
Shakira
3/22/22, 23:15 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?12
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
Da garin Allah ya waye saboda ita da Safe yazo ya Tsaya a Haraban gidan Saboda yasan suna da makaranta yau da safe so yake ya ganta kafin ya tafi.
Sai dai duk yadda yaso Inteesar da suka Fito ya yusuf zai kai su kafin ya wuce wajen aiki bata yarda ta Hada ido dashi ba,Duk yadda yayi kokarin haka yaga Idanuwanta sun tasa alamun Tasha kuka jiya da Dadaddre..
Munari ce kadai ta gaisheshi Inteesar kuwa Mota ta shige Fuskarta ba Fara”a ko kadan ta maida ma kanta wani gefe Ran Imu ya sosu yaji ba Dadi yau shine Intee bata son ganin Fuskarsa abun is so painfull acikin Ransa.
Ya yusuf ne Daya fito ya gansa Tsaye Jikin Mashin dinsa ya Hade Hannuwansa Saman Kirjinsa kamar ko yaushe Kallonsa yayi yana Fadin”Yaushe zaka wuce ne..?
Kai Tsaye Imran yace”Yanzu..!
Yafada Kan Sa tsaye Kuma Duka Kallonsa naga Inteesar wacce ta maida kanta gefe batama yarda ta Dago ba ballatana su hada ido ba duk da ta Lura ita yake kallo kuma jikinta ya bata Wadandan Kafaffun Idanuwansa suna kanta ne.
Ya yusuf yayi sakake yana kallonsa Kafin yace”Yanzu..?kuma kake Tsaye anan ba wani Shirin Tafiya..?
Imran gajiya ma yayi da mganar Yusuf ya barsa yaji da abunda ke gabansa mana bai ce mai komai ba ya Taka zuwa Cikin Falon ko waige Yusuf ya Bisa da kallo kafin ya Tabe bakinsa sai alokacin Inteesar tabi bayansa da kallo Cikin Samun Sukuni da Salamar Dake Tattare da ganinsa din Munari na Gefenta Tana Lura da Komai acikin Ranta tace Allah Sarki Soyayyah..
Yusuf shima Shigowa Motar yayi ya Kunnata yayi Riverse suka Fice Daga Haraban gidan.
Suna Tafiya ba Dadewa Imran ya Fito Cikin Shirin Tafiya yayi shigar Riga da Wando Rigar Fara ce mai Dogon Hannu Tana da Layin Baki ajikinta Sai Wandon Jikinsa baki ya kamasa daga kasa Kadan kafarsa sanye Cikin Bakin Takalmi Sawu Ciki na Fatar Damisa,Ahannunsa na Hagu sanye da bakin agogon Fata na Kamfanin Rado Kan nashi yasha gyara,Bayansa ya Rataye da Jakarsa baka ta baya kamar ta yan makaranta Bawani Kure adaka yayi ba ammh ko sau Daya ka kallesa sai ka kara kallonsa Cikar Zatinsa baiwa ce Daga Allah kwarjinsa da Kyansa kuma Hallitace ta Ubangiji Duk Takamar mace da Kudinta da Iliminta in Imran ya Tsaya a gabanta ya Kalleta ido Cikin ido sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka Maza kuma yan”uwansa Dole in suka kallesa sai sun kara kallansa sun kuma Tabbatar ma kansu Babban Goro sai magogin karfe.
Ko afitowar da yayi Abba Dake kan Dining yana karyawa Sai da ya Dago ya kallesa acikin ransa yana Kirari ga Allah mai gagara Misali da ya Hallici Imran a yadda yake,Safiya ma Dake Zaune afalo bayan ta Rako Yusuf ne ta Jabe anan tana Hutawa ta kasa karisawa Shashenta Cikinta har ya Fito Domin ya Shiga watansa na Biyar,Itama Dake Zaune sai da ta kallesa ta kuma Jinjina Kwarjinsa Ya gaisheta ta amsa mai Cikin Sakin Fuska yana gaisheta Wani Lokacin In suka Hadu Gab da gab ammh fa baya Binta ya gaisheta in sun hadu shima din yana Cikin Mood mai Dadi in Ransa na bace kuwa baya bi ma ta kan kowa.
Wajen Abba ya karisa ya dan Rankwafa ya gaisheshi Abba ya amsa Cikin Sakin Fuska yana Fadin’Bakon Daada..badai har an fito ba..?
Imran na Shafa keyarsa yace”Na fito Abba..!
Abba yace”To haka zaka tafi baka ci komai ba..?
Imran ya Girgiza kansa yana Fadin”A”a Abba bana cin wani abu in zan yi doguwar Tafiya..!
Abba ya jinjina kai kafin ya kallesa yana Fadin”To kana da kudi a Hannunka ne..,?
Imran yadan yi Mirmishi kafin yace”Kada ka damu Abba..!
Abba yace”Dole na Damu mana..Zaka gane gidan kuwa..?kadai kula da kanka kaji ko in baka gane ba ka kirani!
