GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDANMU 1&2 COMPLETE HAUSA NOVEL

GIDANMU COMPLETE HAUSA NOVEL

Mami Asma”u dataji labarin Ta Dauka mganar Khamis ne da Tarewar Sajida Lalle Lokaci yayi da zata Tauna aya Domin tsakuwa taji Tsoro sai Imran ya Raina kansa Sajida na makaranta Baffa ya Kirata yace in ba mtsala tazo Gida zasu da ita Dukku ne Daada tace taje,Tana jin haka bata tsaya wasa ba Ta Tattaro ta dawo gida Daman Damar nan take jira Tunaninta itama ya Tafi kan mganarta da Imran Allah yasa mganar Biki ne da Tarewa da sai tafi kowa Murna.
Su Inteesar dai zasu fara Test Monday sukace bassu je ba,su aka bari agida Da Anty Safiya su Sadam su kadai suka Tafi sun bar iyalansu agida.
Ranar Jumma”a Abba da Ya Yusuf da Sadam suka tafi a Motar yusuf din Imu yana Wajen aiki yace sai asabar da Safe zai taho
Baffa Kabiru ma sai Ranar asabar yace zasu zo su Daddy ne chan su Abba suka iske su shi da Umma da Basheer Inna Bintalo ta iso ita da Inna Maimunatu wannan karan ba yaran kowacce ita kadai tazo,Sa”id ma Aranar da Daddare ya iso Daga Dutse.
Imran sai Ranar asabar da Safe shida Sagir suka hau Motar Haya zuwa Dukku agida ya bar Motarsa

Shakira
3/23/22, 12:02 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?15

Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488

Basu isa da wuri ba,Sai wajen 12pm na rana duk da sun fito da wuri,Sagir dai nashi dan bi ne domin baima san da Tafiyar ba,ana gobe Tafiyar ya kirasa a waya yace mai ya shirya gobe Zasu tafi Dukku ya zata ma amotarsa Zasu tafi Imran din yace A”a saboda bai wani san hanya ba Yusuf ne yasan Hanyar sosai,infact ma bai yi niyyar zuwa da Motar tasa ba.
Sagir kallon Imran kawai yake Ko da bai gayamai komai irin Mirmishin Dayake ta saki na kasan Lebe yasan na mugunta ne irin Mirmishin Imran naci Nasara shifa Bai taba ganin mutum mai sa”a kamar Imran ba Komai ya sama gaba sai yaga bayansa komai yace zai yi to tabbas Zai yi ne yana da kyawawan Halayya da ba kowa ke sanin haka ba sai kana Tare dashi,Mashin dinsa Halak malak ya mallakamai Sagir din Saboda ai ya Chanchanta shi Sagir din ma yaki amsa Daga Farko Imran din ya wurgeshi da key din yace in bayaso to ya Bada ita yadai san In Imran ya Fadi mgana baya sauya mgana Mashin dai ta Zama nashi sai dai shi yayi abunda yaga Dama da ita.
Koda suka isa Tuni bakin Abuja sun iso,Hatta Khamis ya iso,Daman jiya da Daddare ya sauka a Abuja da Safe suka kamo Hanya Harda Sajida Umaima Tana gida Saboda makaranta.
Imran bai yi wata Shiga ba kamar yadda ya saba haka yayi sanye yake da Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa ce Mai Hasken wandon kuma Shima mai ruwan kasa ne sai dai yana Duhu sosai,Wando daga kasa ya Tsuke kadan Ya kamasa.
Sun shigo Har falon Daada inda su Umma ke Zaune ita da Mami Asma”u da su Sajida dasu Sa”id da Basheer,Su Abba suna Dakin Daada tun da suka Shigo Sajida idanuwanta suka Kafe akanshi shi Wlh bai ma ganta ba yaga dai Uwarta wacce ko kallo bata isheshi ba Umma kadai ya gaisar Kadahan kadahan,Sai ya karisa wajen su Ya Yusuf suka gaisawa ta Hanyar yin Musabaha,Abun mamaki Da kansa yau ya mikama Khamis hannu suka Gaisa suna kallon Juna ido Cikin ido.
Imran kallon kayi kadan yake yi ma Imran irin na Riga na gama Dakai shi kuma Khamis Kallon Au ka Tuba ne..?Irin dai dole dai ka dawo Hanya yaro.
