NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Namir yana shiga cikin office din, abinda ya fara duba locker din da File din da aka yi bincike ya fara dubawa, sai dai kash baki daya babu file din babu dalilin shi wani munafukin zuba ne ya shiga zubo mishi, d’ago kan da zai yi suka yi ido biyu da Jikamshi. Wani irin zaman yan bori yayi domin dabas ya zauna akasa bai san lokacin da da wani uban zufa ya karyo mishi ba, ya kura mishi ido.
“Ban san me kake boyewa ba,” daga haka ya fita daga cikin office din,
Kallon shi Faisal yayi tare da cewa.
“Wani abu ne ko?”
“A’a ba zai fada ba, amma akwai lokacin da zai yi magana” ya wuce abin shi kamar bashi ba. Yana nufar wurin motar shi ya shi aka bude mishi ya shiga, shima Faisal ya shiga na shi, suka jera har JIKAMSHI HOUSE. Inda zasu yi board meeting.

Sai da ya tabbatar sun bar asibitin shima ya bar asibitin tare da nufar unguwar su Aaman.


Koda suka isa babu kowa sai Hajiya Shuwa da Alhaji Adamu Abbas Jikamshi, tsayawa yayi yana kallon su, bai ce kome ba. Faisal ma haka sai kallon agogo yake, can kamar bayan minti goma sha biyar, sai ga Alhaji Abubakar da Ambassador Abdulkadir, Hajiya Turai da Humaidah. Kafin aka shiga meeting din, yana zaune a kan kujeran yana jin su kowa ya gama yiwa kan shi campaign.

“Ok idan na fahimta dukkan ku, kuna son  a baku damar rike Jikamshi Group. Toh a nawa tunanin na Yaro karami a cikin Ku sai nake ganin da za a zaben da zai baku damar sanin waye ya dace da matsayin da yawan jama’a shi, sannan idan har na ce Baba Adamu ne, Baba Abubakar zai ce bai yarda ba, idan nace Aunty Humaidah ce Aunty Turai ba zata yarda ba, idan nace Baba Abdulkadir ne Hajiya Murjanatu ba zata yarda.”

” Amma Gong Yoo baka da mutunci? Ban kai matsyin da zaka Kirani da Aunty ba sai Hajiya Murjanatu” ta fada a matukar fusace.
“Koma ki zauna.” Ya nuna mata wurin zaman ta amma fir matar nan taki sauraron shi, sai da ya daka mata tsawa tare da dukar table din, hadiye guntun maganar tayi tare da kura mishi idanu.
A hankali ya mike sannan ya dauki ruwan faro ya bude mata, ya zauna sosai a gaban ta, yana kallon ta ya mika mata.

   “Hajiya Murjanatu ba rashin kunya bane ko rashin sanin Darajar ki a’a asalima nafi kowa girmama ki, shi yasa na kiraki da haka.” A hankali yayi kasa da muryan shi, kafin ya ce mata.
“Idan kika kuma d’aga min murya zan manta kin auri Ubana, zan baki a good disable kuma na cire hannun jarinki a cikin kamfanin mu, kin fahimci abinda nace ai” ya fada .ta haka yana murmushi, wani irin zufa ya karyo mata, mika mata hanky yayi tare da cewa.
“A kula da harkokin kasuwancin kawai ban da cin mutuncin, sannan idan kun amince sai mu shirya nan da kwana uku, amma ku sani an nime Alman Abdul Hadi Shema ba a same shi ba, kuma ana gargadin Ummin mu, ni kuma nayi imani da Allah matukar aka gama meeting din nan bai koma asibiti ba, zan yi blocking account din kowa, ayi break sai a cigaban”

Ya fada tare da mikewa, wajen da aka ajiye musu kayan ruwan zafi ya nufa tare da É—aukar Cafenncino, ya zuba a mug,sannan ya bude mata ruwan zafi. Shi kuma Faisal ya dauki normal garin Coffee da madara ya had’a babu sugar. Komawa gefe suka yi suna hira tare da dariya, ba zaka tab’a daukar akwai abin da yake damun su ba. Kiran Faisal aka yi yana jin ring din ya fahimci Ummin ce.
“Assalamu alaikum Ummin mu, Ya dai?”
“Alhamdulillahi ga Alman, ya dawo sai dai baya cikin nutsuwar shi”
“Ok bari mu gama zamu zo”
Murmushi yayi yana kallon mug din,
“Amma kai kan an yi tantirin mara mutunci sun dake shi” murmushi yayi sannan yace mishi.
“Na gama mishi kome, idan zan tafi zan sauke shi a United State yaje can ya shiga aikin soja”
“Alhamdulillahi! Ka gama min kome kamar kasan abinda nake shirin aikatawa kenan Alman baya jin magana, idan aka tura shi can zai fi samun nutsuwa idan ya tuna baya gida.”
Kurban ruwan shayin yayi tare da kallon shi yana murmushi. Agogon hannun shi ya duba sanan ya shanye ruwan shayin suka nufi board din, inda ake meeting din.

