NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Dan haka suka riko hannuna,.muna fita daga gidan muna shiga cikin gidan mu, matar yan ta kwashe kafana bugu da bango ji kaje kummmm. Daidai shigowar Steven.

“Chinekee ” ya fada tare da daura hannu akan shi, da gudu ya zo dauke ni sai waje, ya saka ni a motar shi ya nufi asibiti dani.

“Mimmah”
“Masu hakuri suna tare da Allah karki damu, Allah yana tare da ita” ta fada tana me wucewa É—akinta, ta zauna ta sha kuka har ta godewa Allah.

A can asibitin kuwa, sosai suka shiga kokarin ceto rayuwar ta suke, kamar ba zata farfaÉ—o ba, kafin Allah da ikon shi sai gashi ta farka..

**
Lagos
Fitowa da yayi daga ban dakin shi ya saka kayan shi, sannan ya Shirya tsaf ya fito falon shi babu kowa dan haka ya zari key motar shi, dan bai ga wanda zai fita da shi ba, tab’e baki yayi yana mita.

       Har wurin parking lot na nufa sannan ya dauki motar shi, sai gidan Ummin su. Yana shiga ya same ta tare da Madam Hannah murmushi tayi sannan ta ce mata.
“Boss Lady wanda Lu’ulu’un Danki  ne?” Lashe baki Ummi tayi tana kallon Bilal da ya zauna a hankali, yana gaida ta.
“Ummin mu na same ku lafiya?”
“Alhamdulillah” ta fada tana kallon shi kafin ta cigaba da cewa.
“Shi ne Bilal Ahmad Jikamshi, Bilal sunanta Hannah sulee, tazo ne daga Office din Minister Æ™asashen waje, suna son ayi harkan kasuwanci da kamfanin motoccinka”

“Toh Ummi idan dai bai saÉ“a doka ba waye zai ki, ina shaidar saka hannun Me girma ministan?” Mika mishi wata farar takarda suka yi ya gama dubawa, jeren wasu kaloli ne. Kamar haka(1❤️2💛3🟪4â›?5â™?6🔶7☣️8💠9🕉ï¸?10♣️11💭12🔲13💚14) kuma an ce sai kayi choose kafin kayi sign dan haka ya dauki purple number 3.. sannan ya mika mata.

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 33

   Kurawa takardan idanu yayi na wani lokaci kafin ya mika mata yana me ƙoƙarin mikewa.
“Mr Jikamshi ko zamu dan keb’e ne?” Wani irin kallo yayi mata, ya dauke kan shi bai kuma bin ta kanta ba, yayi wucewar shi dinning table, ya fara zuba ruwan zafi. wanda ya ji kayan kamshi sai tashi yake kamar zai cire mishi hancin shi, yana kurb’a yana sauraron hiran su Ummi.

    “Bilal ina dan uwanka ya shiga ne, yasan Yadiko zata zo amma ya kama gaban shi.”
“Ya dan fita ne” ya fada yana kallon tea din gaban shi, a sanin shi dai ya bar gidan shi É—an haka ya fara Æ™oÆ™arin niman shi, sai ga sakon ya shigo. A hankali ya sake murmushi mara sauti.
“Hm”
“Man zan yi tafiya kwana uku inshallah zan dawo*

Share shi yayi tare da juyawa ya kalli Ummi.
“Ummi yayi tafiya ne” ya fada yana yana yankar sakwara da ya sha bugu, a hankali ya fara taunawa.
“Hajiya Atikah Abbas Jikamshi, shin Bilal bai da burin aure ne?” Juyawa tayi ta kalle shi, kafin ta mai da duban ta ga Hanan.
“Yayi har sau uku,matan na mutuwa”
“Ayya Allah sarki” daga haka ta mike, tare da nufar inda yake ta ajiye mishi katin ta.
“Idan kana niman side chick am always wait for you” murmushi yayi bai d’ago ba bai mata magana ba, dan haka ya cigaba da cin abincin bishi. Rakwafowa tayi tana kai fuskar ta tana me sauke wasu irin numfashi ta ce mishi.
“Shirunka yayi yawa,”

“Kumasi mita” ya gaya mata, (wato am sorry da Korea.) Sake baki tayi, a hankali ya janye kujeran yayi gaba abin shi.
“Ummi sai da safe” daga haka bai jira me xata ce ba, ya bar cikin gidan.

