lokaci in Bankunansu ta Tura su wata Seminar Tunda dukkansu Zakwakurai ne abangaran da suka karanta ma”aikatan su na matukar ji dasu,yanzu ma Tare da Khalil suka shigo Abba suka Rumgume juna da Dr.Ali Argungun suna masu Hawayen Farincikin ganin juna jin shuru ne yasa su Yusuf suma suka Fito Haraban gidan nan suma suka ga Abun mamaki nan fa aka Shiga gaisawa Cikin Tambayan juna bayan Saduwa Dr.Ali argungun yaja su zuwa Gidansa Tunda nan yayi kura ba wajen Zama basu yi gaddama ba Sanin sa ai shakiki ne ga Abba ko su Daddy sun san Tunda Lokacin Rasuwar su Anni Har Dukku ya Taka Daga baya daya samu Labari shi da Iyalansa.
Alokacin da Abun ya Faru bai sani ba Har Suka zo suka tafi da Abba chan Dukku sai daga baya yaji Labari kuma garin Dukku ba boyayye bane sannan Gidan Marigayi Alkali Dukku ma haka da Tambaya da komai suka isa Dukku Lokacin Abba yana Halin Rashin Lafiya baya gane komai sai sambatu Dr.Ali argungu ya Dawo da Tsausayin Abokinsa matuka acikin Ransa kuma yasha zuwa Dubasa Har Dukku kusan Sau Uku Daga baya da suka Dawo Lagos kuma basu Dade ba aka nemesu aka Rasa ya Zata sun kara komawa Dukku ne sai da yaji Shiru ba waya ba komai Achan Jami”a ma ba wani Labari yasa yaje Dukku da kansa nan ya iske Labari mara Dadi an nemi Dr.Abubakar malami ko sama ko kasa Shi da Sauran yaransa ba’a gansu ba Lokacin ya gana Daada Tana ta kuka Tana Bayyanamai Damuwarta ya Dawo Lagos shima da Damuwar Abun kuma shima yayi ta Bincikensa ba wani Labari sai dai ba Cire rai ba
Suna da Lambar juna shi da Daddy yana Kiransa Lokaci bayan Lokaci yaji ko an ji Labarin Malami sai dai Shuru ne,Shima Daddy yakan kirasa yaji ko da wani Labari Lokacin da Abba ya Dawo Wasu abubuwan sun Doke wasu Shiyasa bai samu Damar Sanar da Abba komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button