NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Dukar kayan  gaban shi nayi, ya fasa wata irin kara, tare da Zubawa yanae dunkule wa wuri guda.
“Ni fa ba zaka iya kome a kai Munir” da gudu ya shigo cikin office din.
“Ya sunan shi?” Na tambaya.
“Irfan Kabir Wazir”
“Ya hadu maza fitar min da shi ka kai shi Asibiti da gaggawa maybe ya rayu da gaban shi”

    “Toh…TOH” ya dauke shi suka fita, dariya ya bani.
**
Karfe hudu na yamma suka iso, dan sun tsaya a dubai, kallon Faisal yayi yana faÉ—in.
“Kai ni kamfani”
“Kuma can?”
” Idan ba zaka kai ni ba na fita da kaina”
“Allah ya baka hakuri”

Har suka iso babu wani magana me dadi dai masifa kamar zai daki Faisal. Har suka iso, bai kula kowa ba ya nufi cikin kamfanin hannun shi daya cikin rigar wandon shi. Har zai wuce yaji ihun munir a staff office.

“Zaka gaya min waye kai ko sai na murde maka” na fada a tsawa ce.

Bude kofar yayi ya gani rike da kwalar rigar munir.
“Sake shi kizo ki fita” tura baki nayi tare da cewa.
“Bana son haka daga zuwa baka san me ya haÉ—a mu ba.”
“Fita nace” ya daka min wata irin tsawa, sai da na sake shi, babu shiri na fita ina kunkuni.
“Ki gama zagina duk ranar da na kamaki sai kin gaya min yadda akayi haka ya faru”

Kallon kayan jikina yayi yana jan tsaki, “mahaukaciya” kallon Munir yayi tare da daure fuska.
“Kar na kuma ganin ka da ita dan zan kore ka” daga haka ya fita.
A hanya na hadu da Faisal, sai masifa nake tare da hararan gefe da gefe. Garin kaucewa P.A din Mr Jikamshi, muka ban gaji juna. Wani igiya ne ya fado kasa.

“Sannu ba”
“Hmm” ya ce min sannan ya wuce. Kallon igiyar nayi me É—auke da Flash, so nake na tuna inda na san shi, a hankali na kuma bin shi da ido, kafin na saka kai ma fita.

Kusan tunda suka shigo tattaunawa suka yi akan Abubuwan da Rubi tai, sannan Faisal bai gaya mishi aikin Rubi bane,

  **
Wucewa Super market nayi na kwana biyu, ban ga matar nan ba. Abubuwa dayawa na saya mata. Sannan na nufi Unguwar,na manta da mayafin da ta bani sai da na isa gidan.

   A hankali na bude kofar shiga gidan,tana zaune a harabar gidan idanunta yana kan kofa.  Kallon ta Ammyn take a jikin ta tana jin kamar ta dawo mata ne, murmushi ta sakar mata.
Cikin nutsuwa nake takawa ina murmushin farin ciki, har na isa wurin babban taburman,na zauna tare da kallon cewa.
“Kiyi hakuri nayi tafiya ne kuma bani da lafiya sai”
“Ya jikin ki”
“Da sauki ai yanzun. Gidan babu kowa ne?”
“Eh yayunki basu nan”
“Ga wannan babu yawa” karb’a tayi tana cewa.
“Wani sana’a kike?”
Kallon ta nayi sannan nace mata.
“Aiki nake a kamfanin JIKAMSHI MENIRAL RESOURCES”

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/10/22, 08:10 – My Mtn Number: 68
“Allah yayi miki albarka a kula da kamun kai, ba ko ina ake sakewa ayi abinda bai da ce ba” ta fada min.
Gyada mata kai nayi ina mika mata ledar.
“Ga wannan babu yawa, da fatan zaki amsa” na fada ina kallon kasa,
“Nagode sosai” kallon farcen hannun nayi naga a gare na ce mata.
“Toh zan tafi”
“Har zaki tafi? Ki gaida iyayen ki” murmushi nayi tare da cewa.
“Zasu ji” haka na bar gidan, ina jin wani irin nutsuwa a raina, ki babu kome ina jin ta kamar uwar da ta haife ni, tausayin da kaunarta suna cika min zuciyata.  Wayata ce tayi kara na ciro na duba..

    “Ayola”
“Kina ina ne?”
“Wani abu ne?”
“Gidan marayun ne ake zo za a tashe su wai wata mata ta saya ga masu aikin rushe gidaje nan”
“Oh God! Toh gani nan zuwa” taxi na nima,da zai kai ni unguwar mu, muna isa, na sauka na biya kudin motar, wurin masu rushe gidaje naje.
“Wai duk meye haka? Sannan waye ya  kawo ku nan? Gidan nan yana bisa tsari tare da duk wani sharudda.”

