GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Kanta yake Shafawa yana Fadin”Waneshi ya Dakarmin Auta guda..? Sha kurumin ki ni Dakaina zan kai ki Har kano gaban Innan naki na Bada Amanarki kana naja ma D’an wajen nata kunni komai kikayi kada ya Dakeki ya Lallabaki ne Saboda ke Auta ce..”Murna Ta Farayi ta Rumgumeshi Tana Fadin”Ina Kaunarka Daddyna.”Kanta yake Shafawa yana Fadin”Nima haka Auta Daga ke ba Kari Intin Babanta..”Umma Dake Goge ma Abidin Baki Daya bata da Madara tace”Uhm..Bashir tashi ka Tafi gidanka kada ka Biyema wannan Shirmen na Alhaji da yarsa..Kabar Hauwa ita kadai gashi kuma kasan Halin Datake Ciki..”Yana Kokarin mikewa yace”To Umma…”
Yafada yana Mika mata Abida Data Fara Barci ta karbeta Lokaci Daya yana Fadin”Daddy zan tafi..Sai Allah ya kaimu.!
Daddy yace”Shikenan Bashir.Ya ake  Ciki kan mganar Tafiyar Inti din..? Kunyi mgana da yaron Wajen Innan naku..?
Bashir yace”Eh Daddy munyi mgana..Lokaci fa ya tafi Tuni sun Fara Lacture ya kamata Cikin Satin nan Tatafi tayi Registration Sati na Sama ta Fara karatu gaskiya..”
Daddy ya Jinjina kai yana Fadin”Shikenan Zuwa Jibi sai muje na kaita..Insha Allahu kafin Lokacin Komai ya kamallah ko Autana..?
Inti ta gyada kai Tana Fadin”Daddy ai kagama Siyan min komai fa Abu Daya ya Rage f..? Yana kallonta yace”Menene shi Autana..? Cikin Daga kai tace”Sabuwar waya Daddy…Taya zan je da Wannan Tsohuwar wayar Jami”a ai sai su raina maka ni..”Ta karishe Fada tana wani Hura Hanci Umma ta saki Baki Tana kallonta kafin Tayi mgana Daddy yace”Hakane kuma fa..To kada ki Damu zuwa gobe Bashir zai je ya Dubo miki wata iri kike so.? Da sauri tace”Samsung Daddy..Ina sonta sosai..”Daddy yace”Shikenan Angama Intin Daddynta..!
Dariya ta saki mai kayatarwa Tana Fadin”Nagode Daddyna..!
Umma dake zaune tace”Ka biye mata kuma..? Wayata fa ko wata Biyar Batayi ba Daka Siya mata bafa..Haba Alhaji bai kamata kana Biye ma yarinyar nan ba..Yakamata ka Rika Duba Rayuwa in yau mune gobe bamu bane Haka koda yaushe Daada na Fadamaka in mukaje Gaishesu taga Inti na wannan Tabaran ko bakomai watarana Gidan wani Zataje..”Yana jinta bai yi mgana ba Illah kallon Inti Dayayi wacce ta batarai yace”Autana jeki ki kwanta kinji ko..? Sai da Safe..”Batayi Gaddama ba ta Mike Tana Fadin”Gud Night Daddy..Umma sai da Safe Ya Bashi ka gaida Anty Hauwa..”Dukkansu suka amsa mata Umma tace”Zo ki Dauki Abida wajen ki zasu kwana..’Baki ta Tura tana Fadin”Wajena kuma Umma..? Tab ni wlh A”a Shegun kukane dasu..Hanani barci fa suke Cikin Dare..”Ta fada kamar Zatayi kuka Umma tace”Allah..? Naga yadda zaki kare in kika Haifi naki..!
Inti na Dariya tace”Daddy na zai Daukan min mai Reno..”da Filon Kujera Umma taRakata dashi Inti ta kwashi Gudu Zuwa Dakinta Tana Dariya Bashir ma Dariyan yake Shi da Daddy,sallama yayi musu ya Biya Kicthen ya Gaida Talatu daya Tarar tana wanke wanke Kafin yayi mgana ma Ta mikomai kulan Umma ta gayamata ya Fice Su Umma ya karama Sallama suka Rakashi da Allah ya kiyaye ya Fice Zuwa Haraban gidan ya Shiga Motar sa Kiran 4matic ya Zuba Hon megadi ya Bude mai get ya Fice Daga Gidan ya Dauki Titin anguwan Rimi inda gidansa yake.

Sai da sukaji Tashin Motarsa kana Daddy ya juyo yana kallon Umma yana Fadin”Meyasa koda yaushe kike maimaita mgana Dayane Salaha..? So nawa zan gayamiki ki Daina Ganin abubuwan da Inti ke yi a wani abu kar ki manta fa yarinya ce fa In ta girma Zaki ga Duk ta Daina wadanan abubuwan kuma kada Ki manta Sai da Bashir ya Shekara Goma sha Biyu aduniya muka Sameta alokacin da muka Fidda rai da samunta ita kadai ce Mace awajenmu menene Laifin in mun bata kulawa da gata..? Ai hakan bai Hanata zama mai Tarbiya da ilimi ba ina alfahari da ita da kananun Shekarunta ta Sauke qur’ani yanzu kan Haddatanta take,Kuma kina gani Da kuruciyata gashi Zata shiga Jami”a Alhamdulillah bata Taba Jawo mana mgana ba Salaha ni banga abun Damuwa ba..”
Ya karishe Fada yana kure ta da ido,Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin”Uhm..Alhaji kenan wai kana Bani mamaki in kace Inti yarinyace..? Wacce ta Haura Shekara ashirin ce yarinya Alhaji..?