Daganan Dakin Daada ya Shiga ya gaida su Abba,Da Daddy sai Inna Maimunatu,Yana kallon Goggo Bintalo da Baffa Kabiru yaki gaishesu da Abba yayi mgana sai yayi Shuru ciki Ciki ya gaishesu kamar bai ganesu ba,Abun yayi ma Inna Bintalo Ciwo sai dai bata mgantu ba Kada yaron ya Zageta tasan Tsab zai iya Tunda bai da kunya,Baffa Kabiru kam bai Damu ba Domin yasan Daman yaron baya Darajasa kuma bai Dauke sa a Uba ba.
Dakin da suka sauka wanchan karon nan suka kara sauka shi da Sagir wanka Imu yayi ya sauya kaya saboda yana jin Zafi,yazo da karamar Laptop dinsa saboda aiki akwai aikin da Wani Ma”ikacin su zai turo mai Daga gyagyadi branch yau din so yana Bukatar ya Duba shiyasa yazo dashi Wayarsa ya Dauko domin yaji karan Shigowar sako Kamar yadda Ya zata Intee ce.
Tana Tambayansa ko sun issa Lafiya ya Tura mata da cewa eh suna Dukku,Daga haka ya maida wayarsa aljihu,agogon Tsitsiyan hannunsa ya Duba yaga lokacin Sallah ya kusa Daman ya Dauro alwala cema Sagir yayi alwala su tafi masallaci ba Musu ya tashi yaje yayi alwala suka Fita Tare koda suka fita duka mazan suna Waje suna alwala har da su Abba ya Hadu da Mami Asma”u a Falo bai ko kalli barayinta ba,Dariya yake cikin Ransa Domin har yana Hango irin yadda Zatayi in taji Hukunci da ya yanke akanta da ita da yarta.
Gabadayansu suka Dumguma zuwa masallaci sai da suka Tsaya aka Tada sallar tunda sunje da wuri bayan sun idar suka nufo gida.
Imran da shi da Sagir suna Baya sai Daga baya suka Shigo gidan Tun Daga Nesa ya Hango Sajida Tana Tsaye ko da bai sani ba yana da Tabbaci shi take jira zatayi mgana dashi Sanye take da wani material mai Santsi Dingin Doguwar riga ta yane kanta da karamin Bakim Vail kafarta Cikin takalmi baki sawu ciki a Fuskarta ta Rame sosai Idanuwanta duk sun Sauya Launi
Sagir na ganinta ya Zunguri Imran yana Fadin”Ga Amaryan ka nan..!
Ko kallonsa Imran bai yi ba sai ma kara Tamke Fuska da yayi kamar bai Taba Dariya ba Har suka kariso kusa da ita Sagir na Shirin Dakatawa Imran ya wuce Kamar ma bai ganta ba ganin haka yasa Sajidan da gabanta ke Fadi Saboda yadda Imran din yayi mata Kwarjini tace”ina yini..!
Imran yajita ammh yayi kamar bai jita ba ya cigaba da Tafiyarsa Sagir Daya ga haka ya Daga Murya yana Fadin”Imu tana gaisheka fa..Don Allah ka Tssya..!
Da kamar bazai Tsaya sai Wata Zuciyar tace ka Tsaya ai ba wani Sauran Rina Dake Tsakaninku.
Cak ya Tsaya Lokaci Daya yana juyowa Hannuwansa ya Haarde Saman Kirjinsa yana kallon Sagir irin gashi na Tsaya sai yaya..?
Sagir ne ganin haka yasa ya Kalli Sajida da kanta ke kasa jikinta ma ya fara rawa tana ta wasa da Kwalliyar Jikin Rigarta.
Ya sanyaya Murya yarinyar ta bashi Tsausayi saboda yasan wacce Zata iya gaba da gaba da Imu ba karamar Jaruma bace
Yace”Ki je ki sameshi in ba haka ba zai Tafi abunsa..!
Daga haka ya wuceta da sauri kusa da Imran ya karisa daidai kunnensa yayi mai Rada”Plz ka saki Ranka She is ur Wife..!
Sanda Sagir ya fadi haka sai yaji kamar ya Mangaresa da mari,sai kuma yayi Fuska kawai ya kara Hade rai ko kadan ba annuri ballatana Samun sukuni agame dashi Sagir dai Ciki ya shige yana Fatan kada Allah yasa Imran ya zabgama yarinyar nan Rashin Mutumcinsa.
