
Aikuwa Abba shi da kanshi Ya gaji Daman da Ganin Inteeear da Imran suna Raba Dare a Gidansa kullum Ta dawo makaranta Chan take yada Zango shima in ya Dawo aiki yana nan Abba ya Kirasu yace su Zauna gidansu Inteesar kada ta kara Biyowa in sungama Exam ta Koma Gida shima in ya tashi aiki ya wuce Gida Imran ya Dinga Kumburi wai Abba na Koransa Abba yace Eh ya Koresa in yaji Haushi kda ya kara Dawowa
Imran yaji Haushi Tunda ga Ranar yace ma Inteeesar in taje makaranta Ta Rika Dawowa Gida,Inteesar sai Kumburi Take Imran mamaki ya kamasa Lalle yarinyar nan wato saboda ya sakarmata da Farko Tana yadda Tagama Dama shine ta Fara Rainasa ai kuwa yaFita Butunta bama Tunanin Ya Tsaya ya Lallasheta bai da wannan Lokacin.
Shakira
3/28/22, 21:16 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?26
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
Inteesar kwana Biyu ta Dauka Tana Fushi da Imran kan Hanata zuwa Gidan Abba shi kuwa baima san Tanayi ba in ma Fushi ne tayi ta gama Shi baima nuna ya gane hakan ba Ballatana ta saka ran zai Lallasheta.
Kwana Biyun ko mgana batayi mai Daga gaisuwa shikenan kuma bataje Makaranta ba basu da jarabawa daman Guda biyu ya Rage musu su gama.
Abun ma nata sai ya koma basa Dariya ko Falo ta Fito da Daddare ta gansa Zaune yana aiki sai ta wani Dauke kanta ta zauna chan nesa Tana Taba wayarta ko Tana karatu Duk yana Lura da ita,bai kuma Taba nuna mata yana ma Fahimceta ba.
Bata san wani abu ba Shi ko basu yi mgana ba Ganinta kawai da Tabbacin Ita din matarsa ce wani Sinadiri ne na Farimciki da Samun Salama da Sukuni a Rayuwarsa.
Data gaji ne da kanta ta Hakura Sanin bazai Taba Sauya mgana ba Ballatana Ya Imu dai baisan ka bata rai kan yayi wani abu ya baka Hakuri ko ya Lallasheka ba.
Imran bai taba jin Labarin Soyayyar Sagir da Hafsah data Khalil Data Munari ba shi ya Dauka da aka gama Biki sun kama kansu da rawan Jikin da suka Dinga yi kan yaran sai Ranar Yaji Inteesar na mgana da Hafsah ta Waya suna Zencen mamaki ya gama kamasa aransa yana Tunanin meke Damun Sagir da Khalil ne..?
Banda Tsabar jama kai Raini ina su ina Wadanan yaran..?
Yana Zaune ne saman Kujera Sanye da karamin Wando 3Quater da Karamar Riga mai Gajeren Hannu Laptop dinsa ne a gabansa yana wani aikin da gobe Manager din Branch din Gyadi gyadi zai karba yaji suna mgana ita duk azatonta yana aikinsa baya jinta bata sani ba Duka Motsinta a idonsa ne sai dai yana komai da Taku ne kuma yana da Karfin ji kamar Maciji Daga cikin Wayar ma yana jin Abunda Hafsah take Fadi
Har suka gama waya bai yi mgana ba Inteesar Complex take sha batayi Girki ba Gogan bai Damu ba Daya Dawo Tea kadai yasha Cikinsa ya Cika.
Sai da suka gama kana ya Dago yana kallon Inteesar Dake sanye cikin Wata Riga mai Taushi tashan Iska sai dai Tana da dan Kauri kadan sai dai bata da Dogom Hannu kanta Hula ce ta Zamani ta yanmata ta Rufe kanta Dashi Kafarta Daya kan Daya ta Dora Tana shan Complex dinta.
Suna Hada ido ta Turamai baki Har da Murgudawa Ido ya Ware yana Fadin”Ni kike Harara kuma kike Turamin baki harda Murgudamin Baki Duka ni kadai..!?
Cikin Tabara tace”Ni fa badakai nake ba..!
Yana Sosa Gemunsa yace”Uhn..Kin rainani..?to bada ni kike ba dawa kike..?akwai wani agidan ne bayan ni dake..,?
