NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Kishingida tayi sai lokacin wani irin nannauyar barci ya fara fisgarta, kamar a mafarki taji an dira a cikin gidan, bude idanu tayi tare da kallon kofar dakinta, Yaranta ta fara tunowa.  Tana jin aka nufi dakin Yaranta, tare da jin motsin an bude kofar a tsorace ta mike zubur, wannan wacce irin masifa, ihun Yaran taji da mugun karfi. Dan haka ta shiga kokarin fitowa, tare da bude kofar dakin. Daidai fitowar mutumin ya arta a guje, ya haye katangar gidan ya dirka. Dakin Yaran ta shiga ta same su a dunkule tare da rungume junansu, suna wani irin kuka. Rufe kofar tayi, ta zauna a jikin kofar tana wani irin kuka da yake taso mata tun daga kasar zuciyar ta, tana faɗin.
“Meye na aikata da ake son kashe ni da Rayuwata? Meye na aikata haka da zafi da ba zaa bar ni ba?” Ta fada da mugun karfi kamar ba dare ba. Rarrafawa tayi  gaban Yaran ta suka fada jikin ta, suna k’amk’ame ta.
“Ammin mu, ki dawo cikin mu”

   Rungume su tayi cikin matsanancin kuka, tana kara jin wani irin damuwa kara ninka birni zuciyarta, taya zata zauna tana ganin Yaranta cikin wannan yanayin, rayuwarta bai da amfani matukar bata bawa Yaranta kariya ba, daga dukkan nin sharrin mai sharri.
“Kuzo muje dakina” suka k’amk’ame ta, tana dauke da Rabi’atu, har zuwa dakinta ta, ta rufe kofar ta saka su a gaban kowa sai da yayi alola tare da gabatar da sallah nafillah, har zuwa asuba suna zaune. Kallon su tayi tare da cewa.
“Ku kwanta idan asuba yayi zan tashe ku” da sauri Rahmah da Wasilah suka kwanta.

    Sai Jamilah da Rabi’atu, da take kallon Amminsu.
“Ammin mu, wanda ya shigo gidan nan waye?” Komawa jikin Ammin su Jamilah tayi tare da sake kuka ta ce.
“Ammin mu, yana shigowa suna na ya kira yana nima na” sake k’amk’ame mahaifiyarta tayi cikin kuk, tana cigaba da cewa.
“Ammin mu…..

Ba zan koya Miki zaman aure ba, ba zan koya Miki kwanciyar aure ba, amma alkalamina zai zana Miki yadda ake jure Yanayin Qadra Ni ba gwana bace yar koyo ce… A kullum alkalamina sabunta kanshi yake. Muje akan wata alkaryar domin itace tushen kowacce Æ™addara…300 ne posting sau biyu inshallah ranar juma’a akwai Barka da juma’a asabar da Lahadi sau daya ne Æ™arku manta ni ce Marubuciyar masarautar Jordan, Zanen qaddarata, Matar so,matar Malam, Yar Yadiko, Mrs Amidud, Ruwa biyu, jini yafi ruwa kauri,Kishi a tsakanin zubda jini… Masu karanta books dina sun sanni, sun san alkalamina 😗 chakwakiyya Ce me É—auke da manyan manyan jigo

InshaAllah

Mai_Dambu

EWF

SabonTaku2022

3/1/22, 18:50 – Nuriyyat:    WATA ALKARYAN…!

{THE BEGINNING OF DESTINED}

BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM.
 
      NA
Mai_Dambu
EWF

Albishir ku.. kuce min goro…ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su kyau da rahuwasa… Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci💋💃🏼Http://wa.me/+234 703 003 7697

Hawayen Zuci<2>

Cikin tsananin damuwa ta kuma rungume Yaranta. Tana jin tsoron kar su kuma fuskarta wata damuwar bayan wanda suke ciki.
“Ammin mu!” Daura hannu tayi a bakinta, tare da cewa.
“Ba kowani magana ake amayar da ita ba, domin akwai wanda idan ka amayar da ita wani reshen ce zata kuma karyewa, mu cigaba da Addu’a ko” ta fadi haka ne domin ta dakatar da su abinda zasu fada ko su tambaya wanda tayi imani da Allah da mijinta yana raye babu wanda ya isa shigo musu cikin gidan a daidai wannan lokacin Allah. Lallai ya yarda mutuwa me tonun asiri ce, yau da Alhaji yana raye babu wanda zai ci zarafin su haka. Dan haka ta shiga rarrashin Yaran.

