NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Da wannan suka gina soyayyar su me tsafta,har su Kim Eau suka bar Russia, shima ya had’a kolin shi sai kasar shi ta gado, inda ya dira a garin shi mahaifan shi.  Ya samu ana ta hidimar bikin Abdulkadir anan yake jin labarin ai Adamu ya jima da  aure.  Babu laifi sun fahimci juna da kuma wasu abubuwan su.

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny.
Na
Mai_Dambu
Sara da sassaka<12>

Bai fadawa iyayen shi abinda ya kawo shi ba, sai bayan an gama bikin Abdulkadir ya samu mahaifin shi da zancen, shiru yayi kafin ya ce mishi.
“Ahmad ina tsoron kar su janye min kai ne, amma waye zai ki cigaban. Gashi anan ma Yan uwanka cutar dani suke, dan sun ga bani da mai kula da dabobbina. Shi yasa suke cutar dani, kai da na yarda da kai kuma idan ka bi mace da?”

Tausayin mahaifin su ya cika mishi zuciya dan haka ya tattara batun niman auren shi ya shiga faffutukar rayuwa da iyayen shi, yana kuma niman aiki ganin aikin ba zai fi ce shi ba, kawai ya koma sana’ar mahaifin shi É—aukar shanu da awakai daga arewa zuwa kudu, Alhamdulillahi wannan tafiya tayi albarka, domin kuwa a waye yake babu cuta babu cutarwa. A irin wannan tafiyar ne ya hadu da wani dan Jos,bafaimi ya gaya mishi ya had’a da karo mana ai shima arziki ne, domin ana dauka zuwa kasashen waje ana madubi dashi.

   Ai kuwa ya ji dadi dan haka yayi mishi alkawarin zai fara gwadawa, kasancewar arewa Allah yayi mata dinbun arziki, yana dawowa ya nime Aron kudi a wurin mahaifin shi kasancewar duniya a kwance take kome na da albarka, itama mahaifiyar shi ta sayar da kadarorinta da wanda ta ajiyewa Atikah na aure, aka ba shi, take bawan Allah nan ya shiga Æ™auyukan Katsina har Kano da Jigawa niman karo, Ubangiji yana aiki da abinda yake zuciyarka ne, dan haka abin sai ya hadu ga albarkan Iyaye ga ta Ubangiji sai Allah yayi mishi lidufi ya kuma azurta shi  daga cikin taskar arzikin sa, sai ga Ahmad ya take babban kwangwaro da wata da shanu sai jos, mutumin nan shi ya mishi jagora suka tafi Lagos, cikin ikon Allah aka sayar da karon nan mafi daraja da alkhairi, yana samun haka ya cirewa mutumin Alkhairi me yawan gaske, sannan ya dawo arewa ya shiga aikin niman karo,. Gashi ya maida kudin Iyayen shi ya had’a ribar da uwar kudin aka koma kasuwa.

A cikin wata shida sai ga Ahmad yana cika manyan motoci biyar shida, yan uwan shi abin yana musu ciwo, ganin haka suka addabi rayuwar shi sai ma aka kad’a hankalin shi ya bar gida, ya koma lagos da zama baki daya, a can ya hadu da Abdul Hadi Shema, ya kuma daura mishi amanar iyayen shi,  sosai yake turo musu aika gida amma baki daya yaki dawowa gida, a haka ya tafi har Korea niman auren Kim Eau, tare da goyan bayan mahaifin shi É—an ya tura mishi sako, tare da niman yafiyar shi amma ba zai iya zuwa ba.

Baban Abdul Hadi Shema ne ya mishi uban auren shi a can Korea,. Suka bashi aurenta aka tawo da ita.

Katsina yasa aka kaita wurin iyayen shi, aikuwa ita kanta taji dadin zuwanta, domin ta samu karb’a a hannun surukanta, satinta uku ta koma lagos. A can suka bude babin soyayyar gaskiya

    Haka rayuwa tayi ta tafiya, gashi yana can amma bai fasa turawa ana kwaso dabbobin mahaifin shi ba, ana mai da mishi da kudin shi, shi da kan shi ya fahimci cewa ba haka kawai baya son komawa ga ahalin shi ba, kamar an shiga tsakanin su ne.