Yafada yana Tsareta da Kaifaffun Idanuwansa bazata jure ba yasa ta Kauda Kai batayi mgana ba sai Chan Tace”To ba kai bane..Sai kazo ka zauna ko fa Hira bakamin ni in nayi mgana kace zan dameka da Hayaniya kana aiki ne..!
Imran na Cigaba da aikinsa yace”Yes..Ko ba aikin nake yi ba..?in na Biye miki zaki hanani aiki na ne..!
Jin haka yasa bata kara mgana ba Ta Cigaba da shan abun Dake Hannunta Shima haka sai chan yace”Wai wasu yara ne Sagir da Khalil ke soyayya dasu..?
Yafada yana Cigaba da aikinsa bai Dago ba,Inteesar Taji Hira ai sai ta Gyara Zama tana Fadin”Sagir yana son Hafsah..Shi kuma Khalil Munari..Don Allah basu Dace b..?munari tace min yace soon iyayansaa zasu zo ayi mgana Hakama Sagir..!
Mamaki ya Cikashi Cikin karin mamakin ya Dago yana Fadin”Wacece Hafsah..!?
Inteesar tace”Laa..Hafsah Autan Goggo Maimuna,wacce ke karatu nan Dutse tana zaune tare da su Ya Sa”id..!
Kai ya gyada yana Fadin”Su yaranan suke so..?yaran da yaushe aka gama Share musu majina..Khalil da Sagir sun ji Haushi basu da Girma sai na Jikinsu..!
Inteesar ta Rike baki Tana Fadin”Munarin da Hafsah ne yara Ya Imu..!,?
A karkace yace”Eh in ba yara ba manya ne..?
Inteesar tace”Tab..Age mate dina ne fa Nima kenan yarinya ce..?
Imran ya Dage gira yana Fadin”To ai kema Duka Kina Layinsu yarinya ce Baki san abunda kike yi ba..!
Yafada kai Tsaye Inteesar ta Mike Tsaye Har tana neman Ture Mug din Dake Hannunta Kan Centet Table din Dake gabansa ta Dankwar dashi Tana Fadin”Ni ce ma yarinya..?ni ce bansan Abunda nake yi ba..?
Tafada kamar zatayi kuka Imran ya Hade rai yana Kokarin Danne Dariyansa yace”Eh mana..!
Ai sai Inteesar ta Fara Buga Kafa tana Tsallen Shagwaba da kukan karya Tana Fadin”Ni Wlh ba yarinya bace..Babba ce Tunda nayi aure..!
Mirmishi yayi yana Kokarin Boye Dariyansa yana kallonta yace'”Ai wannan aikin ma da kike yi na yaran ne..Kuma kin ce ke Babba ce Tunda kin yi aure ko..?
Kai ta gyadamai Tana Jan Hanci kamar mai kukan gaske,Kansa yake Shafawa yana Fadin”Ai fa ga Babba nan..Sannu Babba..!
Yake Fada yana Dariya Inteesar an samu Waje kawai sai ta koma ta Zauna Dirshan saman Cafet ta saka kuka Baki ya saki yana kallonta Kafin ya Gimtse Fuska yana Fadin'”Lalle ma yarinyar nan Duka kike so inaganin ba Lallashi ba ko..!?
tsayawa Tayi da kukan Tana kallonsa kafin Ta waro ido Tana Fadin”Duka..?
Kai ya gyada mata yana Fadin”Eh mana nan fa ba Umma ba Daddy..Wlh kika Dameni Zanemiki jiki Zan yi.U..!
Ai bai gama mgana ba Ta Mike da Sauri ta Dauki Wayarta da Mug din Datake shan Complez suma sum Ta Shige Kitchen bata Dade ba ta Fito ko Gud Night din ma batacemai ta Shige Dakinta Dariya yayi yana Fadin”Better..!
Domin bai Shiryama Rigimarta ba a wannan Lokacin Ita batasan Tana Dagulamai lissafi bane Shiyasa take kara yin wasu abubuwan.
Abun na Ransa bai manta ba Washegari Daya Fita aiki Bayan sun tashi Lunch ya Kira Sagir yana Cemai yanzu banda Tsabar Raini da Zubar da Girma ina su ina soyayya da yaran da ko Hankalin kansu basu gama mallaka ba..?
