NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

Tun daga lokacin, na zama kamar hannun damarta, bata kaunar barina da kowa, ganin Nima ban yarda da kowa ba sai ita yasa ta hakura ta barni ina jinya a gida.
**
Lagos.

Sosai ake kai ruwa rana da Jamilah, dan dole aka taushe Ammyn ta barta akan ta saka Namir ya turo.

  Aikuwa cikin farin cikin, ta gaya mishi, a bangaren Rahmah kuwa Ammyn da kanta ta gayawa Ummin ta turo wurin Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, shi zai musu jagora zuwa Daƙayyawa.

       Bilal kawai Ummin ta gayawa sai Mahaifiyar shi,daga nan sai Yadiko wacce itama ta dawo Lagos shekaru biyu da suka wuce, sune suka sani, ba a gayawa kowa ba, Wasailah ba a saka da ita ba, saboda Alkasim da bai kasar shima ya tafi karatu. Amma an saka bikin Jadwah da Jawahir, suma duk tare za’a haÉ—a.

    Tunda Jamilah ta gayawa Namir ya samu baban shi yaki  kula zancen, kuma abin har an tura yan uwan Baban Faisal sun tafi an basu auren Rahmah babu labarin Namir.

“Na ce ka nima min auren Jamilah kana min wasa da hankali Meye nayi maka da zafi haka?”
“Naki na nima maka auren yarinyar da kuke watsewarka da ita? Ka hakura akwai yan mata amma ban da ita, domin ba zan dauko yarinyar da Yayan Ubanta ya lalata ta ba.”

“Ina sonta a haka itama ba sonta bane Æ™addara ce, idan ba zaka Nima min auren ba zan saka wasu su nima min sai ka san abinda zaka gayawa yan jarida”

Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“TOH babu kome zan nima maka aurenta.”
…kamar yadda ya fada haka ta tafi niman auren Jamilah wa Namir, bayan an bashi a can Jigawa ya dawo nan sannan ya saka aka shirya gagarumin Bikin baikon.

      Sam abin bai kwanta a ran Ammyn ba, amma babu yadda ta iya, domin taga hankalin Jamilah ya karkata a can, dan haka suka ta shirin bikin baikon.

Rahmah itama tazo, domin sun yi Hutu, haka aka yi ta shirin bikin har ranar bikin yazo,a nan ne suka tafi inda xa ayi a jikamshi House.

   Idan ka ga Namir da Jamilah sun hadu, Bilal bai samu damar zuwa ba, sai.dai Mahaifiyar shi da Kannen shi duk sun zo,.haka aka yi ta hidimar har lokacin da xa ayi musayar zobe anan ne aka dan tsayar da su, tare da kunna wani katon cinema da yake hall ɗin.

“Ai Alhaji ni nan na kwanta da yarinyar Ni na fara saninta mace, ai Uwar su ganin haka ne yasa ta gudu suka tafi Lagos karuwanci, itama karamar ai an tafi da ita Karuwanci kasar waje ne, dan haka ina baka shawara karka sake ayi auren danka me mutunci da karuwa.” Shiru hall din ya dauka, abinda Ammyn take gudu kenan, abin tausayi da sauri Faisal ya rufe Ammyn da ake daukar hotarta aka fitar da ita, waje, Rahmah kuma Khalil ya fita ita.

Jamilah ta daskare a wurin ta kasa motsi, Aaman ne ya nufe ta, tare da riko hannun ta suka fito, abin tausayi baki daya aka tozarta su.

“Meye nayi maka Abba? Meye nayi maka da zaka wulakanta min gobe na? Meye nayi maka da zaka tozarta min yarinyar da nake so? Yes so what Dan Yayan Mahafinta ya kwanta da ita? An ce maka ni ina niman mace me dukiya ne? Ita nake so a gaban Jama’a zaka tozarta Musulmi? THANK You amma ka sani daga yau ka fara shirye-shiryen ganin abinda zai sanyaka damuwa,”

   Karfi da yaji suka nuna ai ba wani abu bane.
Ammyn kan jininta ne yayi mugun hawa, Faisal bai kaita asibitin JF ba, ya kaita wani asibitin ne, ya kira Aaman ya gaya inda suke, suna zuwa aka kwantar da ita, domin baki daya an kawota sai haki take, alluran barci aka mata.

  Tun a motar Aaman take kuka har suka isa gida, kasa fita tayi a motar, har Wasilah ta fita, sannan ya ce mata.
“Kiyi hakuri bari na dauki kiran Faisal” nan ta dauka suka yi magana sannan ya kashe.
**
“Amma Alhaji baka kyauta ba wallahi, ka cutar da da Yarinyar da mahaifiyar ta, Allah sai yasaka masu, sun bar can da nufin suyi farin ciki kamar yadda kowa yake shine ka bibiye al’amarin su, idan da a ce tuntuni ka fada wallahi da mun rabata da danka amma sai a cikin al’umma zaka mata haka. Ba kome rayuwa ce Allah ya fidda hakkin wanda aka zalunta.”inji Alhaji Muhammad Lawal Dambatta.