“Eh toh idan ya zama an rushe marayun basu da matsuguni fa? Kiyi amfani da kanki mana.” Juyawa nayi na kalli Jamilah, mikawa Ayola jakata nayi, koda zamu rasa gidan Marayun dole na fahimtar da Jamilah Hauka take.

        “Me kike bukata?”
“Ina son zan rusa gidan nan ne domin na samu shaidar mallakar shi daga sama” ta d’aga yatsar ta tana zagaye wuri da shi.

Sosa goshina nayi tare da kallon ta, sannan nace mata.
“Ban ji sosai ba? Ko zaki iya gaya min me kika ce?” Dake mahaukaciya ce maimaita min tayi.
Riko hannun ta nayi na bude mata motar ta, na cusata da karfin tsiya.sannan na d’aga kafana na daura akan cinyar ta. Motsi zata yi na danna kafar da karfin tsiya.

“Zan yi draging dinki into the hell,ba iya shi ba kika tab’a wannan gidan marayu, suna na ma idan kika ki ji an kira sai kin gudu da kafar ki. Ke bake ba idan akwai wanda yake kara tinxira ki sai na ga bayan ku, zan kuntata miki, zan takura miki yadda sai kin ji kin tsani kanki. Sai na hanaki sakat, ke kar na kuma ganin ki a cikin unguwar nan idan kuwa haka ta faru” murmushin gefen baki nayi mata sannan na rufe mata kofar, na dunkule hannuna na zabgawa glass din motar naushi sai da na fasa akan fuskarta. Wani irin masifaffiyar tsoro na gani akan fuskar ta.

“I don care. Idan zaki shekara kina min ba zan kula ki ba wannan gidan shine ni nan” na wuce tare da d’aga yatsuna ina gargadin ta.

Cikin wani irin mugun tsoro tasa mutanen suka bar wurin.
“Yaushe Rabi’atu ta zama haka? Yaushe ta koma haka? Me ya faru ba ita bayan barin gida?” Ta fada tana dafe kanta, d’ago kai tayi tana kallonta. Musamman yadda ta hade hannunta a kirji tare da kallon yadda ta tsare kofar gidan marayun.

      Cikin tsannanin tsoron ta ke kallon Rabi’ah, yayinda ita kuma take mata kallo cikin da gaske zan yi iya kome domin na tsaya musu, dole suka bar gidan.
Juyawa nayi na kalli yadda kowa yake sauke ajiyar zuciya.
“Mun gode Rebecca”
“Ba kome” na fada ina daukar Abraham, cikin gidan muka shiga.

**
Gidan Ammyn ta wuce, kamar mara gaskiya haka ta shiga, ganin Aaman da wata yarinya yasa ta dauke kai.
“Ina wuni” yarinyar ta gaishe ta,
“Lau” ta wuce dakin ta, bin ta yayi da ido.
“Ammyn ina Wasilah? Gashi yau na kawo mata Husnah.” Cak Jamilah ta tsaya, yana sane da haka yayi maganar.
“Tana jarabawar ta na karshe ne, shi yasa yaushe Alkasim zai zo, dan Baban ku ya isa Jigawa wancan satin sun yi magana da Mai unguwa”

“Eh haka yake gaya min, nima ai sunyi magana da Iyayen Husnah.”  Ya fada yana sosa kan shi.
“Allah ya tabbatar da Alkhairi, Ubangiji ya baku zaman lafiya da Zuri’ar dayyiba, Allah kara maka hakurin zama da ita, ya biya ka ladan hakurin da kayi, Ubangiji yasa itacce mafi alkhairi a gare ka.”

“Amin Ya Allah” suka fada a tare, dakin ta ta shige da sauki, ta fashe da wani irin kuka. Tana me jin kamar zata mutu, shikenan babu wanda ya damu da ita, kowa kan shi ya sani, babu me damuwa da damuwar ta.
(Karki damu sun miki farraqu ne yan comments GRP 🤔)

      **
Washi gari.

Ban fita da wuri ba sai karfe takwas, koda na isa wurin aikin karfe tara da rabi, sabida go slow da aka samu. Sanye ne da gown iya gwiwa, sai yar top din da na daura akai, ina shiga muka gaisa da mutane. Tsayawa muka yi aka fara hira.
“Amma yau Yallabai Faisal bai shigo ba?”
“Eh bai shigo ba, amma kamar gasu nan shi da Mr Jikamshi” juyawa nayi a hankali na Kalle su, yadda suke tafiyar gwanin ban sha’awa. Juyawa baya nayi ina me cigaba da abinda nake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button