NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

    “Rabi’atu bani da lafiya ne?” Mikewa nai tare da zuba hannu a cikin ina murmushin gefen baki. Sannan nace mata.
“Ba sosai ba”
Zan tafi ta kuma rike hannuna.
“Don Allah fa”
Zama na kuma yi a gefen ta tare da rike hannun ta, kina fama da Matsalar  raunin tunani, wanda ya affected din imanin ki. Kin ga nayi cutar Phobia amma kafin nan sai da Abba Musa yayi min jinyar shi, wanda ta kai manta kome. Na sha wahala a hannun Gwaggo Lami, amma daga baya naji sauki ta hanyar samun kulawa daga Maama. Ban sha magani ba amma ba samu farin cikin da ya dace. Ke kuma baki samu treatment din da ya dace ba amma kin samu kulawar da ake bukata, ina kewar Ammyn sosai amma tafi bukatar addu’a sama da kome.

   Idan da zaki mai da hankali akan ganin likita da amfani da shawarar da za a baki, zaki samu lafiya sosai”. Kuka take sosai,  mikewa nayi ba bar wurin ta, fita nayi daga Mansion din ba nufi waje sosai. Inda na samu wani wurin shaÆ™atawa na zauna. Na kifa kaina na fashe da kuka. Kuka nake sosai saboda yanzu nake kukan mutuwar Ammyna, yanzu nake jin wani irin kewar ta.  Nayi kuka kamar raina zai fita tun karfe uku nake wurin sai biyar na tashi. A hankali na koma gida, ina shiga cikin gidan na hango kowa a waje.
“Lafiya?”
“Ina kika je?”  Murmushi nayi tare da cewa.
“Na fita ne, waje”
“Auta kuka kika yi?” Murmushi nayi tare da nufar Umma.
“Ban yi kuka ba.”
“Ai baki iya karya ba,kin yi kuka ga idanun ki ya gaya mana, kiyi hakuri kome yayi farko yana da karshe.”

Suka sani a gaba, tare da kiran Ya Jamilahi, muka sakata a tsakiya ana hira. Idan suna hiran kawai kallon su nake amma baki daya tausayin kaina. Nake, kokarin danne kuka na nake. Ina daukar Deedat na sake wani irin shashekar kuka, tare da rungume Yaron,ina jin kamar na dawo da kome baya, yadda zan gyara kusancina Ammyn.

      Dukkan su, sai da suka yi ta kuka sabida, sunsan dalilin kuka na. Daga ranar da na fita na bar gida ban kuma samun kwanciyar hankali ba, kullum ina gujegujen, ina nan ina can daga karshe na dawo amma babu Mahaifiyar da nayi ta gudun zuwa gare ta.

**
      Kasa magana Irfan yayi yana kallon Bilal.
“Ban san me nayi maka ka tsane ni ba, amma Allah ya gani ina matukar mutunta mahaifiyar ka, duk da nasan  tana abubuwan da basu da ce ba, sannan ina da wani hujjar da zan saka a  kamata amma ban yi ba.  Meye matsalarka da damu?”

   “Ban gane ba?” Irfan ya tambaya yana kallon shi,
“Yanzun zaka gane, hatsarin da aka yi har Surukar Faisal ta rasu akwai hannun ka a cikin hatsarin?”  Wani irin zaro Idanu yayi tare da kallon Bilal.
“Na zata kiyayyar mu iya fatar baki ce ban san ka tsane ni haka ba, bani da saka hannu a cikin hatsarin wallahi”
“Taya zan yarda da kai bayan kai ka fara sanar da asibiti labarin mutuwar Ha Na. Sannan ranar da za a kashe Muneebah kai ne ka kirani.

   Ranar da aka kashe Biyoden kai ka turo min sako, sannan ranar da za a kashe Mahaifina da na Faisal kai ne ka turo min sakon cewa ina kallon ana shirin zubda jini, Irfan Kabir Wazir Meye nufin ka da rayuwata?”

   Ajiyar zuciya Irfan ya sauke tare da kallon Bilal, sannan ya ce mishi.
“Alhaji Kabir Wazir, haifaffen garin Yobe ne, kasancewar shi ya fito daga masarautar Fika, sai ya kasance mutum me matuÆ™ar kyautatta mu’amalar shi ga al’umma.

    Mahaifiyata ba ita bace Hajiya Murja ba, domin ina da yayu da kanne kafin su Suhaima amma sun rasu, ba ina gaya maka haka dan kawai na wanke kaina ba, sai dai zan gaya maka kuskuren da Mahaifina yayi tare mahaifin ka. Mahaifina babban dan siyasa ne kuma dan kasuwa,  mutum ne da a lokacin yana raye gidan mu kamar gidan biki yake, sabida yadda ake yawan zuwa gidan mu, mahaifiyata ta rasu wurin Haihuwa Kanina shima ya rasu.