      Fita yayi tare da jan motar shi, ya tsaya a waje tana fitowa da motar ta, ya sha gaban ta, bude inda take yayi cikin fusata, amma kuma sai ya shanye fushin sa.
“Wannan ya zama Last warning between me and you, kar na kuma ganin ki a cikin wancan kamilallen gidan”

“Bilal kana min barazana ne?”
“Ina gaya Miki abinda zan aikata, bitch kawai” ya wuce abin shi, a madadin ta ji haushi ji b’acin rai sai ma ta d’aga murya ta ce mishi.
“Tasimita” wani numfashi ya fesar tare da dauke kai ya shiga motar.

  **
Karfe bakwai na dare Faisal ta bar garin Lagos, basu sauka sai karfe biyu na daren can.

       A ya sauka dama tun a gida ya saya ticket din Tokyo, bai bata lokaci ba idan ya tuna Yadda yarinyar nan ta kare mishi kallo sai yaji kamar zai kashe kanshi ya huta, basu wani jima ba, suka bar dubai.

   Anan kan sun dauki lokaci a hanya, kafin suka isa garin Tokyo, dake ya bincika sosai kafin ya tawo, asalima hotel din da suka sauka anan shima ya sauka. Dan haka sai da ya sauke sallah kanshi sannan ya kwanta sai da yayi barci na gudu three hours, kafin ya tashi ya shirya tare da fita a dakin.

    Saukowa yayi ya hangota sun shigo da malaman su,sanye take da unifoam, ganin yadda malamin yake wani shige mata ya bashi haushi, bai san lokacin da ya mike ba, wayar shi ce tai kara ashe ya kira Bilal. Da yaji bai mishi magana ba, shine kawai ya kashe tare da kiran shi. Dauka yayi ya saka a kunnen shi.
“Kai lafiyan ka? Wannan kiran ta Internet din fa?”

“Zan kira ka”
“Kaje daukar fansan kallon maka dick dinka ne?” Ya tambaye shi cikin zolaya.
“Zan zage ka, mara mutunci kamata yayi ki biyo ni na dauki fansa ta, amma dan mugun ta sanun wannan baka min ba”
“Ai jinya kake?”
“A’a Ni ne asibiti banza kawai”
“Ok da fatan a daukar fansan naka babu cin zarafi?” Shiru yayi kawai ganin idan ya cigaba da sauraron shi, zai iya saka shi bakin ciki yasa shi kashe wayar. Ya nufi lefte, yana shiga ya kai shi har inda dakin shi yake, dace da yayi ashe suna kusa da juna ne, domin ya hango tana shiga dakin ta, dan haka ya juya tare da nufar dakin shi. Ya zauna yana kara jinjina kalar mugunta da zai shirya mata, yasan yanzun bata shiga wanka ba, san haka ya juya da sauri ta fita.

Allah sarki Baiwar Allah,bata bi ta wanka ba, dake tana hutun Sallah, kawai rehazal kawai ya shiga yi tana yi tana cin abincin, buga mata kofa aka yi. Teacher Abdullahi. Murmushi yayi mata sannan ya ce mata.
“Gashi Yayanki ya kira”
“Thank you sir” ta amsa tana sakawa a kunnenta, ai kuwa Wasailah tasaka ihu suka shiga murna, aka shiga labarin Tokyo da yadda garin yake, an sha hira har da Jamila da bata son magana itama sai da aka yi da ita balle Ammyn da take ji kamar ta dawo da Rahmah É—in.

  Bayan ta musu sallama ta fita zata, kai mishi wayar shi, har ta buga kofar dakin, ganin tayi kamar mutum ya fito daga dakin gefenta ya shiga nata, a tsora ce ta juya daidai fitowar Teacher Abdullahi ya ce mata.
“Rahmah Ishaq lafiya?”
“Babu kome” ta fada tana mika mishi wayar shi, kamar ba zata shiga ba wani irin tsoro ne ya kamata, dakyar ta shiga dakin tare da rufe kofar. Wani irin kara ta sake tare da rintsa idanun ta, ta ja wani irin numfashi. Alamar ta suma tab’A ta yayi ta tafi kasa.

A hankali ya dauke ta kamar baby ya kaita saman gadonta ya juya yayi fitar shi yana tsaki.

   Bata farka ba sai goshin Asuba, ta bude idanun ta, ganin babu kowa a dakin, yasa ta fara tunanin taya aka yi ta dawo gado, bayan ba a gadon ta ke ba, a hankali abinda ya faru ya dawo kanta, wani irin kuka ne ya zo mata, karshe taki zaman dakin ban daki ta shiga ta zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button