NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

    “Jamilah babu magana ne?” Ya tambaye ta, d’ago kai tayi a karo na biyu ta ce.
“Sannun Yaya” daga haka ta mike daga falon zata koma kitchen.
“Ki dauko min goran ruwan addu’oi nan da kofi”
“Toh”
Ta fada tana me shiga cikin kitchen din ta dauki abinda zata dauka ta fito, ajiye mata tayi, sannan ta koma dakin ta, kamar munafuka bata son zama a inda Yake tayi ta kokarin kaucewa kenan bata son zama inda yake gudun kar yayi mata magana. Tun bai fahimci haka ba, har ta ya gane gudun shi take, shi yasa shima ya dauke kai a kanta. Domin kar abin ya zama kiyayya.

   Mika mishi ruwan addu’a tayi tana kallon shi.
“Ka sha da bismillah”  babu musu ya amsa, ya sha sannan ta daura mishi da nasiha. Da nuna mishi girman addu’a a rayuwar shi.

Bayan ya sha, ta shiga tambayar shi yaushe zai koma bakin aikin shi.
“Baka ce min kome ba?”
“Ammyn duk lokacin da kika ga ya dace, zan koma.”
“Toh Allah yasa mu dace!”

“Amin Ya Allah” ya fada tare da mikewa yayi mata sallama,
*
Lagos Police headquarter.

Tun kafin ya shiga Wasu yan sanda guda biyu, suka tare shi da files guda biyu, suna fada mishi yadda suka samu nasarar cafke shi.
“Sir Kamar yadda muka gaya maka, an rigada an yi connect din Number Boss Lady da hukumar Yan sanda, a duk lokacin da za’a farmake ta toh muna an kare da ita, so gashi nan mun kama shi, Ita kuma Layinah tana cikin office”

       Gyada kai yayi tare da nufar cikin office din, kallon mutumin yayi, bai san shi ba amma yayi mamakin yadda ya iya samun zarrar sace Layinah, duk da ba wani abu suke nima ba, amma ya sha mamaki kallon shi yayi, har ya wuce sai kuma ya dawo yana kallon shi.
“Kamar Salis ko?” Sunkuyar,
“Yallabai ka sanshi ne?” Cike da mamaki ya kuma kallon shi. Kafin ta ce musu.
“Na san shi mana, shi yake goge dakin taron JF Groups”  ya fada yana mamaki tare da nuna shi, y gama shiga mamaki.
“Karka damu, indai mutanen yanzu ne zasu yi abinda ya fi haka domin kowa ya saura aniyar yin arziki kota halin k’ak’a.”

   Sun shiga office din commission of Police, Layinah tana ganin shi ta mike tare da fashewa da kuka, tana me fadawa jikin shi.
“Baresta ga wannan copy din a hannun shi muka samu, sannan yana da muhimmanci a karfaffa tsaro a cikin JF Company domin akwai demons a cikin wurin idan aka ci za a musu rikon sakainar kashin ba zai haifar da D’a me ido ba, sannan gata a tambayoyin da aka mata tace ba shi ya sace ta ba, kusan gata nan.”

“Layinah Baby gaya min Meye ya faru?” Ya tambaye ta a rude,
“Wanda ya kama ni, ba Salis bane asalima na farka naga shima yana kwance, sannan ba zan iya tuna kome ba domin ko magana zai yi da wani irin sauti yake ba salis bane”

“Baresta sanin cewa muna bindigin layin shine yasa ya turo wancan
Criticism amma Insha Allah zamu nime wanda yake wannan abin” inji commission of Police.
“Ok Nagode sosai”

   Har zai fita sai ya juya tare da cewa.
“Tunda zargi ake me zai hana a sake shi ya tafi”
“Amma baka ganin haka kamar akwai kuskure?” Kwamishina ya tambaye shi,
“Babu kome a sake shi ya tafi, amma zamu yi fired din shi a kamfanin mu.”
“Ok Babu damuwa”

  Daga haka ya fita yana sauke ajiyar zuciya,
“Ya Faisal me yasa aka sake shi?”
“Sabida ya ban tausayi”
“Ba zai kuma dawowa ba?”
“Ba zai dawo ba”

    Yana isa gida ya ajiye ta, tare da magana akan security da aka basu na musamman, domin kare lafiyar su da Rayuwar su, duk da Allah ne me karewa amma al’amarin mutum da ban tsoro yake.