Ga mata nan manya masu Hankali acikin Gari sai su yarda Girman ku kuna Biyema yara..!
Sagir yayi Dariya kamar me kafin yace eh sun ji shi ba yarinyar ya aura ba..?Sanda yake makale Murya yana Fadin don Allah Baby in d’an kara suna ina..?
Imran ya Rike baki yana Dariya yace”Sangiru ka zama Dan iska In kara uwar me..?
Sagir na Dariya yace”Koma miye ka sani in kuma kana son na Fada ne to..!
Imran yace”Basai ka Fadama ba kada Kasa Kunnena ya Toshe..Sangiru Allah ya Shirya ka Zama D’an iska har kana san Abunda miji da mata suke yi..
Gabadayamsu Dariya suke yi Sagir yace”Bamu sani ba sai kai Tunda kayi aure .!
Imran yace”Kai dallah..Ni fa bana son Raini sam.Kagani nan ko zan amshi Hakkina umarni zan bada kawai..Allah ya kyauta in zauna ina Wani Rage murya kamar wani Sakarai..!
Sagir yace”Uhm..Lokaci na zuwa..Lokacin da zaka gane Karuwa ba yar iska bace..!
Imran yace”Wlh yar iska ce..!
Sagir yace”A”ah fa Sana”arta take yi kada kace haka..!
Gabadayansu Dariya suke yi Daga Karshe Imu yace Wlh su nemi mai musu Best friend Allah ya kyauta yaje Cikin yara yana Bude baki da Girmansa,da komai.
Sagir yace bakomai sun ji gari da yawa maye ai baya ci kansa ba kuma ko bai zama Best friend ba ai ya Zama Babban yaya..!
Haka ya Kira Khalil yana gayamai Shima cewa yayi ai karamar yarinyar ya aura Daga Wajensa suka koya shiyasa Haka shima yace mai Bazai je Cikin yara yana mgana ba in sun neni manyan mata shikenan yana Tsausaya musu ga kayan Raini ga Dawainiya maimakon Ta Kula Dakai kai ne Zaka koma kana kula da ita Dukkansu sukace mai sun ji kuma sun gani sun gode da Shawara ji ya Zama Dole yadda ne ba Dole ba.
Khalil sai da ya bama Munari Labari batayi mamaki ba Sanin Halin Ya Imu Tace ai ita kanta Inteesar Wahalar sa Take sha Kafin ta Samu Lagonsa sai Ta yi kamar tanayi irin su kana yi ne kamar Baka yi ba irin Mazan da suke Laushi bane lokaci Daya,Ammh Zai yi Laushin In Tafiya Tayi Tafiya In ji Khalil.
Ranar Friday ta kama Zasu yi Second to d the Last Paper dinsu Sai Tafiya Hutun da zasu dawo su shiga Aji Biyu sai karfe 12pm suke da Exam gida Imran ya Barta In Lokaci yayi Zata Kulle Gida ta Hau adaidaita Tatafi makaranta Bata Tambayashi Zuwa Gidan Abba ba sai da ya Tafi Wajen aiki ta Kirashi bai Dauka ba sai ta Turamai Sako Don Allah ya barta Tabi Munari zuwa Gidan Abba.
Daya gani sai ya Shareta Aiki yayi mai yawa sai da ta kara Kiransa Sannan Mganar ta dawomai Sako ya Tura mata Cikin Gatsensa “Bana ce kada ki kara Zuwa ba..?
To ki Tafi din..!
Haka ya Tura mata ita kuma Tana ganin haka sai ta Zata ya barta ne suna gama Jarabawa tace Zata bi Munari zuwa gida Munari tace Ya Imun ya barta ne..?saboda ai aganbansu Abba yace kada su kara zuwa nan kusa Har Imran din yayi Fushi Daman Haka Abba yake so su Dauke Kafa na kwana Biyu su Zauna agidansu su kara Fahintar juna.
Sai Inteeaar tace eh ya barta Munari bata kara mgana suka tafi Abba baya nan yana cikin makaranta sai da ya dawo ya ganta Dayayi mgana Tace Imu yace tazo in ya taso aiki Zai Zo ya Dauketa Abba yayi mamaki yafa san Halin Imu bazai Huce nan kusa ba ammh dai bai ce komai ba.
