NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Nuna min abubuwan da ake yayi sannan ya shiga min bayanin da ake ciki.
“A yanzu mun kwaso kwararru a fannin binciken domin a kullum ana Æ™oÆ™arin kutse ga datar kamfanin ne me zaki iya mana”
Shiru nayi, ina kallon shi kafin nace mishi.
“Muje amma kafin nan bari nayi rabu aiki”  gaban kowani ma’aikancin naje na ina duba computers din su, kafin nace musu.
“Ina bukatar laptop nawa na kaina, ina son a bani duk wani bayani nan da awa ashirin da hudu, sannan a hada min internet dina da ta kamfanin nan da kwana uku nake bukatar kome.  Kwana na huÉ—u kuma zamu yi aikin baki daya.”

“Yes Mah” haka suka fada, sai na tsintar kaina nayi yayi wani irin kato.
Sannan muka fita nace mishi.
“Sir cewa suka yi Yes Mah” kallona yayi tare da faÉ—in.
“Yaranta zata motsa ko? Toh wallahi ni ba Bilal bane” tura baki nayi gaba sannan nace mishi.
“Ina kyakyawa na?”
“Zai zo an jima”
“Wayyo da gaske?”
” Da wasa” ya fada min, aikuwa na shiga ihu da murna.
“Kin ga daga yau babu ke babu fita sayowa kowa abinci, za a kawo Miki baki har office din ki, akwai duk abinda kike bukata, karki ce zaki fita kiyiwa wasu hidima, Kema a bar a Miki hidima ne domin kin zama babba anan”
“Woo! Me?” Na nuna kaina ina wani dan rawa cike da shaukin irin na ji dadin nan.
“Kin san ya hanaki shiga harkan maza babu ruwanki da su”
“Toh idan ba shiga cikin maza ba,  me zan yi ba aikin a cikin maza bane ko kai ba namiji bane  gaskiya gaskiya a sauya wannan jadawalin bai min ba” na fada ina wani bata rai.
“Ki kira shi ga wayar ki nan, amma kina bukatar sabuwa”

“Woo duk ni daya?  Gaskiya Nagode”  tafiya ya bar ni, ina ta juyi tare sa mafarkin cigaban da na samu once. Sai dai kuma tun da na fara aiki a department din nan, babu lokaci. Wani sa’in inda nazo karfe bakwai sai karfe tara zan koma gida, nayi wani iri busy da ni kaina nasan bani da lokacin kaina sai na aiki a cikin kwana uku hada mun kome nawa, sannan na shiga kai tsaye kan datar kamfanin.

A yanzu nake da damar na rusa Bilal ko na bare shi ga dukiyar shi da kome a hannuna. Kwanaki talatin da bakwai. Da awa goma sha bakwai yayi yana jinyata a garin london. Ya dauki kome na shi ya bani sabida, sun yarda dani haka mahaifiyar shi da yan uwan shi, ban san lokacin da zan biya shi, idan har na tura wannan al’amarin ga Madam Tola shi ya karye Kenan bayan shi din niman rayuwar shi suke.

   Ya min halacci yanzuh zan biya shi da abinda  yayi min dole na kare hakkin shi da kamfanin shi. Dan haka koda na dawo gida kwana nayi ina aiki har zuwa asuba ba rufe kome na rufe kofar da na bude musu, sannan na saka garkuwa a kowani link da za a tab’a.
Sai da na kwashe kwanaki goma ina sauya kome sannan na dauka na turawa Sir Faisal. Yana gani ya kirani. Office din shi nq shiga bayan na ja kujeran na zauna.
“Sir gani”
“Naga sakon ki”
“Eh na sauya kome na kamfanin domin akwai hannun wasu ma’aikata  a cikin abinda yake faruwa. Sir nasan me ake kira computer da kome nata, nasan yadda ake hada sharri a internet, wadannan abubuwan da na turo sune addanan bayanan kamfanin duk wanda zai tab’a koda wasa ne sai computer din shi ta lalace matukar kutse zai yi akwai virus da ko antiviru aka saka sai sun lakume shi.  Dan haka ka tura mishi amma don Allah kar ka ce ni nayi aikin domin a yadda na gan shi nan ya cika zargi zai iya bina da wani manufa daban”

“Rubi na fahimta, kuma Insha Allah zan mishi bayani kafin nan akwai wani da zan kawo a matsayin shi yayi aikin. Office din ki kuma zan Miki bayanin yadda kome zai tafi”

“Nagode” na ce mishi, sannan na tashi na fita.

    Duk da ba wani zaman office din nake ba, amma kuma babu laifi ina jin dadin yawona da muke da Alman. Wanda muka kulla abotar mu, ko ina a cikin Lagos sai da ya kai ni. Kai ina shan yawon azaba.