Ana cikin haka cutar ajali ya saukowa malam Abbas, Allah Maji rokon bayin shi sa, sai gashi Ahmad ya tafi ya dauko mahaifin shi a nan Lagos ya rasu, lokacin Kim tana da cikin ta na fari. Anan aka mishi jana’izar shi,  suka dawo Katsina aka yi zaman makoki,.kafin bakwai an kwashe rabin dabobbin shi, haka bai damu Ahmad ba, domin an kusan bikin Atikah abun ya faru.

Bayan anyi arba’in ya dauki matar shi ya koma lagos da mahaifiyar shi da kanwar shi, a can aka yi bikin ta. Inda ta auri Abdul Hadi, Ahmad irin mutanen nan  ne da ake kira sana’a goma, baya nan baya nan kuma kowani hanya yasan zai zamu halal yana binta,  ranar da Kim ta haifi danta namiji a ranar Allah ya bashi damar mallakar wata Æ™atuwar fili a ikeja, inda ya shiga gina kamfanin shi tare da Niman yan uwan shi su zo a gina kamfanin tare,  wanda zata na.dauko dabobbin daga sassar kasar tana kawowa su kuma suna kiran dilallai suna saya, sannan ya kuma samu nasaran sayan jirgin ruwa da zata na kai mishi karo har China da Japan.

A haihuwar yaron ya samu budi na fitar hankali, koda Yan uwan shi suka zo suka ga arzikin da yayi aikuwa suka mike kafa tare da cewa ba zasu koma Jikamshi ba, mahaifiyar shi tace Mishi ya nima musu gida haka kuwa ta faru.

Wato idan kana samu gwamnati da kan su, suke niman ka haka ce ta faru, shi kuma ganin zuciyar shi me kyau ana Niman shi kawai sai ya tura Abdulkadir, shi kuma Adamu ya tura shi inda ake mishi lodin zuwa ƙasashen waje.

Ganin suna rarrabe ya sashi gina musu estate baki daya lokacin Ahmad yana da shekara daya a duniya, a lokacin Atikah take goyon Faisal.  Duk da wannan abin da yayi musu. Haka bai saka sun ji a ransu ya kyauta musu ba, asalima gani suke kamar dukiyar mahaifin su ne yake musu wannan bajintar da shi. Dan haka suka ci-gaba da adawa dashi.

    Bayan shekara goma, ana goyon Seyo Na, ya kuma musu magana akan su bude kamfanin kasuwancin dabbobi kamar da gaske aka fara kasuwancin, duk shekara sai su raba ribar, a gefe guda mahaifin Kim ya roki Ahmad ya bashi Bilal, sai da suka yi yarjejeniyar ba zai yi wani addini sai musulunci sannan ta bashi Bilal.

      Dan haka karatun Bilal da kome na shi ya koma korea inda ya taso da sak Ra’ayin kakan shi naso siyasa, sabida yadda yake tafiyar da rayuwar shi da siyasar shi, Bilal ko nace Gong Yoo ya samu halartar Makarantar sakandaren da yake garin Busan, da ya gama ya tafi jami’ar kyung Hee University Korea.inda yá karanta political science, yana gama degree din shi shi ta tafi kasar United State, inda ya tafi yayi karatu akan sociology, inda yayi shakara biyu ya samu babban diploma akan halayyar mutane, kafin ya koma yayi masters din shi anan korea a jami’ar Seoul da yake babban birnin Korea. Baki daya shi da Nijeriya sai Hutu bai ma cika zuwa ba.

     Shekara da ya gama degree na biyu, ya dawo a shekarar babban al’amari ya faru a cikin gidan su, abu na farko da ya faru d’ago maganar auren Alhaji Ahmad da Hajiya Murjanatu wato Shuwa, a lokacin Kim tace ba zata zauna ba domin Seyo tana aji uku na jami’ar lagos, dan haka a kan haka suka samu rashin fahimta har ya kai hawan jinin Yadiko ta tashi, kwanta biyu ta ce ga garin ku, ana cikin wannan yanayin Ahmad ya dage bayan addu’ar bakwai  ya auro shuwa. Ita kuma Kim ta bar mishi gidan da yaranta ta tafi, duk da Hajiya Atikah bata so haka ba, amma babu yadda ta iya, kasancewar Hajiya Shuwa kawa ce ga Hajiya Turai da Humaidah, matar tsohon dan majalisar dattijai ne,. Dan haka tana da yaranta uku, Irfan Kabir Wazir da Zuhairah Kabir Wazir, sai Suhaima Kabir Wazir.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button