Gajiya yayi da tsayuwa ganin Ta na nan Tsaye bata ma tako ba,juyawa yayi niyyar tafiya sai gata ta kariso Salau Salau kamar mara kuzari aransa yace ji ta kamar wata ta Allah.
Kanta na kasa bata son Hada ido dashi Tace”Ina yini..!
Tafada Lokaci Daya gabanta na Faduwa,Saboda bata son kallonsa kwayan idonsa yana bata tsoro matuka yana saka taji duk wani Comfident dinta ya tafi indai tana gabansa gabanta sai Fadi yake in da Zai lura har rawan jiki dana Baki take yi alokaci Daya.
Kallonta yake Daga sama Har kasa so yayi ya sakin mata Tsaki sai kuma ya fasa cikin Dauke kai da Dakuna Fuska yace”Lafiya..!
Yafada yana kallon Fuskarta acikin Ransa yace irin Fuskar uwarta ya”yan nagada ba na haya ba.
Gajiya yayi da tsayuwa yasa yace”Ammh kinsan dai ba wasa tsakanina Dake da zaki Tsaidani ki tasani agaba kuma kiki mgana ko..?
Yafada cikin Kaushinsa kamar ko yaushe.
Jim haka yasa ta kara Sadda kanta Tana Fadin”Dama..Dama!
Wani Haushi ya kamashi yace”Dama What..?ke kinga ni ina da abunyi yanzuma Da kika ga na Tsaya Wlh ba wai domin darajanki bane ke har kin Isa..? Ba macen data isa ta sani ni Imran nayi abunda ban yi niyya ba Darajan Abokina kikaci..So in baki da Fada on my..!
Bata bari ya karisa ba,Tunda taji mganarsa Cikin Kaushinsa kafin tace”Dama ina ta Kiranka a waya ne baka Dauka ba Daga baya kuma sai na Daina Samun ka..!
Karamin Tsaki yaja kai Tsaye yace”Nayi Blooking dinki ne..!
Batasan Sadda ta Dago rinannun Idanuwanta Tana kallonsa ba Cikin mamakin kalamansa Duk da tasan dai Ya kulleta ne ammh bata Zata zai iya gayamata haka ido Cikin ido ba.
Ganin irin kallon Datake yimai ne yasa ya Daga mata gira guda Daya yana Fadin”Yes..Saboda bana son Wata mu”amala ta shiga Tsakanina Dake Infact ma bamu da wata alaqa..!
Bai bata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin”Nasan zuciyarki na Fada miki ba an Daura mana aure ba..? Auran Dan iska dan Shaye shaye bai Dace da Sajida Kabir Dukku ba Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi Diyar na gada ba na Haya ba..To u better wake up..kinga kuwa ni ban Dace dake ba..Ke ba Matata bace bamu da wata akala!
Gabadaya kalamansa sun rikitata Bata san Sadda ta dago kanta Tana kallonsa ba sanda yace ita ba Matarsa bace Kara Dakuna Fuska yayi kafin yace”Eh nace bamu da akala ko muna Dashi ne? Nasan zaki ce to ko ba aure ai ni yar”uwarka ce u ara mad in kikayi Tunanin haka akaina ni Imran Wlh wanda keyi dani sai ma naga Dama Zanyi Dashi acikin Dangi ballatana Wanda basan da wanzuwarsu ba So plz and plz ki Rabu dani kada ki kara Kirana am not ur mate kada ki kara Kirana In baka ba Haka zaki san Oder Side dina!
Tsaki yaja mai karfi yana Fadin”Rubbiish kawai..!
Daga haka ya juya ya shige cikin Gida,da kallo ta Bisa Hawayen da suka cika mata ido suka zubo mata masu Zafi da Tsananin kaunar Imran Kuka Take so ta fashe dashi ammh Zuciyarta ta Chuse waje Daya Meyasa yace ita ba Matarsa bace ko ya saketa ne?
Saurin dafe kanta Tayi jin ya sara mata da wannan Karamin Tunanin a Fili ta Furta”A”a bazai taba sakina ba..Bazai sakeni ba bazai sabama mganar Baffa data Daada ba..Wlh ina sonsa inajin kamar in na Rasashi Zam iya Mutuwa..!
Take Fada tana Sharan Hawayenta kamar Wata Tattabiya soyyaya Ta sakata Zatayi hauka kafin ta Dibi Sauri Zuwa Cikin Gida.
