NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

     Bayan dawowan su da shekara daya, ta samu cikin Rahmah. Farin cikin a wurin Alhaji Ishaq canji babu magana, har lokacin haihuwar yazo inda ta samu Y’arta mace, aka saka mata Rahmah. Domin ranar da aka haifi Yarinyar yayi wani katon mahaukacin canji, inda ya samu nashi kason kusan makudan kudi kamar hauka, kai tsaye ya ce.
“Allah idan ta sanadin Yara mata zan samu Aljannah Ya Allah ka karo min masu albarka irin su”

Allah kuma ya saka mishi albarka, domin yana samu kuma ya dauki soyayyar duniyar nan ya daura akan Yaran shi mata. Shekarar Rahmah biyu, aka haifa Wasilah wayyo Allah a wannan shekarar ne Ubangiji ya kuma ninka mishi samun shi, sai dai bayi sa’an yan uwan ba domin basu da burin da ya wuce su hana shi zaman lafiya da iyalin shi.

       Duk da sana’ar canji kowa yasan sana’a ce ta kasada, amma Allah ya dafa mishi ta kowani fuska,, Wasilah tana da shekara biyu Allah kuma bawa Harirah cikin Rabi’atul Adawiyya, yarinya me tsananin hakuri da shiru. Bata da magana bata da hayaniya..tun daga kan ta Harirah bata kuma samun ciki ba, haka ba karamin d’aga musu hankali yayi ba, musamman ita domin Alhaji Ishaq canji ya ce bai damu ba, Yara matan sun ishe shi.

      Lokaci guda aka saka Jamilah da Rahmah a school, yaran suka taso da kwazo da kokari ta kowani fuska na rayuwa,  shekarar su uku aka saka Wasilah da Rabi’atu, gashi abin burgewa suna tausayin junar su,.suna kokarin kyautatawa junansu. Idan daya bai da lafiya toh dukkan su suke komawa marasa lafiya. Har ya warke.

    Haka suka taso, Jamilah tana Ss1 yayinda Rahmah take jss3 Wasilah tana primary six, Rabi’atu tana primary 4, kuma dukkan su makarantar kudi suke boko da islamiyya.

   Alhaji Ishaq canji, ya samu matsala da wasu kudaden shi da ya zuba yayiwa wani baturen england canji ne, cikin tsautsayi sai baturen ya tafi ba tare da ya biya shi kudin shi ba, kuma wani abin tashin hankali, kudin har da na wasu abokan shi. Duk da yayi musu bayanin abinda ya faru domin nashi kudin ya ninka nasu sau biyar, amma mutanen suka ki yarda Dake daman sun jima suna bakin ciki da samun shi. Kawai suka maka shi kotu, wannan shine mafarin ƙaddarar harirah.

       Duk yadda suka so a dakatar da shari’ar abin ya ci tura, domin kuwa sai da suka sayar da kome nashi aka biya su,.kudin su amma dake sun shirya sharri basu kalli abun ba,.kawai burin su a rushe shi a gidan kaso. 

   Bakin cikin wannan yanayin da suka shiga babu iyaka., Haka suka tasa keyar shi aka kai shi gidan kaso inda zai wata uku, bakin ciki da kewar iyalin shi..yasa shi kasa wani abun a can har ya fara rashin lafiya a tsatsaye.
A bangaren Harirah rayuwa bata zo musu da sauki ba, domin daga ita har Yaranta, sun shiga cikin taskun. Domin sai da takai sun koma Daƙayyawa.

        Anan ta fara soyar kosai, dake tana da zuciya tana kosai da koko, ita da Yaran.. sai gashi sunyi survive. Da shi suka rike kan. Babban burinta bai wuce mijinta ya fito ba. Babu wani taimako daga yan uwan shi, Asalima tunda abin ya faru suka janye jikin su, ya sha gaya mata mata yana da kadarori a wurin yan uwan shi, sai gashi lokacin da ta je Yaya Haliru da Badamasi suka nuna babu ko tsinke shi a wurin su.

     Haka suka rike kan su, domin badan wannan gidan da suke dashi ba,.toh da asirin su ya tonu. Jama’are taje tare da kokawa Yan uwanta halin da take ciki, suka ce zasu hada  kudi, ta ce musu.
“Kudi zai kare, idan kuka saya min kayan sana’a kuma zaku huta da tunanin xan sake dawowa, ko inji ku saya min koda kuwa ta hannu ce”

   Sun san lokacin da take dashi kaje mata,.babu makawa sai kasan kaje gidanta. Dan haka suka bata buhun wanke, rabin buhun gero, masara da shansharan shinkafa, akan ta gume shi..sai sabuwar injin markade. Tare da karamin galan na manja da mangyada,  sannan suka dunkula mata dubu talatin suka bata.
(NAKA SAI NAKA DADIN ZAMA SAI BARE INJI BAHAUSHE,
   

Haka ta dawo dama bata tafiya ta bar yaranta, tun da ta dawo aka kira me hada injin ya saita mata shi, ta fara aikin markade, makotansu na kusa da na nisa,.haka suka kawowa har wurin ta. Wata uku na cika aka kawo mata Alhaji Ishaq canji babu lafiya, yan kudin hannunta da zata saka yaran su a makaranta duk ya kare, haka ta tsaya akan shi babu taimakawar dangin shi.

