GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zan yi doguwar Tafiya ba Allah ya Kiyaye Hanya..?

Haka ya Tura mata bai saka Ran Zata bshi amsa ba san sai ga Sakonta daman Lokacin Daya Kira suna Lecture ne.

“Allah ya kiyaye Hanya..’
Daga haka bata kara ba,Sai da ya Murmusa daya ga Sakonta ganinsa kawai yayi yana Rubuta mata.

“I miss u….!

Ya tura mata bai kuma damu daman Data bashi amsa ba kamar yadda itama Data gani kamar yana gabanta ta Turamai baki tana fadin”Ba wani nam..Kai da zakaje wajen Wata..!
Ranta kuna yake in ta tuna haka sai dai bata isa ta kankare kalmar Sajida matar Imran bane.

Tunda suka Fara Tafiyar har suka kai bai yi mgana da kowa ba amotar duk da na kusa dashi da Direba da wasu a baya sai Hiran yadda Harkan Tsaro ya Tabarbare sukeyi a kasar nan namu ya Takura matuka da Hayaniyarsu sai dai ba yadda Zai yi bai Tofa bakinsa ba an Tsaya wasu sun siya Ruwa da abubuwan ci na saman Hanya ammh ko Shi ko abunda ba”a so bai siya ba,Har na Kusa dashi ya Siya Buredi da Ruwa yamai Tayi ya Girgiza kai Sunyi Gudu soaai koda 12pm na Rana tayi suna garin Gombe Daganan ya Hau Mota zuwa Dukku Goro kadai ya Tsaya a gombe ya siyama Daada Tunda tana ci sama sama.
Daya saura na Rana ya iso Dukku Daada na cikin Dakinta taji Baba Asabe nayi ma Imran maraba mamaki ya kamata lokacin Dataji sunansa Bata yarda ba ta Zata bataji Daidai bane Alwala ta Dauro tana Kokarin Tada Salla Imran ya shigo Dakinta da Sallamarsa Cikin Kaushunsa Koda yaushe.
Takalmin kafarsa ya Tsaya ya Cire nan Kofar Dakinta kafin ya kariso baki ta Saki Tana kallonsa Cikin mamakin ganinsa Shi kuma gabanta ya karisa Fuskarsa bata bayyana Fara”a Sosai ba sai dai ya Saki Ransa ba kamar yadda ya Saba ba,Har gabanta ya karisa cikin Dan yakensa yace”Daada..!
Daada data kasa mgana ta shafa kansa Daya dan rankwafa agabanta yana gaisheta tace”Kai nake gani ko kuwa Idanuwana ne suka Fara Rauni ne..!
Mirmishi yayi kafin yace”Nine Daada..!
Daada Farinciki ya kamata ta kamasa suka Zauna saman Darduman Data Shimfida bakinta Har kunne Tana Fadin”Masha Allah Sannu da zuwa yanzu kake tafe Imrana? Ya wajen Malami da sauran yan”uwamka ko ba daga gida kake ba domin munyi mgana da Mahaifin naka da Safe bai ce min kana Tafe ba..!
Yana Sauke Jakar Bayansa yake Fadin”Daga gida nake Daada..Wannan Tafiyar ta takanas ta kano Taki ce Daada..!
Yafada yana Kallonta Cikin Jin Dadin yadda yaga Tana Murna da ganinsa Cikin Jin Dadinta tace”Kai..Aikuwa naji Dadi sosai ka kyauta..Yau ina Zuwaira Allah ya jikanta tazo taga  yau da kafarka ka tako zuwa Dukku Domin ka Dubani..,!
Kai ya kada yayi kafin yace”Allah ya jikansu da Rahma..!
Daada ta amsa da Ameen daidai Lokacin Baba aasabe ta shigo mai da Faranti shake da Ruwa da ababen sha,Suka gaisa sama sama ta Fice Ruwa kadai ya Tsiyaya yasha,Kafin ya Ciro goron Daya siyama Daada a aljihunsa ya mika mata ta Karba Tana ta Godiya da saka albarka kamar ya bata Duniya Duk sai yaji Tsausayinta ya kara kamashi ba,tun yau ba yasan Daada Tana matukar kaunarsa Soyayyar Datake yi ma Abba ne ya Shafesa.
Mikewa yayi Dauke da Jakarsa yana Fadin”Daada yi sallar ki..Nima bari naje nayi wanka nayi Sallar na Dawo wajenki nazo akwai mganar da nikeso mu Tattauna..!
Daada na Mirmishin Farinciki Tace”Shikenan ina jiranka..!
Daga haka ya Fice Dakin da suka Sauka shi da Sagir wanchan karon nan ya sauka yayi wanka ya Sauya kaya Saboda duk yaji kayan sun Damesa Karamin Wando ya saka 3Quater,da Wata karamar riga yayi Sallah kafin ya Dawo dakin Daada Baba asabe ta jera abinci mai Rai da lafiyan nan ya Zauna gaban Daada Tare sukaci abinci White rice da Miyar kaza Bai wani ci da yawa ba Daadan ma haka Kunun aya dai yasha da yawa suna yi suna Hira sama sama Sai da suka gama Imran ya Kira Abba ya Bama Daada sukayi mgana.
Sai da suka Natsu Daada nacin goron da Imran ya kawo mata ta kalleshi yana Zaune gabanta yadan Kishigida Daga Jikin gadonta tace”To ina Sauraranka Jikana..Allah yasa kan mganar Tarewar Sajida ne adakinta yau da nayi Farincikin da ban taba yi ba..!
Imran kallonta kawai yayi bai yi mgana sai chan ya Mike Zaune Dakyau ya gyara Zama yana kallon Daada kafin yace”Ita ai Tun Washegarin Ranar da aka Dauramna Aure na gama da babinta..,!