Sun cigaba da Meeting din da kansu, suka Amince ayi zaben, domin da farko sun zata zai yi gaban kan shi ne,shi yasa aka samu mugun da ya dauke Alman shi kuma Jikamshi duk abinda zai yi da brain yake yin shi. Sai gashi sun yi barazanar sace Alman domin yabi tsarin su, amma abun mamaki sai gashi barazanar shi ya saka an sake Alman wannan shi ake kira da karfin iko, ba kowa yake da shi ba, su kan su a yadda yayi musu bayanin sai suka gamsu da zaben Kuma suka yarda da cewa shi din shugaba ne a kowani fuska, kuma babu fada ko tashin hankali yayi musu bayanin da yasa su yarda da abinda yake nufi akan Kamfanin su, da wannan aka tashi a taron meeting din.

    
*
“Ban gane ba, idan kana son yarinyar ka gaya min amma zaka nemi tsayar dani akan abinda nasan ina bukata kaga malam bani wuri na wuce” inji Namir Adamu Abbas Jikamshi,

Zuba mishi ido Aaman yayi bai iya cewa kome ba, amma baki daya tana cikin kunci da damuwa, dan haka ya matsa mishi tare da kokarin boye damuwarsa ya ce Mishi.
“Toh Allah ya baka hakuri, indai akan Jamilah ce ga hanya”

Ya fadi haka yana nufar cikin gidan su.
“Wai meye nufinka? Kana nufin ni zan kai kaina cikin gidan su? Dalla zoka raka ni” ya fada yana maka mishi harara.
Babu musu ya dawo tare da mishi jagora har cikin gidan, Ammyn taji dadin ganin Aaman bayan sun gaisa ta ce mishi.
“Aaman dama maganar makarantar su Rahmah da Wasilah ne, akwai abinda za’a yi ne?”
“Akwai makarantar da yake karkashin jagorancin JF Group me zai hana a saka su a nan babu matsalar kome kuma ana Koyarwa sosai” Namir ya amshe maganar da sauri,
   Kallon shi sukayi kafin Ammyn ta ce .
“Toh duk abinda aka ce duk daya ne, amma ina jiran naji me Yayansu zai ce?”  Mai da idanun shi yayi kan Aaman da yake son magana,
“Ina gani tunda dama Jamilah zata zana waec ne aka samu matsala, toh ganin bata lafiya an zana mata, domin nasan tana da kokari,  akwai wani makaranta anan gaba damu ana extra moral, zata zauna na tsawon shekara guda tana karatu, kuma shi karatun kusan daya ne da na yan aji dayan Jami’a, dan haka idan aka yi Jamb sakamakon ta yayi kyau, ina ga zamu turata cotonuo tayi karatu akan shari’a ta zama lauya.”

“Amma me yasa sai cotonuo? Muna da manyan jami’o’i anan sannan muna”
“Amma ba shi zai hana su, shiga yajin aiki ba, shekara biyar zata yi tazo nan tayi law school shekara daya, ta tafi service shekara daya baki daya ake bakwai, sannan kace anan zatayi.karatu, anan din da sai a shiga yajin aiki a cinye semater guda a gida, so tayi karatunta a cotonuo zai fi mata”

  Shiru Namir yayi yana me jinjina qarfin yarda da yake tsakanin Ammyn su Jamilah da Aaman. Muryan Aaman ne ya katse mishi tunanin da ya ce.
“Akwai Makarantar da Jadwah da Jawahir suke a saka Rahmah da Wasailah, ina ga shima babu matsalar kome shi kenan.”

  Murmushin jin dadi Ammyn ta sake sannan ta ce mishi.
“Naji dadin haka, amma ya batun auta na? Har yanzu babu labarin ta ko?”
Shiru yayi ya kasa magana, sannan ya ce mata..

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button