Tana shiga Taga ana ta cin Abinci Mami Asma”u dake Faman nemanta ta Tsareta da ido Cikin Tuhuma Tana fadin”Ina kika shiga Tun dazu..!?
Cikin kame kame tace”Na fita amsa waya ne Mami..!
Tafada Tana kallon Imran Dake kusa da Yusuf suna cin Alalan da Baba asabe Tayi a Filet Daya,Ko barayin Datake bai kallah ba kansa na kasa ya bada natsuwasan kan abun ke gabansa.
Hararanta Mami Asma”u tayi Tana Fadin”Waya ko..? Ita kuma wannan ta waye..?
Tafada Tana Daga mata wayarta da ta barta gefen Mami Asma”u din bata sani ba.
Kanta ta Sadda kasa batace komai ba Hankalin kowa baya kansu Ba wanda ma yabi ta kansu su Abba suna Dakin Daada achan suke cin nasu abincin.
Mami Asma”u kure Sajida da ido take yi,Tana Nazarin wani abu acikin Ranta Taga shigowar Imran kuma ba Dadewa Taga Sajida ta shigo Allah yasa ba ajinta ta Zubar taje tayi mai mgana ba in ko hakane da sai taci Uban Sajida in ta kuskura tayi mata wannan Shirmen.
Abinci tace tazo taci bata cikin good Mood yasa tace bazata ci ba wucewarta Tayi Dakin da suka Sauka ita da Mami Asma”u ranta duk ba Dadi Mami Asma”u ta bita da wani kallon yarinyar nan Tana Hauka ne..?
Ba a dauki Lokaci ba kowa ya gama cin Abincinsa nan mazan suka Zauna suna Hirarsu Imu ma na cikin su sai dai baya mgana Sai dai yana jinsu kawai in abun mgana ce aka Sako sa sai da ya gyada kai ko ya Rage Daure Fuskar Wayace a hannunsa Mgana suke da Intee Tana mai shagwaban gida ba kowa duk ba Dadi tana Missing dinsa,Sakar mai da kasala Take duk da ba Waya suke ba Massages ne bai biye mata yace ta wuce taje ta Dauki Littafanta Tafara Karatu baya son Shirme.
Suna nan Zaune sai ga su Abba sun Fito Dukkansu sun taso Tsohuwa Daada agaba Tana Tafe sanye da Hijabi mai ruwan kasa,Bai da Tsawo sosai Carbi ne a Hannunta tana ja Inna Bintalo da Inna Maimuna suna Kafada kafada da ita sun sakata a Tsakiya.
Kan kujera suka Taimaka mata ta Zauna Gabadayansu suka Zauna a kasa Umma Dake saman kujera ta Sauko ta zauna akasa,Daman Mazan duk suna Malale zaune ne saman Cafet din Daya malale Falon.
Mami Asma”u dai Bata sauko ba sai ma kara gyara Zama datayi akan kujeran ta kara gyara Zaman Siririn Gilashin Dake idanuwamta Khamis na gefenta a kasa yazauna wajen Kafafunta.
Tuni Falom yayi Tsit sai Sautim Muryoyin su Sa”id da suke ma Daada Barka da Fitowa amsawa take cikin kulawa,Tana Bin Kowa da kallo Daya bayan Daya sai ta sauke kallonta kan Mami Asma”u wani abu na cin Ranta Uhm Lokaci yayi da Asma”u zata gane Kuskuranta Juyawa tayi Tana kallon Baffa Kabiru kafin tace”Ina Sajida..?banganta ba ko bada ita kuka zo ba..?
Kai ya girgiza mata kafin ma yace Wani abu Mami Asma”u ta yi Caraf tace”Da ita muka zo mana Daada..Yanzu ta shiga ciki..!
Daada ta gyada kai kafin tace”Jeki kirata..Domin wannan Haduwar ta Shafeta sosai..!
Mirmishin Saman baki Mami Tayi Damam ai tasan mganar Sajidan da wannan Tsagerin yaron nan Lalle kuwa yau Zata nuna ikonta a Mtsayinta na uwa,Sai ta ja Imran a kasan Kafarta bai isa yaja da ita ba.
Tana shiga Dakin ta iske Sajida kwance Tana Hawaye jin muryanta a saman kanta ne yasa tayi Saurin Share Hawayenta ta mike Zaune tana kokarin Kauda idonta kada Mamin Ta gano Halin Datake ciki.
