NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

   Mika min tayi na zauna na cinye har da roman shi, kafin ta dauko ruwan sanyi tana zaune ta shiga wanke wani farin allo tana faɗin.
“Da izinin Ubangiji yadda kika ga Jarabawa a rayuwarki sai kin ga ribar hakurin da kika yi, karni yarda kiyi fushi da rayuwa,miji kuwa da yardan Allah naki ne babu macen da zata aha gabanki. Sha maza Allah yayi miki albarka ba bawa Yayarki nata, haka na shanye tass, sannan ta kwaba lalle da kurku ta shiga goge min jiki da shi tana goge kwallar da yake zuba mata. Haka tai ta goge ni da shi.

  Wajen karfe daya ta ce na tashi, gashi na gaji ina jin barci, haka ta kuma dauko gaushin ta bani na rufu da shi,  ina kaiwa adadin da take so da saka na tashi na murje jikina.  Na zata barci zan yi kawai baiwar Allah nan ta dauko Sugar da lemon tsami ta shiga goge min jikina, haka ta gama min shi sannan ta ce min.
“Kwanta ki huta”
“Toh” ina kwanciya barci yayi gaba dani, wajen karfe biyar na Asuba tashe ni, kwalla ne ya cika min ido.

     Wanka na tashi nayi tare da gyara wasu kayan gyaran jiki da sabulu me shegen kamshi, ina fitowa ta kuma bani wani mai me shegen kamshi sa dadi, na shafa sai kolacha, humra kome na gyaran jiki sosai matar ta bani haka ma ta kaiwa wasilah ta ce wai ai ita wasilah ta ruka, nice nake bukatar gyaran jiki.  Biki aka yi sosai sai karfe biyu muka bar DaÆ™ayyawa zuwa Jigawa, mutumina yana nan yana jirana. Kasa hakuri yayi yana gani na ya shiga d’age min gira.

     Daga nan muka wuce Jama’are, nan ma wani bikin aka yi me daukar hankali. An sha biki sosai.

  Washi gari Monday.

Tun asuba muka bar Bauchi zuwa jigawa, sannan aka É—auki hanyar Lagos a jirgin sama, duk wannan bidirin da ake wasilah kadai ke yin nata, saboda Alman bai da lafiya sosai, shi yasa suke ta kome a tare da Faisal.

   Kasancewar ni ba a Lagos zan zauna ba, domin ya bar kamfanin shi da kome na shi a hannun Bilal da Alman,  muna isa anan aka wuce da wasilah gidan Alman, ni kuma Umma ta saka ni a daki domin jirgin dare zamu bi zuwa Korea. Koda muka hadu da Ya Jamilah tayi laushi kamar ba ita ba, na same ta suna aiki da Ummyn shiga kitchen nayi. Ummyn ta ce,
“Bilal yana hanya da malamin da zai kara biya miki kalmar shahada”
Gyada kai nayi ina kallon kasa.
“Auta?”
“Na’am!”
“Ki yafe min” murmushin yake nayi ina kallon kasa.
“Ya wuce”
“Kice kin yafe don Allah”
“Na yafe miki” na fada tare da juyawa na dawo dakin da Umma take, na koma can gefe na zauna.
Shigowa yayi tare da kallona.
“Saka hijab kizo”
“Bani da shi” na fada a sanyayye,
Fita yayi sai gashi da wani farin yadin dan aba, yadin yayi min kyau, ina sakawa ya sake murmushi sannan ya riko hannuna, muka fita zuwa wurin Malamin.

Zama nayi a kasa, shima ya yiwa malamin bayanin kome.
“Zaki sauya suna ne?” Girgiza kai nayi ina faÉ—in.
“Ina son Rabi’atu Adawiyya na”
“Alhamdulillahi, babu matsala shahadar zaki kuma biyawa”

Nan ya biya min na karba nayi, sannan ya min nasiha akan niman ilimin addini. Koda ya tafi komawa dakin Umma nayi, sannan na zauna shima shigowa yayi ya zauna yana kallona.
“Idan muka tafi sai ki duba idan zaki yi karatu anan ne toh, idan muka zan kai ki Jami’ar mata dake ganin Dayyifa ne toh wane kika gani?”
“Duk wanda kaga ya dace ka bani zan amsa, sai dai karatu a wata kasa akwai takurawa, kawai ka bar ni a korea, sai na mai da hankali akan karatun dukkan biyu. Tunda yanzun an cigaba zaka iya karatu daga dakin ka ma” matsowa yayi na matsa da baya ina me cewa.
“Akwai Umma”
“Eh tasan ina nan ai, bazata shigo ba” ya fada yana kallon fuskana, ture shi nayi na koma gefe, haka muka shiga zagaye dakin, kafin ya kama ni tare da hadani da bango, kai Jama’a mutumin nan dan duniya ne, domin baki daya sai da ya hanani nutsuwa ya birkita min lissafi, sannan ya damke kirjina kamar zai tsinke min su. Buga kofar Umma tayi ya gyara murya, ya fita yana huci. Sannan ta shigo ganin yadda nake É—aukar hijab dina yasa tayi kamar bata ga abinda nake ba, ina gamawa na zauna a wurin.


