NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

    Ta fada tare da mai da kwallar ta cikin idanun ta, tana tuno yadda suka yi da Yan uwanta.
Tunda ba zaki hakura , ki bar musu Yaran kizo mu tafi ba shi kenan amma, ki sani babu ruwan mu da duk abinda ya taso daga gare ki

Lumshe idanun ta tayi tare da kallon su,.tana jin wani abu yana caccakar ruhin ta, ji yake kamar ba zata ja numfashi ba, wani irin abu me nauyi ne ya danne mata zuciya tana ji kamar ba zata iya jan numfashi kirki sai wani irin yake zuwa mata,, a hankali bakinta ya shiga ambaton Allah, tana kiran sunan shi a sanyayye , cikin wani irin kuka ta ce.
“Ya Allah! Kai ne gatan mu, Ya Allah ka gafarta mana laifin mu ka tsaya mana”

         Ta fada cikin matsanancin kuka, a hankali suma yaran suka fara kuka, kallon Yaranta, domin idan tayi dubi da yadda ake rayuwar takaba, ita kowa ma yayi watsi da ita, duk macen da mijinta ya rasu ana niman babbar mace daga cikin dangin mace ko namiji, amma ita danganta sun yi watsi da ita sun tafi sabida wulakancin da Yaya Haliru da Badamasi suka musu, yasa baki daya sun yi zuciya. Dan haka ta share kwalla tare da basu Umarnin su dauki kuɗi ta bawa Rahmah da Wasilah akan su tafi maciya inda ake sayar da kayan miya, su sayo musu kayan miyan da abinda zasu dafa.

   Hijab Rahmah ta saka, itama Wasilah haka suka fita. tare suna rike da hannun junan su, suna tafiya a tare kamar marasa gaskiya, ga Yaran tabarkallah duk inda suka ratsa sai idanun jama’a ya sauka a kan su, sake riÆ™e junan su, suka yi kamar za a dauke su..har suka gama sayayya tare da barin kasuwar..

InshaAllah

Mai_Dambu

TakunFrko2022

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: https://chat.whatsapp.com/GRyYwW2YBaIHOKeYS5ynqs
WATA ALKARYAR…!

{THE BEGINNING OF DESTINED}

BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM.
 
      NA
Mai_Dambu
EWF

Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇🏾💃🏼Http://wa.me/+234 703 003 7697

Kowa Yayi da kyau<3>

Rike hannun Rahmah cikin tsananin tsoro da ganin kamar za a kamasu yasa, su sauri kamar zasu tashi sama, sai da suka kusan shiga unguwar su, suka yi kicibis da Buhari dan gidan Baba Haliru, jikin Rahmah ne ya dauki wani masifaffen rawa, da zaka ce mata kis fitsari zata sake a jikin ta,  d’ago jajjayen idanun shi yayi yana kallonta.
“Ke Yar mace? Tun ba a je ko ina ba har kun fara fita kuna bin maza ne” fisge hannunta  Wasilah tayi zata gaya mishi magana, Rahmah tayi maza ta rike hannunta. Cikin fushi tai gaba abinta, tana ji kamar ta daki Yayarta. Bin bayan Wasilah yayi da sauri tare da saka mata kafa ta fadi, aikuwa zuciya ya kwashe ta, ta dauki dutse ta kwala mishi a goshinsa, sai da ya fashe. Ta kuma tsaya tana kallon shi tarr babu tsoro a ranta. Takawa tayi tare da kura mata ido, yana cizon bakin shi. Tunda yake iskancin shi ba a taba mishi wannan abin ba, murmushi yayi tare da cewa.
“Sai naci Ubanki da wannan Æ™aruwar uwar taku”
“Ba dai Ammin mu ba” tana kara rike da dutse, tabbas idan ya kuma yunkurin zata iya kuma illata shi bai san ta ina zata kuma jifan shi ba, dan haka yayi kwafa tare da tafiya, yana ji a ran shi tabbas sai ya dauki mummunar mataki akan su, musamman ita da take da rashin kunya.. tun a hanya Rahmah da ta gama tsorata ta ce mata.
“Wasilah meye kika aikata? Baki tunanin Baba Haliru yazo ya zagi Ammin mu ne? Ni kam na shiga uku”  Wasilah kan ko a jikinta, sai ma zuciyarta da tayi alamar abin yana sosa mata rai.  Mahaifin sune ya rasu ba zuciyar su ce ta mutu ba, da kowa zai rena musu hankali. Ba zata tab’a sakewa wani ya kuma cutar da su ba, Insha Allah.