Ya bar hall din, Mahaifiyar Bilal itama sai da tai mishi magana, sake Khalil ya wuce da ita gida a tare da su Layinah,a can tayi ta kuka tana cewa.
“Wallahi sharri ne Ammyn mu va haka take ba, wallahi ba haka bane sharri ne.”lokacin da Ummin da Mahaifiyar  Bilal suka iso, mikewa  Rahmah tayi jininta yana rawa.
“Zauna Dotah”
“Ummin wallahi sharri, na rantse Miki da Allah Ammyn bata taÉ“a magana da wani namijin ba, tun bayan rasuwar Abban mu,.na rantse da Allah, kuma wallahi karya ne Ummin”

    Ji tayi an tab’a bayan ta juyawar da zata yi ta ga Faisal. Rike hannun shi tai cikin kuka ta ce mishi.
“Wallahi, sharri ne,.ita kanta Beeyah an ce mana ta rasu. Na rantse da Allah Ƙaddara ce ta fadawa Yaya Jamilah, Faisal ka yarda damu!”
Hannunta ya kai fuskar shi ya ce mata…
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:57 – Nuriyyat: 49
“Waye ya ce miki ban yarda daku ba? Ko duniya zata juya muku baya Faisal ba zai tab’a juya muku baya ba, me yasa baki gaya min tun farko Namir yana son Jamilah ba? Ai da na dakatar da faruwan al’amarin nan? Kin san Halin da Ammyh take ciki yanzun? Tana critical condition ya zamu yi da ita? Hmm”  a hankali ta sulale ta zauna dabas a kasa, ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi nan take.

“Shi yasa taki yarda da maganar auren ashe tasan me zata ji tasan me zata gani ne, Ashe abinda take gudu kenan, Ya Allah mun tuba ka yafe mana.” Ta fada cikin shashekar kuka, duk rashin imanin ka idan ka ga yadda take kuka sai kaji zuciyar ka tana rauni domin baki daya ta gigita baki daya.

“Don Allah ka kai ni wurinta” ta fada tana mikewa tsaye,
“Ba zan kai ki ba, domin kukan da kike kara mata ciwo zai yi kin ga babu amfanin na kai ki” goge fuskarta tayi. Muryan ta yana rawa ta ce.
“Shikenan na daina kukan” rab’a gefenta yayi zai wuce ta kuma shan gaban shi.
“Don Allah ba zan yi kuka ba, ka kai ni wurinta kaji” share ta yayi tare da saka kai zai wuce.

“Nace ka kai ni wurin Ammyn ba zaka kai ni don Allah” ta fada da Æ™arfi, tana hada hannunta wuri guda.
“Don Allah!”
“Faisal!” Ummin ta kira sunan shi.
Kallon ta yayi tare da jinjina kan shi, gyada mishi kai tayi tare da lumshe idanun ta.
“Muje” ya fada a takaice, da sauri ta bi bayan shi, suka tafi har waje, shiga bayan motar tayi tana raba idanu, ya tadda motar suka bar gidan a guje.

Suna fita Ummin ta sauke ajiyar zuciya, kafin ta ce.
“Yaran da mahaifiyar su, abin tausayi ne baki daya abinda yasa Uwar take ta gudun auren su kenan, gani take kamar abinda ya faru da babbar yarta zai iya ruguza rayuwar sauran yaran. Sai gashi duk da Æ™oÆ™arin ta na hana faruwan haka , kome ya lalace a sanadin ita Jamilah na tausaya mata sosai sabida tai kokarin kare rayuwar Yaranta gashi nan kome ya.”

“Ƙaddara kenan ita dama can ba a guje mata.” Inji Maman Bilal, Ta fada a hankali, tana kallon Yaran da suke ta Hamma,
“Kuje ku kwanta.”

   Taka birki yayi tare da kallon ta, ta mudubin motar yana faɗin.
“Idan ba zaki min shiru ba wallahi zaki fita” ya fada da Æ™arfi yana dukar sitiyerin motar. Cak ta hadiye kukanta, tana me jingina kanta tayi shiru, har suka isa asibitin. Suna shiga cikin asibitin ya kaita har dakin da Ammyn. Zama tayi tare da kura mata ido, juyawa tayi taga ya fita. Da gudu ta fita, yana barin asibitin. A guje ta bishi tare da rungume shi. Cikin shashekar kuka. Jan numfashi yayi tare da janyo ta gaban shi yana kallon yadda take kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button