NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

    Saka hannu Hajiya Shuwa tayi a  jakarta ta dauko Wayarta ta danna wasu number. Kafin ta saka a kunnen ta tana faɗin.
“Son kana Ina? Ka kula fa, domin an kashe matar Bilal Ahmad Jikamshi.” Ta fada tare da kashe Wayarta, mikewa tayi bayan ta maida wayar jakarta.

       Murmushi tayi sannan ta ce.
“Alhaji Adamu Abbas Jikamshi, ina da goyan bayan masu hannun jari JF Groups, dan haka ka ajiye niman muÆ™amin Chairman, mu daidaita kan mu da sauran Yan uwanka, tunda Alhaji Abdulkadir Abbas Jikamshi ya cire kan shi.”  Murmushi ya sake irinta manyan, sannan ya mike a hankali, ya kalle ta yana faÉ—in.
“Kin san kunne na yana ciwo, ba kasafai nake jin kome ba! Nasan ance matar wancan kafirin ta mutu, so that mu ajiye niman muÆ™amin zuwa nan gaba”

    Daga ya mike tare da kallon sauran yan uwan shi. Musamman matan nan biyu Humaidah Abbas Jikamshi Mrs Muhammad Alfah sai Hajiya Turai Abbas Jikamshi Mrs Ali Ruma.
“Turai da Humaidah kuzo muje” tasowa Abubakar Abbas Jikamshi yayi  tare da cewa.
“Kun ga ku zauna ayi  magana daya, akwai wani karamin aiki da na sama mana, amma dole sai mun had’e kan mu, sai dai akwai kasada, amma kuma hmm” ya gyara zaman shi yana kallon su. Zama Alhaji Adamu Abbas Jikamshi yayi yana kallon shi. Fito da wasu takardun yayi sannan ya mika musu copy din shi kowannen su,sannan ya ce musu.
“Sabida tsaro mu hadu bayan mun dawo daga Busan”

    A hankali Alhaji Adamu Abbas Jikamshi ya mike tare da ajiye musu takardan.
“I can do anything for money but bana din zan iya rusa al’umma, dan haka kuka kuskura kuka sake ya shiga cikin al’amarin kamfanin mu sai na turawa Gong Yoo ya san abinda yake faruwa.”

Daga haka ya mike, cikin fushi Alhaji Abubakar ya sha gaban shi.
“Kana nufin zamu kyale ne ka sha? Bayan kasan sirrin mu da shirin mu! Tabbas kayi kuskure ka tafi idan zaka kai labari”

   Dariya Alhaji Adamu yayi tare da kallon shi sannan ya ce.
“Abubakar Abbas Jikamshi, ka manta kowannen mu yana da weakpoint din shine, Ina da labarin yau Iqbal zai taso daga Honkok, kuma Inayat tana Abuja ko? Ga dan karamin yaron nan da baya magana,me kake tunanin zai faru?”

    Tabbas yasan Alhaji Adamu Yayan su ne, amma bai tab’a zatan ya wuce karamin tantiri ba, ya manta da cewa kowa yana boye mugun halin shi ne dan a zauna lafiya, idan ka ce zaka fito da mugun halin ka TOH ba makawa zaka iya illata kanka bama wani na jikin ka ba. Kallon shi yayi tare da cewa.
“Kayi hakuri!” Jikin shi yana rawa, tabbas bai zaci haka ba, dan haka ya bashi hanya. Dafa kafadar Abubakar yayi tare da cewa.
“A duniyar nan kowa mugun kan shine,amma baka iya cewa waye tantirin, kana koyan tsageranci ne domin kare kanka da kuma na kusa da kai.”

Daga haka ya rab’a gefen shi ya wuce yana murmushi, Hajiya Turai da Humaidah da Hajiya Shuwa kallon su. Kallon shi suka yi tare da cewa.
“Lafiya kake gini haka?”

“Wallahi kowa ya nutsu kar ku ce zaku iya cutar da junan mu, duk da bani da hannu a mutuwar Matar Gong Yoo, amma ina shakku akan kowa domin ba yau aka fara kashe matan shi ba.”

   Shiru suka yi tare da kallon shi, kafin kuma kowanne su ya mike tare da barin takardan a wurin, tabbas tayin da ya kawo musu babban akafi ne, kuma idan har suka saka hannu da kome a kai wuyanta Gong Yoo ya saka hannu shi kenan. Magana ya kare.

   Daga haka kowa yayi tafiyar shi, ya tattara kayan shi ya tafi, sai dai kuma garin sauri ya manta da foam guda daya,  wanda za a ce sauri ya haifi nawa, domin yana fita wani na shigowa, ɗaukar takardan yayi yana kallon shi.