Imran da ya Murmusa sai da kyakyawan Fararan Hakoransa suka Bayyana ya Mike yana Fadin”Abba am not a Boy fa..?Nasan abunda nake yi..Zan kiraka da Zarar na isa Dukku ku gaisa da Daada..!
Abba yace”Shikenan Allah ya kaika Lafiya Daman mun yi mgana da ita da Safe bam ma gayamata zaka zo ba..Nasan Zataji Dadin ganinka..!
Kai Imran ya Kada bai yi mgana ba suka kara yin Sallama da Abba ya Fice bayan ya Fadaamai Sagir zai kaisa Tasha da mashin dinsa Zai bar mai Mashin din a wajensa har ya Dawo Abba yace hakan yayi nan ya fice Abba da Safiya suka bisa da Faten isa Lafiya.
Yana Fitowa ya Hau mashinsa ya Fice Daga Gidan Iro megadi ya bisa da Allah ya Kiyaye Daman sunyi Waya da Sagir Tun jiya da Daddare,kuma da Safan nan sun yi mgana yana Kofar gida yana Jiransa,yana zuwa Sagir ya Karbi Tukin Mashin din Imran ya Dawo baya ya zauna suka tafi Tasha koda da sukaje Motar Gombe suka Tarar ta kusa cika Sai Imran yace bari ya Hauta in yaje Gombe sai ya Hau Mota ta karisa dashi Dukku.
Akwai kudi a Hannunsa Sauran kudinsa Bankinsa ya Ciresu Saboda Tafiyar nan,20k ya Cire ya bar 10k agida Saboda akwai abunda zai yi dasu in ya dawo 10k ya Sako a Aljihu Saboda Tafiyar nan
Kafin Motan ta karisa cika suka Tsaya nan Gaban Motan suna Mgana Sagir ya kallesa yana Fadin”To ita Inteesar din tasan zaka tafi Dukku Saboda ita..?
Imran ya bata rai Cikin bayyanar Bacin Ransa yana Fadin”Ita Datake Fushi Dani..!.
Sagir ya kallesa cikin Mamaki kafin yace”Fushi to me kayi mata..?
Imran ya mele baki ya fara bama Sagir Labarin abunda ya Faru ya Karishe da Fadin”Kaji fa wai yarinyar nan ni zata Rubuto ma wai khamis Mijinta..?ni fa ta rainani yarinyar nan Naji dama sanda take fadin haka tana kusa dani na Daki bakinta sai yayi Jini nan gaba zatasan me zata rika gayamin Tunda ni ba sa”an wasanta bane..!
Yafada Cikin bayyana jin Haushinsa Sagir kuwa Dariya ta kamashi Har da Dukawa Imran ya Bisa da kallon Takaichi yana fadin”Kai fa Banza ne..!
Sagir ya Dago Daga Dariyan Dayake yi yana Fadin”Ban ga Laifinta bafa..wayace kace Sajida Amaryarka..? Ashe ba Dade ai kuma ta baka amsarka Daidai da mganarka..Wow..wannan Salom Soyayyar taku ta fara Burgeni kuna son juna ammh Dukkan ku baku sani ba,Inteesar Tana sonka Shiyasa take Kishin Sajida kamar yadda kake Kishin Khamis..!
Yafada yana kara Sakin Dariya kallonsa Imran yake Cikin Nazarin mganarsa Cikin mamaki yace”Itama Tana Sona..?
Sagir ya gyada kai yana Fadin”Am Very Sure..Itama Tana sonka kamar yadda kake sonta..!
Shuru Imran yayi bai yi mgana ba yana Jujjya mganar Sagir Cikin Dakuna Fuska yace”Ni ai ba sonta nake yi ba!
Sagir ya kallesa yana Dariya yace”Allah ko..?
Imran ya Hararesa yana Fadin”Kai wai a ina kasan Soyayya ma haka Daka ke fadin cewa ina sonta tana sona da karfin Gwiwanka ko ka taba Soyayya ne ban sani ba.,?
Sagir yace”Ni ba irin ka bace..ina shiga Social media ina Hulda da abokai ina Karance karance nasan abubuwa da yawa kan soyayyah ammh ni ban Taba soyayyah ba sai dai irin na yarinta..!
Imran ya saki karamin Tsaki yana Fadin”Shirme kenan..Ni ko na yarinta ma ban yi ba..!
Sagir zai yi mgana kenan akace Mota ta Cika a Hado kudin Mota Dole ya Dakata Imran ya bada Kudim Mota ya Shiga Gidan gaba Key din mashin din Daman yana Hannun Sagir nan yace ma ya riketa a wajensa Har ya Dawo Sagir bai bar tashan ba,Sai da Motar su Imran tatashi Kana ya bar Wajen Cikin kewar Imran din.
Sai da suka Dauki Hanya kana ya Lalubo Wayarsa ya Danna ma Inteesar Kira ammh bata Dauka ba Koda baya son nuna Damuwarsa Dole Damuwar ta bayyana Sako ya Tura mata.