Har bayan Isha”i Shuru ba Imran ba Dalilinsa kuma a ka”idarsa yana Tashi aiki Hudu zuwa Biyar na yammah in ya Tsaya wani abun ne Shida na yammah Kafin mangariba ya iso ammh Yau shuru Inteesar Tayi ta Kiransa bai Dauka ba sai idonta ya Raina Fata Munari ta Kalleta Tana Fadin”Wai Daman bai barki ba kika Taho..!
Inteesar na ta Fito da Wayarta Tana Dubo Test din da yayi mata ta Nuna ma Munari Tana Fadin”Shifa yace naje kalli ma ki gani..!
Munari ta amsa ta karanta Cikin Mamaki ta kalli Inteesar Tana Fadin”uhm..ni ban ma san me zan ce miki ba..?Kalli fa abunda yace Keji din..?shine kuma kika je din..?Allah ne kadai yasan yadda Kika Batamai rai kila don ma kene Da yau wani ne ko Wata da ya Raina kansa..!
Inteesar Idonta ya Raina Fata Tayi Shuru ta kasa mgana Munari na Kallonta sai ta bata Tsausayi ya Imu naWahalar da Inteesar ta rasa ta yadda Zata gayamata ta gane komai itama Ta Dauki Hanyar Ramawa bata karance karance bata damu davSocial media ba ballatana ta san wasu abubuwan gata kadai ta sani ita Tana Karance karancen Littafan Hausa Dana Turanci Tana kuma Mu”amala da Social media Tafi Inteesar Bude ido sosai kuma ta Fita Shiga Mutane..
Ganin ta Damu yasa Munari taje ta Fadama Abba yadda akayi Abba bai ce komai ba Daman yasan Za”a Rina Ya Yusuf na gefe yana Fadin”Shi yama yi Auran Har yau bai yi Hankali ba..?
Abba ya Daga waya ya Kirashi bai Daga Kiran ba sai da ta Katse kana ya Kira Daga baya Abba bai ma Tsaya amsa Gaisuwarsa ba yafara Fadin”kana ina..?
Imran ya Dakuna Fuska yana Tsaye a Falon gidansa Roban Ruwa Hannunsa Guda Dayan kuma yana Rike da Waya yace”Ina Gida Abba..!
Abbba yace”Ka manta da Matarka ne ka wuce gida baka zo ka Dauketa ba..?
Imran yace”kafar da ya kawota sai ya Maidota Abba..ni ai ban aikota ba..!
Abba yace”Ni kake Fadama haka Imran..?wato Kafarta ta maidota ko..!Nagode..!
Imran yadan Bude ido yana Fadin
“Abba kada ka Dauki mganar nan da Zafi..Ba dakai nake ba..Ni ban ce tazo ba ta Raina ni ne Dole ne sai abunda Take so zan yi akoda yaushe..?nace mata Kada taje bataji mgana ta ba ta Tafi ai tunda ta iya gaban kanta sai ta Dawo da kanta..!
Abba yace”Kayi mata hankali Ita yarinya ce..!
Ran Imran ya kara baci yace”In ita yarinya ne sai ni kuma Shikenan sai na Lalace akanta..?Ni Bata mata Rai zan yi bana son wasa meyasa batajin mgana ne..!
Abba yace”Kayi Hakuri kazo ka Dauketa..Yaushe Zata rika Fahimtar ka kana mata mgana Gatse gatsen ka Kwata Kwata kai Imran baka Laushi..!
Imran yace”Abba nayi Laushi Saboda ita..Bata Samu Compt Imran ba Half Ta samu..kuma na riga na Rantse ni ban Zo na Dauketa ba kuma bata isa ta Sani Kaffara ba..!
Abba ya Bude baki kafin yace”Har nima ko..!
Cikin Dakuna Fuska yace”Ni fa Abba ban ce kai ba..!
Abba ya gyada kai yana Fadin”Ka dinga dai Hakuri kai Babba ne ka Girmeta..Ka Rika Tunawa sai ka Sadda kan ka wani Lokaci ita yarinya ce akwai kuruciya Tare da ita..!
Imu Hade rai aransa yana Fadin Wato ya Sadda kai ya Zama Sakarai Allah ya Tsareshi..!
Abba yace”Yusuf zai kawota..Zan mata Fada kada ka mata wannan Hargagin naka nasan Halinka..!
