NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

**
Bayan wata uku.

Shigowa Khalil yayi da sauri, ya same shi da Jamilah da ta kawo mishi ziyara.
“Yallabai an samu matsala anyiwa ma’ajiyar kamfani kutse fa” kallon shi yayi tare da cewa.
“Kamar Ya? Maza kira Faisal” kafin nace me har an Faisal ya zo,tun safe ake aikin har Jamilah ta gaji ta tafi, shi su kan suna fama da computers din su.

  Wajen karfe uku suka wuce shagon su Rubi cin abinci,  bayan sun yi odar kome ta kai musu, dake baya ya nunai bata lura da shi ba, tana cikin sakawa taji Faisal yana cewa.
“Amma nayi mamakin kai hari da aka yi kai tsaye kamfanin nan kuma a rasa me gyarawa”
Har na wuce sai na tuna na bar Abraham bai da lafiya, koda muka kaj shi asibiti wai aiki za a mishi a kodar shi.
Ana niman dubu dari biyar,  kamar zan musu magana sai na share na tafi kar su yi tunanin cutar su zan yi, ana haka ma’aikatan kamfanin suka shigo suma suna maganar, akwai mutanen da na saba da su, dan haka na koma gefen su na ce musu.
“Meye ya same kamfanin ku?”
“Wallahi ana gab da rusa kome na kamfanin”
“Hacking kenan?”
“Eh wllahi kuma an ce ba karamin asara xa ayi ba”
“Nawa zaku biya ni ba gyara muku?”
“Ke bafa abin wasan yara bane.”
“Kunsan irin baiwa na ne? Kawai ki fada min nawa zaku biya ni”
“Ok ai ga ogan can”
“Yallabai ga wata zata gyara wai nawa za a biyata” kallon juna suka yi da Faisal ya ce mishi.
“Tazo ta gyara sai a biya ta”

Jin haka ya sani babu shiri na ajiye tiren, na bi bayan ma’aikatan, zuwa kamfanin,anan na zama yar kauye har zuwa office din computers É—in. Kallona suka yi ta yi irin ba zan iya nan ba,ina zama na kura mishi ido murmushi nayi kafin na mikar da hannuna, kafin na kalli agogon na ce musu.
“Ku duba min karfe nawa? Bana son na wuce karfe hudu da arba’in ban bar ikeja ba”
“Uku da talatin da biyu” lashe bakina nayi tare da kurawa computer din idanu, sannan na shiga amfani da hannuna baka jin kome sai karan keyboard din laptop din, sai da na nutsu sosai na gane anyi amfani da karamar laptop ne na kamfanin Hp Microsoft.

    Karfe hudu da minti biyar na mike ina faɗin.
“Ku duba kome na gama”
Ganin ya nuna kome ya koma mazaunanin shi, na ce musu.
“Toh maza a biya ni” jagora suka min har office din Ogan su,  muna zuwa yana fita da sauri shi da mutumin nan kamar xan yi kuka haka na hakura, na dawo shago mu.

  A can surulere.

Anan aka kai Hannan watanin baya, kuma tunda aka kai ta wurin ake tambayar ta meye alakar shi da wannan kudin da aka bashi matar nan tayi kunnen kashi su kuwa suka kwace kome da yake nata kamar da daga waya kome da zai sadata da waje suka hanata, kuma suna son su mata azaba amma taki.

   Shi kuma anan wani aiki ya dauke hankalin shi haka yasa suka tura Mishi sakonnin abinda yake faruwa, ga matsalar niman Yarinyar Paris, ya sha kan shi. Dan haka bai kuma bin ta kanta ba, sai da Thomas ya kira shi. Sakamakon gaya musu da tayi cewa.

“Ku gaya mishi cewa a kullum sai ya fuskanci barazana a rayuwar shi. Dan haka ku gaya mishi yazo ina son ganin shi idan yaki kuwa zai ga abinda zai dame shi”

     Suna gaya mishi kuwa shine ya fusata ya zo, sakawa yayi a bashi Coffee.
“Kika ce me? Zan na fuskantar kalubale a kullum gaya min a ina na samu kudin nan?”

