SARKI HAUSA NOVEL

Cikin sauri ya miƙe tareda nufoni da gudu, banyi aune ba sai jin hannunsa nayi kan wuyana ya mugun shaƙeni kasancewar ina kusada jikin ƙarfen kuma hannunsa na iya fitowa
Ihu ya kurma yana faɗin “mai kikayi min?” Yana girgizani
Da ƙyar aka ɓamɓare hannunsa daga wuyana, sai da na maida numfashi sannan na saki murmushi na dubi securities ɗin nace ku buɗemin ƙofar sannan ku riƙe shi
Hakan suka aiwatar kamar yanda na faɗa, cikin takun isa na shiga ciki tareda ƙuresa da idona
Murmushi na saki sannan nace “daa nayi niyyar wahalar da kai sama da yanda ka wahalar da ni, na so azabtar da kai kwatankwacin azabar da ka ɗanɗana min, amma na fasa!, kasan meyasa?, saboda na tabbata ƙuncin da kake ciki ya isheka ba sai na wahalar da kaina ba” dariya na saki sannan nace “a mighty prince will rot here in underground prison, and the amazing part nan shine kabarinka!!” Na faɗa silently haɗe da sakin killer smile
Prince Yar banda hawaye babu abinda yakeyi
Dariya na ƙyalƙyale da ita sannan nace “looser!!!!!” Na kwaɗa mishi mari sau biyu nace “bazan iya yafe wannan ba!” Sannan na fice nayi gaba
Ina jin ihunsa da securities suka rufe ƙofar with so much pain and resentment
Murmushi na saki nace “serves you right!” Sannan nayi gaba zuciyata wasai
PRINCE YAR POV
Kuka yake wiwi kamar ƙaramin yaro, yasan yayi cuta amma hukuncin nan yayi masa tsauri dayawa
Da girmansa da kuɗinsa da jinin sarauta babbar masarauta kamar ta abu-dhabi da ke yawo a jinin jikinsa amma ace ya ƙare rayuwarsa a haka cikin ƙasƙanci, cikin firzin, firzin ɗin ma ta ƙarƙashin ƙasa wadda ba kowa ya san da zamanta ba bare a kawo masa ɗauki! Kaico!!! Kaicon wannan rayuwa, yana farinciki zai amshi sarauta kwatsam sai mummunan abu yayi masa katanga, katanga ba ta sarautar kawai ba, ta dukkan farincikinsa, katangar da ta raba shi da dukkanin MURADINSA ta raba shi ahalinsa, kaicon! Zuciya wadda itace silar komai, da yayi haƙuri da yanzu ba ya na cikin kwanciyar hankali ba, haƙiƙa wata kalma ta hausawa gaskiya ce, su kan ce “dukkan abinda haƙuri bai ba ka ba, rashinsa ma ba zaya baka ba”, yayi nadama a ranar da bata da amfani, yanzu ina dukiyar tasa, wa zai ce shi ɗin yana da haɗi da masarauta ma bare yace shine wanda ya sa ran zai amshi mulki, ashsha! Ashe haka duniya take, ta kan datse maka jindaɗi batareda ka so ba, ashe akwai abinda dama zai masa katanga da muradinsa, kaico!! Kaicon son zuciya, kuka ya saki tareda durƙushewa yana faɗin “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un”
PRINCE YAMEEN POV
Kwance yake kan gado yana tsiyayar hawaye, zuciyarsa mugun ƙuna take yayinda yake jin kamar kwanaki ƙalilan ne suka yi masa ragowa na cikin rayuwarsa
A hankali S A R K I ya turo ƙofar ɗakinsa bakinsa ɗauke da sallama
Cikin rashin kuzari Prince Yameen ya soma ƙoƙarin tashi bakinsa ɗauke da dull smile
S A R K I ne ya ƙarasa tareda ɗagosa yana faɗin “sannu ɗan uwana!”
Murmushi yayi sannan ya ɗaga masa kai
“Ya kamata fa ka cire wannan damuwar daga ranka, ita cuta ba mutuwa ba ce, akwai masu cutar nan da suka shafe shekaru batareda ta bayyana ba, sukayi rayuwarsu tamkar kowa, cutar ba ita ke kisa da wuri ba Yameen damuwar da kuke ƙagawa ranku ce, nayi tunani ya kamata ka samu kayi aure wataƙila kasamu kwanciyar hankali”
A sanyaye yace “wace zata aureni?, babu wadda zata so ta zauna da ni” ya faɗa ƙwalla na zubo masa
“Akwai! Cikin yaran da kayi hulɗa da su ka zaɓi ɗaya idan tanada irin cutarka sai ku sasanta” cewar SARKI
“Salamat!!!” Ya faɗa sai kuma ya ɗanyi jim yace “amma na koreta!”