  **
Ikoyi streets

JF Hospital.

   Jerin gwanon motar Barista Faisal Abdul Hadi Shema ne,  suna shiga asibitin securityn da suke bin motar suka fita da sauri aka bude mishi, mikar da hannun shi yayi a hankali, ya gyara zaman Italian suiter din shi yayi  grey colour, gyara zaman madubin fuskar shi yayi yana kallon mutanen da suka nutsu kuwa ya nutsu sosai, wayar shi ya ɗauka. Ya nufi cikin asibitin da sassarfa yana jan hancin shi.

   Kai tsaye ya nufi office din Babban likitan Dr Namir Adamu Abbas Jikamshi, yana shiga ya same shi yana waya, kallon juna suka yi na few seconds kafin escort din Barista Faisal Abdul Hadi Shema ya ja mishi kujera ya zauna, yana kallon shi tar. Shima kuma Dr Namir Adamu Abbas Jikamshi waya yake.

“Ok Dad Babu damuwa sun zo daukar gasar ma” ya kashe wayar shi yana kallon Faisal.
“Uban yan shishigi! Kace kai zaka tsayawa gawan har Busan”

         Wani irin daura kafa daya akan daya, tare da kai hannun habbar shi ya dunkule tare da daura kan shi akan hannun shi, fuskar shi kunshe da murmushi. Mikewa tsaye Dr Namir Adamu Abbas Jikamshi yayi, jikin shi yana bari ya  shiga danna wayar telephone irin na da can.
“Hello ku gama kome akan lokaci ku kawo har da binciken a kawo yanzun nan, ana jiran shi.”

Kasa zama yayi bayan ya gama wayar sai da Faisal ya zare madubi a idanun shi ya ce mishi.
“Zaka iya zama” babu musu ya zauna jikin shi yana kerma.

“Wannan rawan da jikin ka yake bafa Bilal Ahmad Jikamshi bane, ai ashe kun kafirta shi toh ba Gong Yoo bane, Faisal Abdul Hadi Shema, hmm idan har SAN irina zai girgiza hantar ka, Ina kuma idan shine a nan fa?”

Shigowar nurse dauke da wasu documents ta ajiye mishi a gaban shi, ta juya zata fita ya ce mata.
“Tsaya ki kai su mutuary”
“Ok Dr Namir” kallon Faisal yayi tare da cewa.
“An gama Shema”
Mikewa yayi yana faÉ—in.
“Ka kiyayyi me nima” daga haka ya juya yana me barin office din, zama Dr Namir yayi yana ajiyar zuciya, Faisal kenan ina kuma Bilal da kan shi? Ya tambayi kan shi yana ajiyar zuciya, a hankali ya janyo wani lock ya kalli wani red file, ciro shi yayi yana kallon file din cikin sanyin jiki, yasan wannan file ya fada hannun Jikamshi tabbas sunan kowa sorry, ya rasa waye zai bawa File din q cikin mutane shida nan, Mahaifin shi zai bawa ko Hajiya Atikah ko Alhaji Abubakar, ko Ambassador Abdulkadir, Hajiya Humaidah zai bawa ko Hajiya Shuwa, hajiya Turai zai bawa ko Mr Jikamshi da kan shi. Bude lock yayi ya wurga file din yana ma dafe kanshi tare da jan iskar bakin shi wannan bala’in cikin Familyn Jikamshi ya isa ya kashe mutum kwanan shi bai kare ba.

Tashi yayi da sauri ya fita daga Office din , ya nufi Faisal yana kallon su aka fito da gawarwakin wato ita da danta. Abin tausayi aka wuce da su.
“Hello Gong Yoo, ga gawar nan na Turo maka hoton su, so yanzun zamu biyo private jet din mu tawo i hope ka isa?”
Kashe wayar yayi yana kallon Namir. Da bakin shi yake rawa ya ce mishi.
“Faisal yaushe za’a dakatar da wannan yanayin? A kullum kara tsorata nake, don Allah ka cewa Bilal a dakatar da wannan zubda jini, idan ma da hali ya hakura da aure.”

           Murmushi yayi sannan ya wuce abinshi yana me manna madubin shi a idanun shi, har ya kusan fita daga asibitin ya juya a hankali ya koma wurin Dr Namir.
“Karka damu, ka saka idanu, zaka sha kallo inda Ranka”

Daga haka ya saka kai ya fita yana murmushi, motar É—aukar gawa aka kawo, da akwatin gawa aka sakata a hankali tare da danta a gefenta suka rufe, suka nufi airport inda ake jiran su..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button