Wasilah gidanta tare da su taimakawan Ya Rahmah da Seyo Na, suka gyara ko ina dama ta sami su Liyanah da Lubna, suna tare da Alman ne sabida yanayin jikin shi, dake yana barci har suka gama abinci  sannan suka bar gidan kallon dakin shi tayi, gabanta yana faduwa. A hankali hankali ta fara takawa har kofar shi sannan ta murda kofar, budewa yayi ta hango gadon baya nan,  gyara gadon ta fara sosai tana tattara dakin baki daya. Tana gyara kayan daman mirror din dakin. Kamar ance ta d’ago kai tayi ido biyu da shi yana tsaye a bakin kofar ban dakin daure da towel, sau daya ya Kalle ta bai kuma kara na biyu ba.tana tsaye a wurin kamar gunki har ya tawo ya dauki man shafawan shi ya shafa, sannan ya koma ya nufi wata kofa ya bude closet din shi da dankare da kaya, tari ya fara. Komawa yayi da baya ya jingina da kofar closet din, ganin haka tayi maza tazo tana cewa.
“Sannun zauna bari na dauko mata kayan wani iri zaka saka?”

   Kallon ta yayi sannan ya kauda kan shi ya ce mata.
“Akwai kayan army ki dauki min. Rigar Armless ne sai 3qter.” Da sauri ta shiga ta fara dauki wandon ta kawo  mishi, sannan ta koma ta dauko kishi rigar. Kallon shi tayi sannan ta ce mishi..
” Ka saka !”
“Bani da karfi” a hankali ta isa gaban shi, ta taimaka mishi ya saka rigar. Wurin saka wandon ne ya rikice mishi. Kallon yadda take matukar tsorace da shi yasa shi murmushi sannan ya rike hannunta, yaja wandon sama, sannan ya sake ta ya daure k’ugun.

       Bata kalle shi ba har ya gama, riko hannun ta yayi suka zauna a wurin, cikin shiru babu magana. Har aka kira sallah, a tare suka yi sannan ya koma ya kwanta.
“Na kawo maka abinci?”
“A’a! Ki duba kitchen akwai fruit ki min wani abu zan sha shi”
“Toh” ta fada sannan ta nufi kitchen zama yayi yana jiran ta, har wurin minti talatin, sannan ta kawo mishi. Tashi yayi zaune ya fara cin fruit din da ya markadu. Ta zuba madara a cikin shi sai ice cube ta zuwa yayi kyau kuwa, haka yayi ta sha yana kallon ta, bayan ya gama ya koma zai kwanta, da sauri ta tashi ta saka mishi pillow a baya tana faÉ—in.
“Karka kwanta, bari ya sauka kar ya zama maka ciwo” haka ya zauna yana kunshe idanun shi, itama fita tayi zuwa dakin da aka sakata, tayi wanka ta gyara jikin ta, sannan ta fito falon ta samu ya fito. Yana kallo wucewa kitchen tayi abincin da suka yi da zubo mishi,ta kawo Falon. A hankali ya tashi zaune ya fara ci tana bashi ruwa..
” A ina maganin ka suke na dauko maka?”
“Yana side bed” tashi tayi ta shiga dakin ta dauko mishi, ta dawo. Yana gama ci ya sha sannan ya koma ya zauna. Wayar shi ce a daki tayi kara, ya shiga kokarin mikewa. Tashi tayi tana faÉ—in.
“Barshi na dauko maka” ta nufi cikin dakin da sauri ta dauko mishi, sake kiran wayar aka yi,ya dauka.
“Ummyna! Shine zaki saka aka a kawota tayi ta wahala dani, ita da ake son ta huta sai ta fara wahala”
“Allah ya muku albarka ba wahala bace lada ne, dan haka ka kwantar da hankalinka zata kula da kai babu abinda zai faru insha Allah, amma don Allah a kula da jinya kar a ce za a yi wani abu bayan da sauran ciwo”
“Toh” ya fada a shagwab’e.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button