Koda suka dawo gida jikin Rahmah a matukar sanyayye, dan haka ta rasa yadda za tayi, ta bude baki zata gayawa Ammin su, sai ga Bana Haliru da Buhari.
“Shigo ka nuna min wacece ta fasa maka goshi?”
Kamar wani sakarai yana shigowa ya nuna Wasilah.
“Yanzun dan Ubanka wannan yar abun ce zata fasa maka goshi? Toh yayi kyau, maza kamata kaci Uwarta.”
Cikin rashin tsoro ta kuma É—aukar wani dutse a tsakar gidan, tana me gyara tsayuwar ta. Sanin bata da hankali zata kuma karta mishi rashin mutunci tare da fasa mishi kai yasa shi ja da baya, wani irin bakin ciki ne ya turnike Baba Haliru, bai san lokacin da ya rufe Buhari da mari ba, yana faÉ—in.
“Dan iska yanzu wannan yarinyar ce zata baka tsoro? Shegen Dan iska lalatacce da sata ne da yanzun ka dauka amma mace yar karama ta razana ka. Fita ka bani wurin” ya juya kan Wasilah da take zare idanu kamar wacce ta hadiye kunama. Jan itacce yayi tare da bin Wasilah da gudu, zai maka mata sai ga matan makotan yan gaba dasu. Sun shigo da sallamar su.

“Shegiya lalatacciyar, tsinanniya jinin Annoba sai na fasa kanki yar banza mara mutunci har kinsan ki fasa kan dan Mutum ya fidda jini yar iska” ya fada cikin matsanancin fushi.
“Kayi hakuri sha’anin Yaran mu sai addu’a, Allah ya ganar da su yi shirye su shiryar addinin musulunci.”inji wata dattijuwa a cikin su.

Kwafa yayi tare da fita daga cikin gidan yana surfawa Ammin su zagi,
“Sannun ku, ku shigo tana cikin dakin,” suka nunawa Mutane dakin Ammin su, suka shiga tare da mata ta’aziya.

“Yanzun Maman Jamilah anya kin san waye Wan mijinki kuwa? Hmmm”inji daya daga cikin matan da suka zo mata ta’aziya,
“Kai Larai bakin ki bai da linzami, Karki daina fada fade sai kin fadi abinda zai daure ki har karshen rayuwarki” kallon tsohuwar tayi kamar zata yi kuka. Kafin ta kalli Ammin tace
“Toh wallahi idan zaki kasa idanun ki akan Yaranki mata ki saka, domin Malam Haliru babu wanda bai san halin shi ba”

“Iyar Dan Asabe ba zaki iya da bakin ki ba ko? Kin zo ta’aziya ko tadda husuma? Tashi mu tafi domin ba zaki jangwalo mana rigima ana zaman lafiya ba, kiyi hakuri Maman Jamilah.” Gyada tayi bata ce musu kome, sai da zasu tafi suka ce mata.
“Allah ya baki hakurin rashin da kuka yi.”
“Amin Ya Allah, Nagode Allah ya bada lada”
“Amin Ya Allah” suka fita da sauri domin sun lura da bakin Larai magana ce a cike dam, dan haka suka jata ba zasu yarda ta ja musu tashin hankali ba. Domin sun san Malam Haliru ba hankali ne da shi ba, dan haka suka yi maza aka fita da ita,.

  Bayan fitar su ne Ammin ta kalle su baki daya,
“Rahmah meye ya faru?”
“Hm, dama dama” ganin zata b’ata mata lokaci yasa ta kalli Wasilah. Murmushi tayi mata tare da bata labarin abinda ya faru. Kura mata ido tayi tana faÉ—in.
“Ai daga yau babu me kuma takura miki na kyale shi sai na dagargaji kan shi, na fasa mishi kai kuma idan ana ganin kina shiru toh wallahi duk wanda ya kuma zagin ki!”

“Allah ya shirya min ku, kul na kuma jin anyi wani abu da ku, wallahi kika kuma fasa kan wani sai na bata miki rai.” Tura baki tayi tana wani mirgina kai kamar an mare ta, nan kuwa fadar ma a cikin sanyin murya tayi mata,amma dan sakalci zaka rantse da Allah maketa tayi nan kuwa babu abinda tayi mata illa faÉ—a.

….
Karshe abincin har dare basu sake ransu, sun ci ba amma Wasilah taci ta koshi. Haka suka wuni da dare a dan tsorace. Da dare Ammin ta rufe kofar gidan tare da saka yaranta a gaba suka wuce dakinta. Domin dama dakin akwai banÉ—aki a cikin dakin dan zaman da yayi da karatun da yayi ya sanya shi sanin wasu abubuwan na rayuwa, shi yasa koda yayi ginin ya fidda kome na zamani ne, amma akwai baranda can gaba kadan falo ne babba sai turakan shi..bayan nan kuma akwai dakuna manyan guda biyar suma da ban dakin su, sai tsakar gida babba da kitchen, da kuma ban dakin tsakar gida, akwai katon zaure da daki a zauren. Shima akwai ban daki yana kallon zauren.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button