Daada ta Kalleshi Cikin Tsoro kafin tace”Bangane ba..?
Dan Mirmishin Saman lebe yayi kafin yace”Manta da wannan mganar Zamu yita Daga baya..Yanzu dai kan mganar yarinyar nan ne ta kawo ni Daada…plz zan Roke ki kada ki aura mata wannan yaron basu dace da juna ba Infact ma bata sonshi kada ki kware ta kamar yadda kika kwareni..!
Yafada kai Tsaye yana Kallonta Daada Tayi Sagale tana Bin Imran da kallo Tana auna Wasu abuubuwa acikin Ranta,
Cikin Karin Haske data ke so Daga Wajensa tace”Wata yarinya kenan..?kuma dame na kwareka..?
Imran kai Tsaye yace”Inteesar mana Daada..Da yaron nan na wajen Baffa Kabiru wachan zuwan namu kina cewa ya nemi yardanta..,!
Daada tana kara Nazarinsa tace”To menene mtsalan Imrana..!
Imran ya Dakuna Fuska yana Fadin”Mtsala Daya Daada bata son sa kuma bai dace da ita ba..!
Daada ta dade shuru batayi mgana ba ganin haka yasa Imran ya Rike duka Hannayenta yana Fadin”Daada kada ki yarda da mganarsa..Wlh inteesar bata sonsa koda yazo yace miki wani abu karya yake yi..kada ki Saurareshi..,!
Daada ta Sauke Numfashi Tana Fadin”Naji bata sonshi..To wa take so..,?
Imran ya tabe baki yana Fadin”Ni bansani ba abunda kawai na sani bata sonshi kuma amtsayina na Dan”uwanta bazan so hakan ya kwareta ba..!
Daada ta Kallesa ido Cikin ido kafon tace”Kai kake sonta kenan shiyasa kace kada na yarda da mganar mai sunan megidana Hamisu..?
Abazata yaji mganar da Sauri ya Kalleta yana Nazarin mganarta meyasa Daada itama tace ko yana son Inteesar ne Hade rai yayi yana Fadin”Nifa ba sonta nake yi ba..Ni fa ban ma sani ba ko ina sonta ko bana sonta..!
Daada Tayi mirmishin su na manya akallah dai a shekarunta Zata iya gano Inda Imran ya dosa domin ta ma Lura Shi kanshi baisan yana son Inteesar din ba Zuciyartsa ke jansa yana aikata wasu abubuwan baisani ba.
Saboda ta kara Tabbatar da Zarginta ta gyara Zama Tana fadin”Naji bata son Khamis kai ma baka sonta..To na yarda da mganarka ature mganar khamis daman akwai wani yaro dan kawata Aina”u tuni take son mu Hada Zuru”a da ita sai nayi mata mgana yaje ya ganta su Sasanta nasan Zasu Daidaita..,!
Ai kamar Daada ta Zubamai Wuta haka yaji mganar nata,Kallonta yake kai tsaye yana jin Zuciyarsa na suya Daada na Lura dashi Tana Dariya acikin Ranta.
Bata rai yayi yana Fadin”A”a daada baza”ayi haka ba gaskiya..!
Kai Tsaye tace”To ya za”ayi.?ko kana da wanda za”a hadasun ne nifa bana son na Mutu ban aurar da duka jikokina ba Daga Mazan har matan..!
Imran yayi shuru yana wani Tunani Kafin kai Tsaye ya kalli Daada yana Fadin”Ni zan aureta Daada shikenan..!
Daada ta saki Dariya aranta tace Dan kwal uba kama Dawo Hanya ne..
Kai Tsaye tacemai”Sajidan fa..?kasan bazaka Hada jini Daya kishi ba ko..!?
Tabe baki yayi yana Fadin”Daada matso kiji..!
Kunnenta ta kawo ya rada mata mganar da baisan kome yace mata ba Naga dai Daada ta Zaro ido Tana kallonsa kafin tace”Innalillahi wa”inna Ilaihirraju”un Imrana meyasa kayi hakan..?
Batare da Shakka ba yace”Saboda Hakan kadai ne mafita Daada..Kiyi Hakuri ban iya cika Miki Burinki ba..Ammh ki bani Auran Inteesar na miki alkawarin bazan baki kunya ba..!
Daada Cikin jimami tace”A”a itama ai baka sonta bazan baka ita a maimaita abunda ya Faru ba..!
Da Sauri yace”Bazai faru ba Daada..Nifa ina son ganinta kusa dani ban Tsaneta ba..Kinga ai zan iya Zama da ita ko..!?
Yafada batare ma Daya sani ba Daada Tayi Shuru batayi mgana ta shiga wani Tunani,acikin Ranta bata isa tace ma Imran A”,a ba kodomin ta gyara Kuskuranta na baya na Auramai Sajida Domin gyara Zumunci sai dai abubuwa sun Faru marasa Dadi.maimakon Zumuncin ya gyaru sai abubuwa suka Lalace a mganganun Imran ta Lura yana son Inteesar wannan ne karo na Farko Daya nemi wami abu a wajenta bazata hansa ba Tunda ya kasa Rike abunda ke Ransa yazo ya gayamata kuma Tabbas Zatayi amfani da wannan Damar ta nuna ma Mami Asma”u kuskuranta ta kuma Nuna ma Kabiri sakacin da ya aikata,
Duk da abunda Imran ya aikata bataji Dadinsa ba Da Sajida da Inteeaar duka nata ne,Sai dai gwara hakan gwara ayi abunda za”ace gwara da akayi da Abunda Daga baya za”a zo ana nadama ita kanta Daga wannan Datayi bazata kara aikata irin wannan Kuskuran ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button