Imran ok kawai yace ya Katse Kiran Ransa na baci kokarin ma Daidaita kansa yake In yace abu baya so kuma ana Damunsa akai Abba fa da kansa yace kada su dawomai Gida nan kusa Shi mutum ne Dake Daraja Kalaman mutane masu Daraja awajensa Musamman Abba Shi bama da Wata Manufa yace mata kada taje ba ya bari ne sai Abba ya nemesu da kansu suma su Rama bacin Ransa Daya daya Dawo bai ganta ba wato ke je din Taje din Sai Taga abunda zai Faru..!
Abba Fada yayi ma Inteesar Sosai Tayi Narai Narai kana Abba ya Umarci Ya Yusuf Daya maidata Gida Tace Munari Tazota Rakata Munari tace Allah ya Tsareta Ta Rakata Ya Imu ya Hada da ita,Tana ma Rokonta Kada ma a bayaninta ta Kira sunanta
Inteesar dai Tasan yau sai ta sani da Fada Ya Yusuf ya Dauketa ya kaita Gidan ya kulle gidan ta Ciki sai da Ya Yusuf ya Kirasa a waya kana ya Fito ya Bude mata bai Shigo da Motar ba Daganan yayi musu Sallama ya Juya Imran yana wani Cin mgani aransa yace Yau Inteesar ta Zama nama kenan..
Shi ya Tsaya Rufe Gidan ita kuma Tayi Sadaf Sadaf ta Shige Cikin Gidan Tana Kokarin Shiga Dakinta ya Shigo Falon Cikin Dakiyarsa yace”Zo nan..!
Cak ta Tsaya gabanta na Fadi kafin ta Juyo bata iya Dagowa ba kanta na kasa Tana wasa da adon Gyalen dake Jikinta Daga sama Har Kasa ya Kalleta Kafin yace”Sagir bai baki Sako ba..?
Kai ta girgizamai Cikin Dakuna Fuska ya Danna ma Sagir Kira ta Wayar Dake Hannunsa Buga Daya ana Biyu ya Daga Yana Fadin”Ango kasha Kamshi..!
Imran yayi Tsaki yana Fadin”mallan ina Aikin da na baka..?
Sagir yace”Wani aiki kuma da Daddaran nan..?
Imran yace”Hijabin da na baka kudi a Dinkama MARYAM..!
Sagir yace”Au na manta kasan bani ke yi ba Kasuwa nakai Wajen wani abokina yana Dinkasu kala kala bari gobe zan Tabosa naji ko ya gama Hala Baka son Tana saka Mayafi ne..?
Banga Laifinka ba kada Maxa su kalle ma yar babynka..!
Imran Tsaki yaja ya Datse Kiran Yabar Sagir da Dariya Inteesar na Gefe Tana Sauraransa Zama yayi saman Kujera ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Sanye da Riga da Wando Fari da baki.
Kallonta yake yi yana Kokarin Daidaita kansa Cikin Kaushinsa yace”Yaushe kika Fara rainani da Har Zan ce kiyi abu kiki yi..Sai abunda kika ga Dama Zakiyi..?
Yauahe muka Fara wannan Dake..?
Ya Fada Cikin Tsawa da Daga Murya Inteesar da Tuni Idonta ya Ciko da Hawaye ta ce”Kai fa..kai fa kace naje..!
Cikin Hararanta yace”Yaushe nace kije..?cewa nayi ki je din Shine kuma Saboda Tsabar kin Raina ni sai kika je din ko..?
Inteesar na Sosan Idonta tace”Naji to kace naje kuma…!
Ransa ne ya kara baci ya daka Mata Tsawa yana Fadin”Shup up anan Wajen in kika kara mgana Kika Harzukani Zan tashi nayi kasa kasa Dake anan Wajen..!.
Jin haka yasa ta Toshe bakinta da Mayafinta Tana Hawaye bata son Fada a Rayuwarta.
Cikin Fushi yace”Bana so..Bana so..Ina mgana kina mgana Raini ne..Zaki cemin ke bakisan gatse bane..?da zaki kwashi Kafafu ki Tafi..?Kina Biyema wannan yarinyar ko..?munari Daya kuke da ita..?ke fa matar aure ce nan ne gidanki itama Chan ne gidansu Ammh baki da aiki sai Biyemata sai anyi mgana Kice Munari Munari kaza kaza..Munarin Daya kuke da ita nace..?