Cikin Halin ko inkula yace mata”To in ba yarinya bace Babba ce..? Shekara ashirib Duka Duka nawa take..? Don Allah ki Daina wannan mganar..In bamu kula da yayanmu ba..Ai samun mu ya zama na banza sai mu Daina Fita Neman Salaha..!
Sanin bazai Taba Fahimtarta ba yasa ta bar mganar ta Mike Dauke da Abida Tana Fadin”Bari na kai Abida Daki tayi Barci..”Daddy yace”Ga Abidin ma yayi barci ajikina..”Batayi mgana ba ta wuce Ciki Dakinta ta kai Abida ta kwantar kan gadonta kana ta Dawo ta Dauki Abeedin Shi ma takaishi ta kwantar ta Rufa musu bargo ta Rage musu Sanyin Ac ta kuma Rage Hasken Dakin kana ta Rufo musu kofa ta Fito Ta samu Daddy zaune in da Ta barshi ya maida Hankalinsa kan Talabijin yana kallon Labarai Kitchen ta wuce ta samu Talatu na Goge goge Sannu da aiki Tayi mata kai tsaye Fulas din Dake Kan Cabinet din kitchen din ta Nufa ta Dauki karamin mug ta Tsiyayo Ruwan lipton din Dayaji kayan Itatuwa da Ganyen Na”a Na”a ta Fice dashi Zuwa Falo Tana Zuwa Taja Center Table din Dake Tsakiyar falon ta ijiye Tana Fadin”Alhaji ga Ruwan Lipton din nan..!
Dago kansa yayi yana Fadin”Yauwa Nagode..’Daukowa tayi ta mikamai ya karba ya Fara Kurba sau Biyu yayi ya Dauko yana kallonta yace”Wata anguwa Su Yaya Aminan suka koma ne Bayan Tashin su Daga zoo road..?
Umma tace”Gadan kaya suka koma..Gidan Marigayi din da Sagir din yagada Ta koma Ciki suna zaune..”Daddy ya gyada kai yana Kurban Tea din yace”Sai nake ganin kamar Nauyi zamu kara mata Salaha..!
Umma ta kalleshi a kaikace tace”Wani irin Nauyi kuma..? Sai da ya kara Kurban Tea din yana Fadin”Kai mata Inti da zamu yi ta zauna wajenta Tayi karatu..Ga Wahalan Rayuwa ga Kuma Rigiman Diyar taki..! Umma Tayi Mirmishi Tana Fadin”Wlh ko Daya Alhaji..Bakaji da na kirata na gayamata Intisar ta samu addmission anan BUK ba..Kafin na Furta mata ina son Inti ta zauna wajenta sai dai ta rika zuwa Tana Dawo in anyi Hutu sai Tazo mana nan tayi mana Hutu ita ta Fara Cemin ammh wajena Zata zauna ki..? Kasanta da son Diya mace kuma Allah bai Bata ba Danta kenan kwara Daya Sagir..Bayan mutuwar Mahaifinsa kuma tace bata Sha’awar kara aure ba yadda su Baba Bala basu yi da ita ba tace baxata kara aure ba Shiyasa taki Dawowa ta Fara sana”arta achan tana kula da Danta har gashi yana Karatu shima kuma yana Sana”ar dole suka sakamata ido.!.
Daddy ya jinjina kai alamun gamsuwa yana Fadin”Hakan ma yayi. tunda wani Lokacin sai kiga karayin auran ma wani abu ne Dabam..Badai shi yaron Dangin Mahaifin nashi na waiwayansa ba..?
Umma tace”Eh suna iya bakin kokarinsu..Ai kanin Babbansa Daya Wani Manu..Ko Yaya Aminan wh suna mata kokari..Ita Dayake bamai jira bace macece mai neman na kanta Ko Daga nan gida zaka ga ba kasafai take kira Tanemi wani abu ba..”Daddy yace”Allah sarki..Rabona da kano Tun Rasuwar Mahaifin yaron nata..”Umma tace”Sai gashi Dalilin yarka zai kai ka ko.? Yana Dariya yace”Zaki fara ko..! Kin san bana samun Zama ne..Allah ma ya Taimakeni Bashir yanzu yana kula da komai..”Umma tace”Gaskiya fa..!
Daddy ya mika mata Mug din yana Fadin”Naji Dadi da Inti Tana da inda Zata zauna..Dama bana son zaman Hostel sam kinsanta Tana da Tsiwa kuma bata saba Zama cikin mutane ba..Uwa uba da kuma D’an wajen nata ko bakomai zai rika Taimakata awasu abubuwan Tunda Bashir ma yace shima nan yake Karatun nashi..”Umma tace”Eh Haka Yayan tacemin..Ya kusa gamawa tace shi..”Daddy ya Mike yana Mika yace”Shikenan dai..Zuwa gobe ki kamalla mata komai jibi zamu tafi insha Allahu..”Umma ta mike Itama Tana Fadin”Allah ya kaimu..Miya ce zan mata..Dambun namanta na Soya mata..Sai su Snaks Datace Tana so nayi ma kawata Mgana Gobe za”a kawo..”Hanyar Dakinsa ya Nufa yana Fadin”Ina jiranki aciki..”Hanyar Kitchen ta Nufa Dauke da Mug din Tana Fadin”Gani nan Tafe..Baban Inteesar..”Yana jinta yayi Mirmishi ya Shige Cikin Bedroom din Dayake mallakinsa,Umma Data fito Daga kitchen din Kashe Tibin Tayi Kafin ta Rufamasa Baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button