     Hajiya Shuwa wacce ake kira da Murjanatu, yar kasar Chadi ce.  A yadda Mahaifina ya fara niman aurenta an gaya mishi mutuwar shi zai aura domin su basu cika barin Mazan ba, sukan kashe mazajen su ne sabida dukiya shi kuma ya ki ji ya aurota. Farkon zuwan ta babu Matsalar sai dai kuma wata  biyu da zuwanta gidan babban Yayan mu ya rasu, satin shi biyar wacce take bin shi ta rasu. Mun kasance mu biyar ne har da kanne na biyu,duk sai da suka rasu ya rage ni.

Nima kuma abinda yasa ban mutu ba, sabida kwana na yana gaba, haka na rayu cikin Kadaici da kewar yan uwna, a lokacin ne Hajiya Murjanatu ta fara haihuwa, mace ta haifa.  Tayi bakin ciki sosai, ana haka muka dawo Abuja saboda baban Mu ya samu dan majalisa.
Bayan wasu shekaru sai gashi ta kuma haihuwar mace, kiri kiri ta nuna bata son Yar. Mahaifin mu ya amshi yar hannu bibbiyu. Tun daga nan ta dawo da tunanin ta kaina. Inda tattara duk wani soyayyar duniya ta daura min.

   A hankali al’amuran baban Mu yake gaba, tare da samun cigana na ban mamaki. Ana haka ta fara fita Dubai sayayya, abinda yayi mugun kawo rashin zaman lafiya a tsakaninsu da Babban mu, domin ya ce yana sauke hakkin shi ba zata fara kasuwancin ba. Ranar da ba zan manta ba na dawo makaranta kenan naji tana cewa.
A gama da shi bai da amfani daki na shiga na kasa zama na kasa zaune, muna cikin wannan yanayin aka kawo mana gawan shi.”

Shiru Bilal yayi yana kallon Irfan sannan ya ce mishi.
“Kuma kana ji kana gani an kashe Yan uwanka da mahaifin ku?”
“Toh kamar haka shine lokacin da na yi ta gaya maka magana, a duk haduwar mu, Hajiya Shuwa tana da Kani Hilal shi yake mata aikin kashe kashen da aka yi a cikin Mansion din ka,Hilal shaidani ne domin kamar aljani yake,  ko lokacin da ta hadu da mahaifin ka naso gaya maka kayi a hankali da mahaifin ka amma baka sauraren Ni ba burin ka kawai abinda  yake gaban ka kawai.”

    “Me yasa baka gaya min haka ba?” Bilal ya fada a tsawace.
“Kana taya Mamarka kishi ba zaka yarda ba, kana jin haushi na, ba zaka yarda ba,  ka san yadda Kadaici yake? Ka koma ka tambayi Rabi’ah Meye KaÉ—aitaka?” Ya fada bayan ya Mike.

“Mahaifiyar ka ma ta tsallake rijiya da baya ne amma burin su,su kashe ta. Sannan babu wanda ya kawo Hajiya Shuwa cikin Familyn ku sai Alhaji Abdulkadir Abbas Jikamshi, domin dama can abokan sharholiyar ta ne. Batun hatsarin nan kuwa datsae kiranta aka yi wanda da xaka tambayi Rabi’atu zata iya bincika maka abinda ya faru”

  Shiru Steven yayi kafin ya, bude goran swan ya d’aga kan shi sai da ya shanye tass.
“Ban tab’a ganin wannan irin Family ba, dukkan akan me?”
“Sabida kowa yana son a ce yau shine yake rike da dukiyar Bilal” inji Irfan.

“Meye yasa ka boye alakarka da Nadrah” shiru yayi kafin ya ce mishi.
“Ina sonta, Hajiya Shuwa da Hilal suna son na auri kanwarka, bayan na fahimci Hajiya Turai da Shuwa ba zasu yarda da soyayyar mu ba, ni kuma ba gaji da halin da muke ciki yanzu haka tana da aurena a can inda take karatun har da Yarinyar mu, sannan na cigaba da renawa Hajiya Shuwa hankali, inda take son na auri NaNa idan aka juya a hankali dukiyar ya zai dawo hannuna, sai na damka ga Hajiya Shuwa.  Kai kuma ka auri Suhaima itama a hankali ta haÉ—a kome ta dawo da shikan ta. Sai suka samu matsala daga Shuwa,Turai, Humaida kowacce tana son ka auri Y’arta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button