Yafada Cikim Tsawa ai Sai Inteesar ta Saki kukanta cikin kukan Tace”Ni bansani ba..Wlh bansan Gatse kamin ba..kana ta min Fada..Ni bana son Fada..!
Take Fada kafin ta Shige Daki da Gudu Tana kuka Baki ya Saki yana kallonta Wato ita batasan Fada..?to ya barta ta Cigaba da iskanci kenan bai Mata Fada ba,daya Daga Cikin Illan Auran yara kenan Yanzu in babba ce Taya ya Zaka Xauna ma kana mgana..?ai tasan abunda ya Dace da ita Soyayya batayimai adalci ba Data saka ya Fada soyayyar yarinya karama Datake Neman ta Sauya shi Daga Imran dinsa Zuwa Wani Imran din na Dabam
Yana Jinta Tana kuka yayi banza da ita In bai rika mata haka ba Watarana Da mganarsa Zata Rika ja tana yarda taga Dama Kwanjinsa bai Hana in Anyi ba Daidai ba ya magantu Soyayyat taci kaza kazanta alokacin in Komai ya Dawo Daidai sai a Tuna.
Yana Aiki Bisa Laptop dinsa yaji Har Tana jiniyan kuka kamar Wata karamar Yarinya.
Da Sauri ya Mike Ransa na Baci ya Shiga Dakin afusace kan gado ya ganta ta Dunkule Tana kuka kamar ya Daketa Cikin Fusata yace”Na Dake ki ne..?Kukan Dadi kikeyi kinsan Allah in baki min Shuru anan Wajen ba Na Tako Inda kike sai nayi kwallo Dake Nagani kukan Jini Zaki yanzu ko na Hawaye..!
Ai jin haka yasa Kaji Inteen Daddy Tsit Tasan zai aikata Kyafci yayi ya Fice Daga Dakin Ta rakasa da Harara Damam kukan Tabara ne afili Tace”Ko ma ya Lallasheni ina kuka.!.tafada Tana Tura baki Ranar Bai kara ganinta ba da Safe mahar ya Fita bata Fito ba aransa yace in na Nemeta zata Rainani ne gwara na Kyaleta ai itace Tamin Laifi da Wannan Tunanin ya Fita Batunta mai Dade a Office Dayake asabar ne wani aiki ma ya karisa Daganan Shagon Sagir yaje suka sha Hira bai bar Sagir yayi Salama ba sai da sukaje suka karbo Dinkin Hijaban Inteesar matar mallam Imu ce yadi Hudu Hudu ne Har yana jan kasa Mama Tayi Danwake ya Shiga Har Ciki Suka gaisa suka ci Danwake shida Sagir yana ganin Gidansu yaso kamar ya Shiga sai kuma ya fasa kada Intee taji tace Ita ya Hanata Shiyasa ya Fasa shiga ammh sun Hadu dasu Abba a Masallaci Ya Yusuf nata yimai Tsiyan mai Yaji ya Daka Borkunu Imun Abba..
Bai ce komai ba ya Kara Hade rai kamar an aikomai da Sako mara Dadi a an anguwar yayi sallar Isha”i kafin ya Koma Gida Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba ya Damu Yana so yaji Lafiyarta ya barta itaa kadai agida Tun Safe.
Ya Kirata bata Dauka ba ya Turamata sako.
“Kina lafiya..?.
Ta karanta Ta Sharesa Wata Zuciya Tace ka kama kanka Imran da Girmakka Yarinya na neman janka a kasa da wannan Tunanin ya Fita Batunta ammh fa Tana Ransa Ranar Lahadi ba aiki yana Gida yana Daki yaji Fitowarta da Safe ta Shiga Kitchen yana jin haka ya Fito Falo ya Zauna Saboda yaji kamar Girki take yi Sai da Ta gama ta Fito Dauke da Filet Shake da Indomie,Ko Gaisheshi batayi ba Bakinta agaba ta Shige Daki Dauke da Goran Ruwa ta kasan ido ya Kalleta Dariya ta kamsa afili ya Furta”Imu ka Tabo Autar Daddy sai Allah..!
