NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

    “Nagode” bai ce mata kome ba, ya cigaba da tafiyar shi, komawa baya tare tana me jin kamar ta koma ta duba halin da Baba yake ciki, amma tsoron kar ya tafi ya barta yasa bata fara komawa bukkar ba.

   *
Har kofar gidan ya kawo ta sannan ta wuce abin shi baya yaga shigar ta cikin gidan..tana shiga cikin gidan ta samu sunyi cirko cirko suna kallon kofar gidan.
A hankali ta shige jikin Yan uwanta, wani irin kuka ne ya kama ta, suma kuka suke. Dakin Ammin su tashiga tare da zubewa cikin dakin.

Ta rarrafa gaban Amminsu, ta daura kanta a kafadar ta, tana kuka tare da tuna abinda ya faru da maganar da Malam Aaman.
Idan kika koma gida me zaki gayawa Abban ki da Ummanki?
Shiru tayi kanta a sunkuye tana kallon kasa.
Ba a gayawa Iyaye wannan maganar kinji zaki lalata zumunci ne, kiyi shiru Karki gaya musu ba zai kuma Miki kome ba
Gyada mishi kai tai tare da yin gaba, yana bin bayanta har zuwa gida, wani irin kuka ne ya kuma zuwa mata.

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny

Na
Mai_Dambu
MAMAN LABIB COLLECTION TAZO MUKU DA TURAREN WUTA MASU KAMSHI DA KAMA WAJE.

KAMAR SU KAJIJI,  SANDAL FLAKES, SANDAL BANGE, SUGER CUBE, WHITE SANDAL, HALUT, DORUT, DUKKAN,  AKAN FASHI ME SAUKI

Http://wa.me/+23408144687796

Wani Al’amarin<5>

Rungume Ammin su suka yi dukkan su, watakila su fahimci halin da suke ciki, watakila su din su fahimci halin da take ciki, amma da matukar ciwo,  rungume yaranta tayi kamar yadda suka rungume ta, sai ta sumbaci kan wannan, ta koma kan wannan, tana shafa kansu.

        Sun jima a cikin wannan yanayin kafin tayi karfin zuciya tace musu.
“Amma yau azumi zamu dauka ko?” Dariya suka saka tare da mikewa kowa ya fara kokarin kama abinda yasan na shine, har suka gama dafa dukar shinkafa da wake, wacce ta ji kayan miya da daddawa da citta sai wani kamshi yake na musamman. A babban ture suka zuba nasu. Ita kuma Ammin suka zuba mata nata, suna ci suna kallon juna, lokacin zuwa lokaci. Suna share kwalla. Har suka gama sannan suka mike.  Basu da kawaye sune kawayen junan su,.dan haka Jamilah taja Rahmah suka fita dakin su ba da, tana gaya mata abinda Baba Haliru yayi mata. Kuka Rahmah ta saka tare da rike hannun yar uwar ta, tana faÉ—in.
“Bai miki kome ba?” Ta tambaye ta a tsorace tana kallon ta,
“A’a bai min kome ba wallahi” ta fada tare da kallon jikinta.
“Kirjina ne kawai yake ciwo”

Cikin tausayin Yar Uwarta tace mata.
“Na saka miki ruwan zafi ne ki gasa jikin ki?” Rungume Rahmah tayi tana jin wani irin dadi da kuka yana kamata.
“Nagode Sosai yar uwa!”
“Yaya karki damu, ina tare dake a koda yaushe, ba zan tab’a barin ki kiyi kadaici ba.”

    Haka ta fito ta haɗa wuta, ta daura mata ruwan zafi, wajen karfe shida ta shiga ban daki tayi wanka tana fitowa , Gwaggo Lami tana shigowa kai tsaye ta nufeta, tare da rufe ta da duka.  Dan tozarci ma har da kunce mata zani tana ihu.
“Wulu wulu!!!  Karuwa dan Yaya Haliru ya hana ki bin mutumin shine zaki saka ya dake shi a gaban shi wato ya kashe mishi gaba, kai wannan yarinyar Anyi tsinanniya, la’ananniya mara kunya Æ™aruwar banza.”

Bata fasa dukanta tana kira mata jafa’i ba, sai da Rahmah da Wasilah suka kwaci Jamilah a hannun ta, suna k’amk’ame juna. Kallon su tayi daidai fitowar Ammin daga cikin dakin. Ta ce musu.
“Toh, ai dole ku nuna min ku cikakkun ya’yan kariya ce, amma mu zuba daku, Harirah akan Yarki aka nime kashe mana Dan uwa, toh wallahi sai mun shigar da ke kara kotu. Inshallah sai sun ajiye miki abun kunya dan daka kuka.”