Kallon Tsab Mami Tayi mata kafin Tace”Wai Sajida kukan Uban me kike yi ne Tun dazu..?
Sajida tace”Kuka kuma..? Ni ban yi kuka ba Mami..?
Tafada tana kokarin mikewa ta kaucema Kaifaffun Idanuwan Mami Asma’u Daga gano yanayinta.
Mami Ta wani kalleta a karkace kafin tace”Kina Zaton ban san kukam me kike yi bane..? Uhm yaro man kaza..Dazu fitan da kikayi wajen Dan iskan yaron nan kikaje..!
Sajida ta Dago kanta cikin mamaki ta Bude baki Zatayi mgana Mami Ta Dakatar da ita lokaci Daya Tana Daga mata Hannu tana Fadin”To bari kiji na Fada miki in ma Kina kokarin Saukowa ne ki yarda da auransa Cikin Sauki ni Asma”u uwarki ban yarda ba ko Zan amince da wannan auran ba yanzu ba sai na ja Yaron nan akasan Kafata ya duka yana kuka yana Bani Hakurin Rashin Da”ar da yayi min sannan kuma yana kuka yana Rokon na bashi ke sannan zan iya yarda ma ki Zauna dashi ammh in ba haka ba Duk wacce Za”ayi sai dai ayi bazan bari ki Zauna da wannan Dan iskan yaron ba.!.
Tafada cikin son Tabbatar da mganarta bata damu da yanayin Sajidan ba ta Fice Tana Fadin”Ki fito Daada na kiranki..!
Sajida Kuka ya kwace mata Mami bata son Imu shine Rayuwarta ba Wani irin so mai Tsanani ne ya kamata alokaci Daya tana jin kamar Zata Mutu in ta rasashi Wata Zuciyar tace to ke sai ki bari ki rasashi..Ina bazata taba bari haka ya Faru ba Imran mijinta ne kuma Dole tayikomai Saboda ta Dauwama Dashi Wannan karon zata Dakatar da Mami Zata Fadamata gaskiya She Love Imran Tana matukar sonshi kuma Zata Zauna dashi a duk yadda yake so ta kyaleta don Allah kada ta Shiga Rayuwarta ta lalata mata
Tiolet ta shiga ta wanko Fuskarts tazo ta Tsane da mayafinta kana ta Fito Falom ita ake ta jira ba”a Fara Taron ba Tana Zama gefen Dan”uwanta Daada ta kalli Yusuf Tana Fadin”Yusufa Bude mana Taron da addu”a..”
Ba musu ya gyara zama ya Bude Taron da addu”a aka shafa sannan Daada tayi gyaran murya ta Fara mgana..!
“Da farko dai ina yi ma Duka ya”yana da jikokina da suka Taru anan wajen barka da zuwa..nasan kun baro duka Tarun ayyukan ku ka amsa kirana Naji Dadin haka Allah ya saka Muku da mafificin Alheri ya raya muku Zuru”a ya baku ya”ya wadanda zasu ji kan ku kamar yadda kuke jin kaina..!
Gabadaya aka amsa mata da Ameen Ameen.
Kafin ta dan yi shiru kafin ta Cigaba Cikin muryan tsufa”Dalilin Dayasa nace ina son ganinku duka da wasu Daga cikin yayenku Mgana ce Daya zuwa Biyu..na farko mgana ne kan Imranu gashi chan Dan Wajen Malami sai Sajida Yar wajen Kabiru..Kafin naje gaba a mganata kowa anan wajen ya Shaida Auran dana saka aka daura shi Wata Daya Daya gabata a garin nan tsakanin Imranu da ita Sajidan ko..?
Kowa ya gyada kai alamun hakane Daada tana Jan Casbahanta tacigaba da Fadin”Alhamdulillah kuma kowa anan yasan abubuwan da suka yi ta Faruwa bayan an Daura auran da kafin a Daura Inda Asma”u gatanan matar Kabiru ta rika nuna rashin Amincewarta tare da Diban albarka kala kala ammh duk na kauda kai bam ce komai ba Saboda bai kamata nayi mgana alokacin ba Kuma ni miye nawa..?ko me zan ce tunda agaban Mijinta ne Gashi nan kabiru bai Tsawarta mata ba kenan shima ya yarda da duka abunda ta Zauna akai bai so hadin Zumunci Tsakanin jininsa da jinin Abubakar ba..!