  Bai gayawa Bilal abinda ya faru ba, amma tabbas suna cikin damuwa, domin kuwa bai tab’a zata matsayi da aka bawa mahaifiyar su zai tab’a darajar su ba, ita kanta Ummin bata san abinda yake faruwa ba. Amma tabbas akwai Æ™atuwar matsala da zata iya hana su sakat, idan ya duba yadda abinda ya faru.

  **
Deeper life orphanage.

Maganar gaskiya gidan marayu ne a idanun duniya da jama’a, amma ta bayan fage sayar da yaran suke, ga ma’auratan da basu da Yaran mata, suna Adopt din Yara ake tare da tura su akan marayu, sannan yaran da suke wurin mafi akasarin su ba marayu bane, wasu sace su ake kamar Yadda aka dauko Rabi’ah, sannan idan har aka bada kai inda suka saye ka, babu kai babu wurin su har abada, domin da zaran ka koma za a iya kashe ka domin da zaran sun fahimci an fara gano su, zasu dauki yaran su kai su kudancin Nigeria, a can kuma suke bada su ga kowa idan babu ruwan su haka ma idan aka kashe yaro  babu wani bin kadin shi. Akwai kananun Yara daga shekara daya zuwa biyar, akwai yan shekara Tara zuwa Goma. Sai dai wani abinda zai burgeka babu tsana babu tsangwama, asalima suna biyar da Yaran ta yadda zasu manta iyayen su.

Matar da ta duba bata sosai, kafin ta mikawa Hukumar cikin gidan, sannan a yadda ta fahimta, ta lura da cewa Rabi’ah musulma ce, dan haka bata boye musu ba, domin aikin su ne a juyar da Musulmi zuwa Kirista babu wahala. Kuma a yadda suke kyautatta mu’amalar su da Yaran da wasu abubuwan da suke basu yasa ko sunan Iyayen su da nasu sun manta, dan haka Rabi’ah ta samu sunan ta daga yadda suka fahimci yanayin ta, domin.suna da wasu irin Pirate da suke duba future din Yaro, lokacin da aka kawo. Rabi’ah sai da ya dafa goshinta, ya jima yana addu’oi kafin ya bude yana kallon su.

“Ba zata cigaba da zama a cikin mu ba, dole zata tafi domin fuskarta Æ™addaran ta, amma akwai lokacin da kome zai kuma juyowa, dan haka ku bada ita ta tafi duk lokacin da bukatar haka ya taso” shi yasa suke ta addu’a Allah ya kawo masu bukatar Yara, su dauke ta.

    Yau sai gashi daga babban church na kasa wato Ecwa an zo niman Ya mace, Mss Folina ta kalli Yaran ta ce musu.

Suna zaune an basu abinci suna zaune sai da aka gama addu’a, sannan suka fara cin abincin. Dake katon hall ne kamar na makarantar bording. Shigowar wasu ma’aurata guda biyu, da wasu mace daya sanye da unifoam na gidan marayun, suka shigo cikin hall É—in.

“Barka dai Yara! Sannun ku ko? Rebecca zu ga Mr and Mrs Uchanna Jeshua zasu tafi dake sabon gida ai na gaya muku zaku sami sabon Family ko?” Gyada mata kai Rabi’ah tayi, tare da mikewa daga abincin.
“Tayi muku? Tana da gashi sosai, sannan tana da nutsuwa bata da yawan hayaniya”

Mrs Uchanna Jeshua ta kalli Mss Folina ta ce mata.
“Amma yanayin ta kamar Fulani girl bana son a samu matsala ne domin sun iya gane jinin su”

“Kai haba babu wannan zancen tsinto mana ita akayi kuma babu abinda zai faru ku tafi da ita nayi muku alkawarin haka” inji mss Folina,

Duk da Mrs Uchanna Jeshua bata so haka ba, amma babu yadda ta iya haka kawai take kallon yarinya kamar matsala ce a gare su, dan haka Mss Folina ta shiga dakin Yaran ta hana mata kaya, ganin yadda Rabi’ah take Zubawa hawaye yasa ta rungume ta,
“Kina kewar mu ne?” Gyada kai tayi, tana kara rungume matar a ranta tana jin wani irin yanayi na daban, kafin ta sake matar ta fita.

Har wurin motar mutanen suka nufa, 
“Mrs Jeshua ga Rebecca nan, ina rokon ki da ruhi me tsarki karki bari wani abu ya cutar da ita, bata san kowa ba sai ke bata san kowa ba sai ku yarinya ce karama ba zata wuce Shekara goma ba zuwa sha daya,. Don Allah a kula da ita ku bani number ku zan kira ku.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button