    Allah ya saka yaran ta masu zuciya ne, sune suka tsaya akan abinda take suna kula da kome. Dake yaki yarda su tafi asibitin a bar yara a gida,.ko sun je dutse ganin likita basu kwana suke dawowa. Zuciyar shi ta tabu sosai. Bakin cikin abinda aka mishi, na tozarta shi, ga Yan uwansa sun guje shi. Matar da basu kauna itace a jikin shi.

         Haka ya cigaba da ganin takaici. Sai dai idan ya zauna da ita yana yawan gaya mata cewa.
“Idan hakkina ne, Allah sai ya ninka min su, ko ban mora ba Yarana zasu mora. Idan kuma ba hakkina bane Allah ya baku zaku dogara dashi, a cikin yarjejeniyar da muka yi. Na saka sunan Yarana kece wakiliyarnsu, Allah kana gani, na bar maka kome a hannun ka, Ya Allah iyalina, Ya Allah kajibanci al’amarin su. Ya Allah na bautawa zumunci Ya Allah ka jibanci al’amarin Iyalina.”

Wannan shine addu’ar shi a kullum, idan Ya dubi yaran shi, basu zuwa makaranta, sun koma kamar marasa galihu, haka yake kallon su zuciyar shi yana kuna. A hankali rayuwar take tafiya, watan shi biyar da  barin gidan Yari Allah ya amshi abun shi, tun a jinyar shi Haliru da Badamasi basu zo ba, sai yanzun da Ya rasu nan suka sako Harirah a gaba na lallai sai ta gaya musu inda ya ajiye sauran takardun shi, dama kamar ya sani da Abokan shi Alhaji Lawal Dambatta yazo ya mika mishi takardun yana faÉ—in.
“Gashi kai ne silar zamana wani abu,  wannan takardan Yarjejeniyar mu ce akan canji. Alhaji Lawal Dambatta yan uwana zasu nima Harirah zata basu, ni kuma bana son haka. Don Allah gashi ka ajiye a wurin ka, domin nasaka sunanka da address dinka ko basu samu Iyalina ba,.kai kasan inda zaka same su nagode”

Sun yi haka da kwana biyu, domin Alhaji Lawal Dambatta yazo har Daƙayyawa. Bayan tafiyar shi ya samu  labarin rasuwar Aminin shi. Bai ji Yazo ba a lokacin domin yasan dangin shi suna tare da Harirah,kuma yasan idan yazo zasu iya matsawa rayuwar ta da na Yaranta tunda yasan kome akan su, tun dan uwan su yana raye.

     Wannan shine mafarin labarin.

A hankali ta yafito Yaranta, da sauri suka zo jikinta..suma suna kuka tare da jin kamar su cire mata damuwar da yake damunta. Tun addu’ar uku yan uwan ta, suka so tafiya da ita tace ba zata busu ba, domin Yaranta. Wannan dalilin yasa suka tafi da safe Bayan anyi addu’ar bakwai.

     “Ammih ki daina kuka” inji Rabi’atu, sake rungume ta tayi tare da jin kamar ta boye Yaranta, domin gani take kamar kowani lokaci rayuwar su, tana fuskarta barazanar rayuwa, haka  ta saka su a cikin jikinta,.kamar dai yadda kaza take sanya y’ay’anta a jikin ta.

    Jamilah da Rahmah suka shiga kitchen,  suka dumama musu abincin da aka rage na sadakar bakwai din safe, ta zubo musu, tare da kawo musu dakin su, Rabi’atu tana jikin Uwar kamar zata koma Cikin ta, wani irin shakuwa ce take sake shiga tsakanin su, irin na uwa da d’a. Abin tausayi sai tayi kamar zata yi kuka sai kuma ta cigaba da ajiyar zuciya. Kallon ta Harirah tayi cikin tsananin damuwa.
“Adawiyya meke damunki?”
“Babu Ammih, ina son nayi kuka ne” ta fada tare da kallon Mahaifiyar ta.
“Kuka kuma Wiyyah” inji Jamilah,
“Eh Yaya Jamih” ta fada tare da daura kan ta, a jikin Ammin su, shafa kanta Ammin tayi cikin wani irin tausayin Yaran. Boye kukanta tayi tare da rarrashin su, har suka ci abincin. Sannan suka zauna mata. Kamar ba zata bar su. Su tafi dakin su ba. Haka ta bisu har dakin su ta musu addu’a. Sannan ta dawo nata, bata iya barci ba, alola ta shiga tayi a ban daki ta fito ta fara nafillah, har wurin karfe daya na dare tana zaune, kuka take kawai idan  ta tuna shi kenan mijinta ya tafi ya barta, da Yaran su. Sai ta ji zuciyarta yayi mata nauyi tare da jin wani irin abu na mata yawo a kan ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button