Tafada Tana dan Sauke Numfashi Kowa afalon yayi shiru yana Sauraranta Baffa Kabiru ya dago kansa ya kare kansa Daada ta wurgamai wani kallon Da Dole yayi Shuru da bakinsa Mami Asma”u kuwa na gefe Kafa Daya kan Daya tana karkadawa alamun tana jiran kowa wanda yace kule sai tacemai Chass..!
Daada ta cigaba da Fadin”a lokacin da nayi Tunanin wannan Hadin har ga Allah Zuciyata Daya ina ganin cewa hakan shi Zai kara mana Dangom Zumunci da son junanmu sai Daga baya na gane nayi kuskure kuma nayo Hadi inda bai kamata ba na manta Asma”u ita ke jan Ragamar Rayuwar gidan Kabiru tamkar itace mijin shine Matar baya iya Zartar da mgana sai abunda tace,Sannan ko mganace ta Dangi bazai iya mgana ba sai da yawunta ko da amincewarta Shiyasa data nuna bata amince ba shima ya Goyi bayanta..To Alhamdulillah na Taraku ne anan saboda na gyara Kuskurena..Mustapha ina son ka bama Danka Imranu auran Diyarka Maryama mai sunana ba sai gobe ba yau din nake son adaura wannan auran indai kaima ka amince saboda ina Tsoron nuna isata akan ku Alhalin ban isa ba!
Gabadaya Falon sai kallo ya koma Wajen Daada ita kuma ko ajikinta Sagir ya kalli Imran alamun How comes,shi kuma ya Dagamai gira Khamis da yayi mutuwar Zaune ya Dago yana kallon Daada lokaci Daya ya koma yana kallon Imran wanda ya Cije mai baki ya Dagamai girarsa Duka Biyu irin kaga nawa ikon..?to yaya Zata zama takan ne..?
Gabadaya kowa sai mamakin Daada yake yi,Yusuf ya kalli Imran ganin ko ajikinsa ya juya yana kallon Abba da Daddy da suma suke kallon Daada aransu suna Tunanin Riikicin Tsufa ya Fara Taba Daada.
Daddy ne ya bude baki zai yi mgana Abba ya girgizamai kai,Baffa Kabiru kuwa bai ce komai ba Domin ya kasa Dora komai akan Mizani..
Sajida kuwa allah ne kadai yasan Halin da Zuciyarta take ciki gani take kamar ta Kurmance bataji Da kyau ba Mami Asma”u kuma mamakin yadda Zaton ta ya sauya take yi anya Daada nada Hankali kuwa..?
Abba ne ya Dago yana kallon Daada Cikin Sanyin murya yace”Daada bawai ina ja da mganarki bane..ko kin manta cewa Imran ya auri Sajida kuma Inteesar Shakikiya ce ga Sajida Daada duk da ba Haram bane ammh ana barin Halas ko dom kunya..!
Karamin Mirmishi Daada ta saki kafin Tace”Na sani..Ina sane da komai..Ai ba aure Tsakanin Imranu da Sajida a yanzu..!
Gabadaya mamaki ya hana kowa Mgana Inna Maimunatu ce tace a wannan karon”Daada bamu gane kan mganarki ba..!
Daada ta Dago ido Tana Fadin”Ku juya amsarku Wajen Imranu..Kai Imranu gayamusu abunda kazo ka Fadamin..!
Imran ba wani Tsoro ko Fargaba ya Dago kansa yana kallon yadda gabadaya Idanuwa suka koma kansa Ya gyara Zama yana kallon Idanuwan Mami Asma”u da Sajida da ya kusa Fadowa saboda Firgici da Tsoro.
Cikin Kaushin sa yace”Na saki Sajida Tun Washegarin Ranar da aka Daura mana Aure da ita..!
Ya fada kai tsaye Lokaci Daya yana Fito da wata Takardan a Aljihun Wandonsa ya mikama Yusuf Dake kusa Dashi Wanda yayi Jagale yana Bin Imran din da kallon mamaki.
Kalamansa sun Daki kowa afalon banda Daada Data san mganar.
Ammh Firgicin yafi bayyana kan Fuskar Baffa Kabiru,Mami Asma”u da Sajida wadanda Tsabar Rudani ko Motsi sun kasa.
Daada ta Umarci Yusuf ya Warware Takardan ya karanta afili kowa yaji Cikin Sanyi jiki ya Bude Takarda ga Hand Writting din Imran nan ya Rattaba Rubutun kamar haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button