“Ai muna da address ɗinta, sai mu bincikota yanzu dai ka dage ka rage damuwa ka dinga cin abinci, komai zaiyi sauƙi ka ji ɗan uwana” cewar SARKI yana tapping ɗinsa
Gyaɗa kai yayi sannan yace “nagode Ya Sydeek, Allah ya biyaka da gidan aljanna” ya faɗa yana share idonsa
SALAMAT POV
Kwance take kan yaloluwar katifarsu tana ta shararar ƙwalla, wa za ta iya fuskanta tace masa tana ɗauke da cutar HIV wadda babu maganinta, tayi danasanin biyewa RUƊIN ZUCIYA yanzu ga shi son abin duniya ya kaita ya baro, dole tayi ta ɓoye cutarta dan ta san muddin ta fito da ita dole kowa zai gujeta
Hawaye ne suka ziraro mata, a hankali tace “Allah na tuba, Allah ka yafe min”
Mahaifiyarta ce ta turo ƙofar hannunta ɗauke da bowl, zama tayi kan katifar tana faɗin “Salamat ni fa na kasa gane kanki, ki ci abinci ba zaki ci ba, sai aukin kuka, ki shirya muje asibiti inaga zai fi”
“A’a Ummi bazani asibiti ba, zan ji sauƙi insha Allah” ta faɗa tana maida hawayen da ke shirin sauko mata
“Salamat kinsan ya kamata muje asibitin nan dan ki samu kiji daɗin jikinki da wuri ki koma aiki, da aikin ki ne kawai muke ci kinsani” cewar mahaifiyarta cikeda damuwa
Wasu hawaye ne masu ɗumi suka zubo mata sannan ta zaro bangles ɗin da Batool ta bata ta miƙa ma uwar tace “Ummi sun koreni, ki saida wannan mu dinga amfani da kuɗin zuwa wani lokaci”
Shiru uwar tayi tareda amsa tayi waje batareda tace uffan ba
“Batool kin taimakeni, Allah ya saka miki da gidan aljanna!” Ta faɗa tana sakin smile. …..
[11/22, 1:45 PM] Muslima????: 89&90
SYDEEK POV
Cikeda ɗaukin ganinta ya tura ƙofar da zata sada shi da parlorn, ganin bata nan ya sanya ya samu waje ya zauna kan sofa yana latsa wayarsa, ya ɗauki lokaci mai tsayi yana latse latse kafin ya miƙe dan ko ɗuriyarta bai ji ba, ƙofar bedroom ɗin da take ya nufa tareda knocking sai dai babu response ya kai kamar minti biyu kafin ya tura ƙofar ya shiga, saurarawa yayi ya ji ko akwai ƙarar ruwa sai yaji nan ma babu alamar mutum
Bathroom ya buɗe sannan ya tura toilet nan ma shiru babu Anitha babu alamarta, cikin tashin hankali ya fara kiran “Anisa!, Anisa!!, Anisa!!!” Amma shiru babu amsa
Parlor ya koma tareda ɗaukar wayarsa ya fara kiran number ta sai dai a kashe take, yana shirin fita idanunsa ya sauka kan wata brown envelope
Ɗauka yayi ya warware sannan ya fara karanta wasiƙar, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sannan yace “na ɗauka wani abun ne ya sameki” ya faɗa yana zama
Tsaki ya ja tareda cewa “wannan yarinya batada kirki, she should have let me know zata tafi”, haka ya ƙare zantukansa kafin ya miƙe ya nufi gida ransa a jagule
PRINCESS ZAIRAH POV
Kwance take kan gado babu komai jikinta sai farin ƙyalle da ta rufe babbar al’aurarta
Wata daga cikin maids ce ta turo ƙofar ɗakin tareda shigowa, cikin sauri ta maida kanta ƙasa tana faɗin “ki gafarceni”
Princess Zairah miƙewa tayi har yadin yana faɗuwa sannan ta nufi maid ɗin tareda kamo hannunta suka dawo gado
Ƙoƙarin fara yi wa maid ɗin kiss tayi, maid ɗin kaucewa tayi tareda faɗin “dan Allah ki bari bana so”
Cikin ɓacin rai Princess Zairah ta fizgota ta fara kiciniyar rabata da kayanta tana faɗin “sai kinyi, Batool ta hure muku kunne ko, toh babu wanda ya isa ya gujemin, ita kanta Batool wallahi sai na kwanta da ita, zamu haɗu da ita ne”
Maid ɗin cikin ƙarfin hali ta fizge sannan ta fice a guje tana kuka
Zairah ma kuka ta saki tana faɗin “meyasa kuke guduna, Batool kece kika ja suka fara juyamin baya, wallahi sai na mallakeki sai kin zama tawa Batool!!!” Ta ƙare tana sakin mugun kuka mai haɗe da shasheka…..
[11/23, 5:54 PM] Muslima????: ???? S A R K I
91-95
week later
ANITHA POV