NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

       Shigowar Ammyn falon da tire wasilah ta mike tare da amsar tiran.
“Bana ce idan aka yi bako kina bamu wuri ba?” Rau-rau tayi da idanun ta kafin ta ce mata.
“Kiyi hakuri Ammyn” ta fada bayan ta ajiye mishi tiren, a hankali ta dauki qur’anin ta bar falon. Zama tayi tare da shiru wanda ya sa shi d’ago kai ta ce mata.
“Kiyi hakuri, dan matsala motar makarantar su ta samu” kura mishi ido tayi sannan tayi murmushi.
“Mamarka tana nan?”
“Eh” ya bata amsa bayan ta ajiye kofin da ya zuba ruwa a cikin shi.
“Ka tambaye ta wani yanayi take ji idan har yarta mace bata dawo daga makaranta da wuri ba?” Girgiza kai yayi sannan ya ce mata.
“Tana da Asthma bana son ko min girman É“acin rai ta fuskanta domin kar ya tab’a mata ciwonta”

“Kasan yadda uwa take ji kenan?” Gyada mata kai yayi tare da cewa.
“Kiyi hakuri.”
“Ba zancen hakuri bane, na hango farin ciki a tattare da ita ne, lokacin da ta fito daga motar ka,  a kwayar Idanunta na fahimci tana tsoron fadar da zan mata, amma sallamar ka na shigowa cikin gidan nan ya sani fahimtar wani abu!” Mikewa tayi tana kallon window dakin su.
“Ban sani ba ko zan iya shanye É“acin ran da na shiga a baya, ko zan kuma fuskarta wata kaddaran. Da matukar ciwo da zafi sosai, ba kowa bane zai gane yadda nake ji, idan na roke Alfarmar akan ta zaka iya min? Don Allah ka fita a rayuwar ta. Ka tafi don ka bar min rayuwar ta cikin salama”

Kasa magana yayi yana kallon ta cikin girmamawa.
“Ban san me yasa kike korana a rayuwar ta ba, sannan nima ba wai nazo cikin rayuwarta  na bata mata Bururikanta bane, kawai abin yakan kasance ne a lokacin da baka shirya mishi ba, amma zan yi yadda kika ce na gode” ya fada yana me mikewa daga kujeran.
“Zan tafi”
“Allah Ya tsare, karka ga laifina ba kowa bane zai iya jure rashi da Æ™addara, sai wanda Allah ya bashi damar rungumar haka, hawayen uwa, hawayen Y’a hawayen Yan uwa, ka tab’a ganin haka? Hmm” a sanyayye ya bar falon yana jin wani irin babu me girma a zuciyar shi me yasa ta nisanta shi da Rahmah? Sannan bai ga wani abun aibu a wurin Rahmah ba.

Wannan shine abinda ya faru. Koda Rahmah tazo makarantar a ranar aka sauya mata unifoam, dake Ammyn ta mata nasiha, tana ganin Faisal taki kula shi, sai da ya wuce ta juya tana bin shi da ido, kalaman Ammyn suna dawo mata daki-daki.
Yaron nan ya fi karfin ki, Yaron nan ba sa’anki bane, karki kai kanki inda Allah bai kai ba, Karki janya mana abin gori! Daga yanayin shi zai tabbatar Miki ba sa’anki bane

Hawaye ne ya zubo mata, ta goge, koda aka kirata akan case din ta, kukan da take yi ne yasa Bilal sallamar ta. Kallon juna suka yi shi da Bilal bayan an fito daga Office din Humaidah. Suka hangota zaune ita É—aya hannunta rike d popcorn. Sai gwagwanin coke.
“Ka fada soyayyar ta baka sani ba ko?” Bilal ya tambaye shi, yana kallon ta.
“Ban sani ba Bilal, mahaifiyar ta ta roke ni na rabu da Yarinyar!”
“But why?”  Bilal ya tambaye shi yana kallon shi.
“Ban sani ba, sai dai ko zaka raka ni wurinta.
“Akan me yasa?”
Shiru yayi kafin ya juya ya ce mishi.
“Namir Adamu Abbas Jikamshi yasan wani abu akan su zo muje”
“Muje” ya fada tare da bude motar Bilal zai shiga daga bayan su aka ce musu.
“Oppa mu zo tare ka É—auki tailed dinka zaka tafi dashi” juyawa yayi ya kalli Faisal wanda ya gama cika ya batse.
“Ungo ki tafi zan zo”
“Motarka?” Ta tambayi Bilal,
Ajiye mata yayi a kan motar suka shiga na Faisal suka bar makarantar.  Asibitin JF suna isa, Namir yana fitowa daga cikin asibitin zai tafi gida.