Ta saka kai tafita, kallon Jamilah Ammin su tayi, kafin ta koma dakin ta, bin bayan ta suka yi suna kuka. Har cikin dakin suka zauna a gabanta.
“Ammin wallahi ba haka bane bata fadi gaskiya ba, Ammin wallahi sharri ne” a hankali ta gaya mata abinda ya faru, shiru tayi kanta a sunkuye, tunani ne ya zo mata, ta rasa me xata yi domin kare rayuwar Yaranta mata. Dan haka bata ce uffan ba, amma kuma zuciyar ta yana ciwo. Har aka kira sallah magrub, ta tashi ta rufe kofar gidan ta dawo suka yi alola suka gabatar da sallah.

     Har bayan karfe goma tana kallon Yaran da suke takure wuri guda, buɗe musu hannu tayi, da sauri suka fada jikin ta suna kuka. Itama daurewa take amma tabbas kukan zuci take.

   Har suka kwanta, bata iya barci ba, a wannan lokacin hana idanun ta barci tayi tana gadin Yaranta. Ta hana zuciyar ta sakata, tana kallon su sallah kawai yake d’agata, bayan nan babu abinda take iya yi. Goshin asuba ne ta kwanta, barci ya É—auke ta. Dan haka basu tashi ba, sai da Rabi’atu ta tashe su, baki dayan su.

   “Toh Yau kan Ammin babu kosai dan an makara.”  Ta fada tana nufar hanyar ban dakin Ammin su.

“Innalillahi! Yau kuma nice da makara, maza ku tashi gobe INSHA ALLAH, ayi kosan muyi sallah sai ku shirya zuwa makarantar.”

   Haka suka shirya a gurguje, suka nufi makaranta. Tun a hanya Jamilah take cewa.
“Rahmah, Wasilah don Allah ku raka ni ajin mu,.idan muka raka Beeyah aji”
“Ba zan raka ki aji ba, domin ina son yau na zauna a kujeran gaba ne fa” inji Wasilah.
“Yaya muje ni da Yaya Rahmah mu raka ki kin ji.” Inji Rabi’atu.

    “Yawwa Yan matan Ammin.” Inji Rahmah suna shiga makarantar, har kofar ajin  su ta ajiye ta, sannan ta juya abinta.

Bayan ta shiga ajin ta ajiye jakarta, zama tayi. Ummu Abiha da kawayenta suka dauki jakar, tare da zazzage mata shi a ƙasa.
“Shegiya me shegen kyan bala’i da nace kar a kuma ganin ki da Malam Aaman D Muhammad shine aka ganku tare ko? Kamar yadda na zazzage jakarki haka zan ci.”

   Dukar kafarta aka yi ta baya, da sauri suka juya, Wasilah ce tsaye tana wasa da pencil dinta, tana feke shi da shaperno.
“Ke dan Ubanki” take mata kafa Wasilah tayi, sai da ta fasa ihu ta fadi.
“Dan bamu da arziki bayana nufin bamu da zuciya bane, kassara kan mu ne a tab’a Yaya Jamilah mu kasa magana, kwashe mata materials din ta, zuba jakarta ko na karya Miki kafarki.”

Sai da suka kwashe mata books dinta, sannan suka ajiye mata kayan ta, zuwa tayi gaban yayar da take kallon ta.
“Gashi nan pencil dinki ce jiya nay’i aiki dashi, yanzu na sayi nawa” ta ajiye mata tare da barin ajin. Haka Malmin Maths ya shigo ya fita, Ummu Abiha tana kuka, a boye karshe haka suka kaita clinic na cikin makarantar, aka duba kafar, tare da tambayar ta, Meye ya faru. Taki fadar gaskiya sai cewa take tayi tuntube.

Asibitin.

Matar Yaya Haliru, kallon shi tayi tana mamakin yadda yasaka son zuciya a cikin al’amarin shi, domin tayi Imani da Allah  karya ce kawai, garin ya lalata musu yar mutane ne haka ya faru da shi. Domin tasan shi yadda yake bin mata kamar bunsuru.  Karya ce kawai ya gindayawa yan uwan shi.
“Assalamu alaikum, Sannun ku Haliru ya aka yi haka ya faru da kai, ko dai kaje bin mata mutane ne aka samu wanda ya doke maka ƳaÆ´an yayan itaccen ka?”

  Cikin fushi ya makawa dan uwan shi, yana faɗin.
“Dalla yarinyar nan Jamilah na kama a bayan lambuna, ita da wani mutum suna masha’a, shine suka rufe ni da duka, wallahi kuwa ku tambayi Yarinyar ai ba zan mata karya ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button