  Har aka yi sallah asuba, tana zaune. Tashin su tayi suka yi sallah bayan sun sake alola, kwanciya suka yi tare da jan babban bargonta ta lullebe su. Sannan ta dawo kan abin sallah, jin ana buga kofar gidan su ne yasa ta mike, akan kunnen Rabi’atu da sauri ta bi bayan ta, suka fita.
“Mama na ba zaki kwanta ba?” Lumshe idanun ta tayi masu É—auke da zarazaran eyelashes masu kyau, sannan ta ware idanun akan Ammin su, tana me murmushi mata, kyawawan haÆ™oranta masu matukar kyau,.suka bayyana akan fuskarta,
“Bana jin barci idan zaki yi Ammin mu sai muyi tare”

    Ya Allah ta furta kasan zuciyarta, tana son Yaranta, but she can’t explain yadda take jin Adawiyya a ruhin ta  kwalla ne ya cika mata kwayar idanu ta, ta isa bakin kofar ta bude sabida jin hayaniyar da ake a kofar gidan su. A hankali ta bude dattawan unguwar ne, dan haka tayi baya kaÉ—an.
“Barkan ku da asuba?” Ta gaishe su,
“Barka da Maman Jamilah, ya karin hakuri? Allah ya jikansa yasa mutuwa hutu ne a gare shi.”
“Amin Ya Allah, Ya kyautata namu bayan su”. Baki daya suka amsa da Amin,
“Dama jiya wajen karfe daya zuwa biyu, mun ji ihun yaran nan. Muka ce lafiya.” Sunkuyar da kai tayi, tana girgiza kai tare da cewa.
“Wani ne da bamu san shi ba, amma Allah ya san shi, ya shiga dakin su Rabi’atu, yana niman Yayar su.”

“Malam liman kaji ba? Kaji abinda ja gaya maka ba. Wallahi sai mun tozarta duk wanda zai bata mana suna a cikin unguwar nan,. jiya jiya aka yi addu’ar bakwai na me gidan fa”  inji wani Dattijo yana maganar a mugun fusace,
“Kuyi hakuri, Insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba,.zan saka su Ammar su Ghali suna kewayawa. Idan kuma kina bukata saka Yan haya tunda gidan akwai manyan dakuna sai na kama dakuna biyu a cikin gidan domin idan akwai namiji a cikin gidan wasu zasu ji shakkar shigo miki, Ammar zai yi aure bawai ban da daki bane, a’a inda yaran zasu samu wanda zai tsaya musu a matsayin wansu ne nake bukata, Ya kuka gani tunda sauran wata biyu bikin shi sai su dawo nan, Ghali ma yana da matar shi, idan suka zama biyu dole motsin su zai rage wasu abubuwan ya kuka gani?”

     “Eh toh yanzun tana cikin kwanakin takaba, mu mata uzuri zuwa nan da ranar da zasu cika kwana arba’in, ko?”  Inji wanda yayi fadar dazun.
“Duk abinda kuka yanke duk daya ne, na baku wuka da nama a hannunku”

“Toh shikenan, Allah yasa a dace. Ubangiji ya kiyaye na gaba”  suka mata addu’oi, sannan suka wuce.
Rufe kofar tayi tana kallon Rabi’atu, “muje a kwanta wannan idanun naki yana bukatar barci.”

Murmushi tayi tare da damke hannun Ammin su. Suka shiga cikin gidan, tare da gyara kwanciyatarsu, Rabi’atu ta shige jikin Ammin su, tana murmushin jin dadi,gata ga Ammin su. Gyara mata kwanciya tayi, suka fara barci. Bude idanu Rabi’atu tayi tana kallon Ammin su, da ta fada sosai, kwalla ne ya cika mata idanu ta.
Sai yaushe Ammin su, zata daina kuka?.
“Kwanta kiyi barci” inji Ammin su, kara shigewa jikin Rabi’atu tayi tare da jin, kamar za a kwace ta a jikin Ammin su. Karfe takwas aka yi da buga musu kofar gidan kamar za a b’alla musu kofar gidan. A matukar firgice suka mike, Rahmah ta fito da sauri ta bude kofar.
“Shegiya! Masu mugun hali, wato shine ba zaku bude mana kofar ba, dan gidan Ubanku ne?”

   Inji Gwaggo Lami da ya shigo cikin gidan, tare da Yaranta mata biyu. Suna bin uwar su kamar wasu shanu.
“Ina munafukar Uwar taku?”
Shiru Rahmah tayi mata, tare da bin bayan su, har cikin gidan, inda suka samu Jamilah da Wasilah a tsaye, suna zare idanu. Shiga cikin dakin suka yi,
“Toh algunguma, na kawo su Beebah da Safinah su miki ta’aziya ne, ashe ana nan da mugun halin nan dai”  bata ce kome ba, kanta a sunkuye, idan tace zata yi magana ma, babu amfanin yin haka, domin su din dangin Yaranta ne.
“Barka da safiya, Gwaggo Lami.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button