Kitchen din ya shiga yaga iya Cikinta ta Dafa,Cikinsa ya Shafa ya Lafe sosai yana jin yunwa Inteesar Muguwa ce ko Ta Dafa dashi in bazatayi mai mgana ba ko acikin Kitchen din ta ijiyemai yazo yaci bakomai.
Hakanan ya Dafa Ruwan zafi yasha Tea sama sama ya Dawo Falo Laptop dinsa ya Dauko ya Fara aiki Domin ya Daukemai Hankali.
Ranar haka suka Wuni Inteesar Har Kai take kaudawa bata son kallonsa Imran shima ya Mazaye baya bari Ta gane ya ganta shima ya nuna mata ya Fita Zafin kai.
Washagari Monday Ranar ne Last Paper dinsu,Karfe 10:00am suke da Jarabawan Zai Rigata Fita Shiyasa da Safen ya Taka Har Dakinta tana Kudundune Cikin Bargo ta Rufe ido kamar mai barci batasan ya ganta ba Tana Danna Waya tana jin Sallamarssa Ta Tusa wayar Cikin Bargo Tana Barcin karya.
Bai bi ta kanta ba ya Ijiye mata Ledan Hijaban yana Fadin”Ki yi amfani dasu..Bana son na kara ganinki da Mayafan nan..!
Yafada Lokaci Daya yana Dora mata Dari Biyar saman ledan Ya kama Hanyar Fita yana gyaran Zaman Briefcase din Dake hannunsa.
Yana Fadin”Kiyi maneji ba kudi a Hannuna..!
Daga haka ya Fice ya Turo mata Kofar sai da Ta Tabbatar da ya bar Gidan kana ta Mike Zaune ta jawo Ledan Tana Dubawa ai data Gwada sai da ta Rike baki Tana Fadin”Tabdijam..Ni ce Zan saka wannan kamar wata Malama..!
Tafada Tana kallonta ta Madubi,Wata Zuciyar tace”Kuma ki ki sawa..Abu ya Zama Bala”i..Kila ma wannan karon Har da duka!
Tuna Haka yasa ta bata rai Hijabin kala Goma ne kala kala gashi an yi musu Dinkin Zamani.
Bata bar gidan ba sai ta Soya kwai tasha Da Tea da Buredi wanda sai da ma suna Hanyar dawowa Gida Ranar tagani tace su Tsaya su siya kana ya Tsaya ya siyan musu shi ba ci yake yi ba ballatana Yayi Tunanin siyowa.
Dakyar ta samu Daya daga Cikin Hijaban ta saka Kalan pick Zanen Material din Jikinta Har kasa ya kaimata ya Rufemata Diga digi ya ta iya Matar Imu take in batajin mgana Mganinta Zai yi a Dake ka kuma a hanaka kuka kuma aki Lallashinka sai dai ka gaji kabama kanka Hakuri..!
Lokacin da Munari taganta a makaranta Sai da ta Kusa Kaiwa kasa Saboda Dariya Inteesar sai kwal kwal kuka Cikin Shagwaba tace”Duk ban yi kyau ba ko..?
Ba yaya Imran bane ya kawomin wai kada ya kara ganina da mayafi..!
Munari na Dariya tace”Tab..Mrs Imran Abubakar Malami..!
Take Fada Tana Dariya wayarta ta Fito da ita Tana Fadin”Bari nayi miki Hoto naji Dadin Bama su Nasara Labari..!
Daman Kiris take jira sai ta sakamata kuka ganin haka yasa Munari ta Daina Dariyan afili Sai da Taga Inteesar din Idanuwanta duk sun kumbura alamun tasha kukabata Tambayeta ba sai da suka Fito Paper Course mate din su suna ta Murna Final Suka samu Waje suka Zauna Munari ta kalli Inteesar Dake Fama da Hajibi Tana Fadin”wai ya imun dukan ki yayi ne naga Idanuwanki sun Sauya..?in dai kuwa ya Dakeki Wlh Tashi muje office din Abba ki Fadamai kan me..?aure ai ya wuce wasa..!
Inteesar ta Dago tana kallonta kafin Tace”Wlh bai Taba Dukana ba..!
Munari tace”To me ya yi miki..?daga ganinki kin sha kuka wannan i don naki..!