  Dariya tayi mishi sannan ta ce mishi,
“Na zata baka tsoron mutuwa ne? Toh sai gashi kazo daga gaya maka haka. Ka sake ni domin rike ni da kake..”  buga hannun shi yayi tare da cewa.
“Ke”
“Kai Yaro ne, ka manta lokacin da ka saka hannun a takardan ne? Ko ka manta ko ka manta lokacin da ka zab’i purple team ne? Haka ka saka a kunna maka wayata ka duba kan gallary na, akwai hotunan yaran da aka saka hannun aka fitar da su safara da fatauci,kasan yadda ake yaki da kudirin majalisan wakilai. Sannan ana gab da kaiwa majalisar dattijai, daga nan a mika shi Majalisar koli su kuma su duba a mikawa shugaban kasa ya saka hannun. Sannan a mai da shi ga alkalai, su kuma su mikawa lauyoyin sannan aja mai da shi dabtarin dokar hana safara da fatauci. Wow haka yayi kafin a saka dokar duk me hannu a cikin shi zai fuskaci mutuwa ko zaman gidan kaso.”

Dariya ya saka mata, sannan ya juya abin shi ja fita yana gaya mata.
“Anan zaki dawwama idan aka fitar dake toh tabbas kiri-kiri zaa wuce da ke” yayi ficewar shi kiran shi taya ya juya ta ce mishi.
“Kazo”

**
Tunda na isa gidan, na samu har Ayola ya zo.
“Rubi ya akayi kin je asibitin” jiki a sabule na zauna kafin na mikawa Mama abincin na ce mata kayan abinci na ce mata.
“Gashi nayi wani aiki ban sani ba ko zasu biya ni kamar yadda na bukata”

Na ina mika mata kayan.
“Amma kizo muje asibitin” duk da na gaji haka na bishi.

   Lokacin da na ga Yaron sai da naji kamar na cire ciwon a jikin shi na maida jikina.
“Ayola bari naje na dawo” na fada tare da fita da sauri,  dakyar na samu motar da zata kai ni, har wurin aikina.

      Lokacin gari ya fara duhu, koda na isa na samu security service din kamfanin samun su nayi da cewa.
“Ina tambaya a ina gidan me kamfanin nan yake?” Dake sun san ni kuma sun san aikin da nayi yau, suka ce min.
“Kiyi hakuri yana cikin amma idan ya fito zamu gaya mishi dan jira”  haka na zauna tun karfe tara har wajen sha biyu saura ya fito tare da wani, ina ganin mutumin da yace na zauna yayi mishi magana, amma ya share tare da gaya mishi ko me oho yayi tafiyar shi.

   Akan idanuna ya fita hawaye ne ya zubo min, na gyara zaman Jacket din jikina na fara tafiya ta, domin baki daya raina a b’ace yake.

      Gashi nayi dare ga ba biyan bukata, haka yasani cigaba da tafiya domin nasan garin ba zai rasa nasaba da yan iska ba, tunda nice na kawo kaina. Nayi dogon tafiya har kusan karfe daya na dare, kafin na isa babban titi anan naga ikon Allah, kamar motar mutumin kamfanin can ne a kife a tsakiyar titi, ga wasu mutane kewaye da shi, dauke da karafuna, kamar na dauke kaina nayi tafiyata tunda ban ga kome ba, sai na tuna Mama Estar tana cewa.
“Addinin Kirista ya koyar mana da tausayi da jin kai karka ga wani a halin taimako ka wuce shi Allah ba zai yafe maka zunuban ka ba, sannan idan har da halin ka taimaka mishi”

Tsaki nayi tare da isa wurin na dauki,  wasu kananan duwatsu, na cire dan karamin dan kwalin kaina, na nad’e duwatsun, sannan naja zip din Jacket dina na rufe har wuya kasancewar wuyar shi high na neck ne, ya rufe min fuskana kwayar idanuna ya rage,   a cikin minti biyar kacal, na isa wurin.
Tab’a wanda nake bayan shi nayi, yana juyawa na dauke shi da dan kwalin. Nan kuma fadar ya dawo kaina. Kafin kace me mun kaure da azababben fasa, wanda shi kan shi da yake cikin motar yana zubda jini sai da ya sake jijjiga kansa.

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/4/22, 16:02 – Nuriyyat: 56

Lallai so yake yaga waye haka! Waye ya kawo mishi dauki a daidai wannan lokacin, amma ina domin ta bugu sosai.
A wajen kuwa fadar da nake dasu, ba irin shi suka sani ba, sai da suka ga ba fara neman hanyar nakasa su, suka gudu. Tare da shiga cikin motar su, da gudu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button