    Sau uku ina haduwa da Jamilah, a wani wurin da ban tsammaci haka ba, haka kawai naji ina shakku akan ta, dan haka na share ta dan babu wata alaƙa da zata hadani da ita tunda sama can ba sona take ba.

Ranar wata juma’a Alman ya kai ni gidan Aunty Rahmah, ranar taji dadi domin har kitchen na bita tana aiki ina tayata da hira.
“Baki iya girki bane?”
“Hmm!” Na ce ina murmushin fatar baki.
“Kowani rayuwa yana zuwa da kalubale iya karban shi iya imanin ka, na iya kome amma ban iya ko dafa ruwan zafi ba, nasan xan iya hada wuta na daura tukunya amma ban san yadda ake ya dafa abinci kamar haka ba”

“Ayya kiyi hakuri, na bata miki mood din ki”
“A’a kawai kin san Bature ya ce. DESTINED
Can choose three step for you  in life
1-Love
2-Caring
3-Hatred
No matter how you struggle no matter you reach your Fated.. Dan haka ba wani abu bane kawai kaddarata ce haka”  shiru tayi tana kallona. Idanun ta yana cika da kwalla akalla shekara kusan bakwai ko takwas da autar su yi irin wannan maganar yau gashi ta ji a bakin yarinyar nan.

“Maman Baby lafiya?” Na tambaye ta, Murmushi tai hawaye na zuba mata.
“Babu damuwa”

  Haka muka yi aikin babu walwala, sai dare ya mai da ni gida.

**

Bayan sati Uku
Korea

Wannan shine karo na hudu da ake turo mishi hoton rubi tana gantali idan da tashi aiki. Likita yana shigowa ya Kalle shi kafin ya ce mishi.
“Zamu sallame ka, ka koma gida kayi ta shan magani tunda sun warke” ya fada yana mika mishi wani takardan.

   Cikin farin cikin da bai san yanayi ba,ya kalli Umma da ta amshi takardan. Suka tattara kayan su zuwa gida.

  Tun a hanya yake fadawa Yoona.
“Ka shirya min fly gobe ina son isa lagos”
“Ok Sir”
       Suna isa ya nufi gida bai bi takan kowa ba, ya wuce dakin shi ta haɗa kome sannan ya zauna yana kallon ciwon shi da suke warkewa, lumshe idanun shi yayi yana hangowa hotar Rubih yadda suke yawo da Alman, lashe bakin shi yayi a karo na babu adadi.

    Ko da fito abinci ya ci yana kallon Yoona da yake tsaye.
“Ka gama kome?”
“Eh, amma jirgin sha biyu ne”
“Ok”
“Amma baka samu lafiya ba fa, Bilal” yasan duk lokacin da takira shi Bilal ta kai makura ne a bacin.
“Umma! Kamfani na tana bukata na, idan na bari kome zai lalace lokaci yayi da zan tsaya da kaina”
“Allah ya baka Sa’a ya kuma baka abinda ka fita nima ya kare ka daga sharrin mutum da aljan”

“Amin Ya Allah”

Bayan su wasu awowi, sannan ya bar korea,
**
Lagos

Muna zai staff office,  na department din mu, ya shigo dama yana yawan damuna.
“Rubih duba min laptop dina ban ya akayi na shiga nan ba” haka na cire mishi.
Sannan na mike zan fita ya bi bayana da ido.

     Office dina na shiga na fara abinda take gaba na, d’ago kai nayi tare da kallon agogo,  yau ban ga Yallabai Faisal ba. Tabe baki nayi ina me mai da hankali kan aikina sai ji nayi an burmo min Office.
“Ita ce ma’aikaciyar shi.”
“Lallai ta hadu, dole yayi ta iskanci son ran shi”

Takowa yayi gabana, kallon shi kafin na hade hannuna nayi tagumi.
“Me yasa kika rufe link din kamfanin nan baki É—aya?”
“Kafin nan ma tukun waye kai?”
“Ubanki ne ni, kai fita idan na gama sai ka shigo ka yi kai ma domin na lura sai na ci Uban ta”

  Sosa goshina nayi kafin na taso gaban shi na kai hannuna rigar shi ina balle mishi aninin rigar shi tare da cewa.
“Ka tab’a aure?”
“Uwarki zan aura karuwa” gyara mishi wuyar shi nayi da nickties din shi na matse da karfin Bala’i,
“Kasan me? A duniya ina kaunar cin kwalar rigar mara mutunci! Kafin ka auri Uwata bari na gyara maka kayan ka.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button