Inteesar ta kauda kai batayi mgana ba Munari tace”Shikenan Tunda baki san Gayamin ammh Zan Fada miki gaskiya in baki Mike Tsaye ba Wlh Ya Imu Wahala Zai ta baki kafin ki gano kansa Kingama Jigata..!
Inteesar ta Juyo tana kallonta Kafin tace”Uhm..Naga alama..Ranar da naje gidan nan..!.,
Nan ta shiga bama Munari Labarin abunda ya Faru ta Karishe da Fadin”Haka ya dinga min tsawa da Fada ina kuka bai Lallasheni ba yace ma in na kara Damunsa yazo nan sai yayi kwallo Dani..Ni ba ance Miji na Lallashin matarsa ba ni Wlh Ya Imu bai Taba Lallashina ba Munari in ma Fushi zan yi baisan inayi ba sai don in nagaji na Hakura dakaina anya Yana Sona..?
Munari ta gyara Zama anzo Wajen Data ke son zuwa Cikin Hikima tace”Wlh yana sonki..So mai Tsanani ma Daya kai ku wannan Mtsayin in da baya Sonki ko sama da kasa Zasu Hade bazai Aure ki har ya Zauna dake ba Baki ga Sajida da baya sonta ba ya Saketa.ba..?haka Ya Imu yake Dan kafiya Dan Ra”ayi bamai Turasasa yayu abu Dole sai Abba ammh ko shi baya yarda yasakashi ya Zauna da abunda baya Ra”ayi..!
Inteesar ta jinjina kai alamun gamsuwa kafin tace”Ai bai taba Cemin yana sona ba..!
Munari tace”Ai bazai fada ba..Ke ce Zaki Sakashi ya Fada ma bai sani ba..!
Inteesar tace”Ta yaya..?
Munari tace”Baki gane ba..?tsaya ma wai Kun Fara amarcin ne ko kuwa Dai kina nan kina Jiransa..!
Inteesar ta Rausayar da ido Tana Fadin”Bama mu taba fa kwana Daki Daya ba Tunda muka yi aure..!
Munari ta Zare ido Tana Fadin”No Wonder shiyasa bai yi Laushi ba Har yanzu..ke kuma kika yarda..?baki cemai kina jin tsoro ba..!
Imteesar tace”To ya zanyi..?dakinsa yake Shigewa fa sai na Bishi..!?
Munari tace”Sosai ma.irinsu ya Imu sai da Tarko..Ki bisa ki Danamai Tarkon da zai kawo kansa da kansa yana Magiya..!
Inteesar tace”Ta yaya hakan zai Faru..?kamar fa baya son abun ne ni ko irin Romance din nan bamu taba ba..!
Tafada Abun na fitowa Daga Karkashin Ranta Munari tama kasa mgana Inteesar ta Cigaba da Fadin”Ina Fadamiki sirrina ne saboda Ke Kawatace kuma yar”uwata wacce banda kamarki..ki bani Shawaran ya Zanyi..?
Munari tace”Insha Allahu Inteesar Zan baki Shawara kamar yadda Zan bama kaina..!
Nan Munari ta Zauna Tana ta karanta mata Yadda Zatayi da Dubarin mata Inteesar tayi Kasake tana ji kafin tace”Kina ganin…kin fa san Ya Imu..!
Munari tace”Ai shima Mutum ne kamar Kowa kuma Namiji mai Lafiya Wlh karyansa ya Ture Kiran wannan Majalisar Dinkin Duniyan in kuma ya Fara Dandanarta To zai so kullum ya Dinga Ninkaya aciii ina nan Zaune Zamu gani Ya Imu yayi Laushi sai yadda kikayi Dashi..!
Inteesar tace”Allah yar”uwata..!
Munari tace kina wasa ne Dariya sukayi lokaci daya suna Tafawa Inteesar na Fadin”Khalil ya Shiga uku..,!
Munari na Fadib”Ai yama shiga Goma ne..!.
Dariya suka saka gabadayansu sun dan jima acikin makaranta bayan sun gama Sallama da Course mate dinsu suka Tafi Office din Abba suka gaisheshi bayan sun gama shan A.c da Lemo suka Mai Sallama suka Tafi Daga Bakin Get suka Rabu kowacce ta hau adaidaitan da zai kaita inda zata suka Rabu Da Inteesar kan Zata gwada Shawarwarinta.