Ganin Bilal sai da zuciyar shi ta buga, dan haka kamar ya juya da sauri, sai kuma ya dake, kallon juna suka yi shi da Faisal.
“Yawwa dan duniya kai nake nima, ina zaka yanzu?”
“Gida” shigo muyi wata magana me muhimmanci.” Babu musu ya shiga amma yaki sake jikin shi da su, kallon shi suka yi lokacin da ya zuba musu ido shima.
“Meye ka sani akan Yaran nan da muka tab’a hadu lokacin da aka kawo Ummi Asthmar ta ya tashi?”  Shiru yayi yana kallon su, kafin ya hadiye yawun ya ce musu.
“Yayar an yi rape din ta, and daga baya nake jin labarin karamar su tab’ata sanadin ciwon Yayar su” shiru motar ya dauka. Dafe goshinsa yayi sannan ya ce mishi.
“TOH wannan shine abinda ya saka mahaifiyar su tsoron duk wanda zai kusance su?”
“Eh nima nayi kokarin haka, amma abun ya ci tura dan dole na hakura”
“Ok mun gode”
Fita yayi daga motar yana jin kamar an kunce shi daga daurin da aka mishi.
“Baka lura da wani abu ba?”
“Kamar Ya?” Faisal ta tambaye shi,
“Namir duk lokacin da zamu hadu sai naga tsoro da firgici a kwayar idanun shi akwai wani abun da yake faru ne?”
“Anya Bilal don Allah ka koma aikin tsaro mana, mutum sai bin diddigin mutane yake, kamar wanda yake aikin tsaro ba halin mutum ya É—an sauya sai ka ce bai da gaskiya.”

Murmushi yayi tare da kauda kan shi suka bar asibitin.
“Ina son mace!”
“Kamar Ya? Kana son mace?” Ya mai da mishi tambayar shi.
Kallon gefen hanya yayi, sannan ya ce mishi.
“Da gaske ina son mace Bilal, ina son na ajiye matar kaina, Bilal ko babu soyayya ina son matar da zata dauke min hankalin. Yarinyar nan itace dai-dai dani.”
“Ba zan iya maka ba, domin alamarin ka ya fara fin karfina, idan aka cigaba da haka tabbas zaka iya danne yar mutane.”
“Subhanallahi ban tab’a tunanin haka ba” ya fada yana kallon hanya, har suka isa office din Ummin.
“Don Allah ka fahimtar da Ummin mu mana”
“Akan me fa?”
“Akan ina son aure”
“Toh zan gaya mata kuwa” suka fita a tare ganin motar shi a can ya fahimci Nadrah tana office din,  shiga ciki suka yi suna hira. Har office din Ummin tana tare da Nadrah. Zama suka yi tare da kallon ta.
“Sannun ku, kun tafi makarantarta kun zartas da abinda yayi muku ko ku gaya min? Ita Yarinyar da ka zaka Guardian dinta yar waye?”

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 39

Kallon Bilal yayi yana sosa goshin sa, kafin ya ce mata.
“Ba yar kowa bace mareniya ce, da take da Uwa ta gari. Yarinya ce da tsoron Allah da tausayin Mahaifiyar ta ya girma a zuciyar ta. Yarinya ce da take gudun duk abinda zai shiga kunnen mahaifiyar ta, kiyi hakuri sati Daya da ya wuce na shiga Tokyo na sace ta. Abinda ya fada min yasaka ni jin ba zan iya rayu babu ita ba. Duk abinda xan mata na mata amma kar na saka ta tarasa mahaifiyar ta. Ummi niyyata na tambaye ta abinda tayi min da saninta ne, amma sai ta gaya min idan na mata wani abu Ammynta zata iya mutuwa.” Share kwalla da yake gefen idanun shi yayi sannan ya mike.
“Idan har mahaifiyar da tana ji tana gani aka cutar da Yaranta biyu, bata kare rayuwar su domin cimma nasarar su ba, babu amfanin ta rayu wannan shine abinda Mahaifiyar ta ta gaya min jiya.”

“Toh ka hakura da ita mana, tun da mahaifiyarta bata sonka.” Inji Nadrah, Murmushi yayi me ciwo kafin ya ce mata.
“Ba soyayyar gaskiya kenan, soyayyar da zaka iya tafiya kabar abinda kake so bane, soyayyar da zaka iya bada rayuwarka domin abinda kake so shi ne soyayyar gaskiya, ba wai ina mata soyayya shirmen banza bane, ina mata soyayyar da zan ajiye ta a wuri guda ne har karshen rayuwata, so nake na mallaketa ni daya na babu wanda ya isa ya zo inda take. Ba soyayyar na kwanta da ita na gudu bane, soyayya ce da nake son duk lokacin da nake tare da ita taji a ranta she deserves to me, ba wai inta bata wahala ba yadda sai ta tsane ni a’a ina son na reneta ne kamar sarauniya. Ba”
“Toh meye ma’anar wannan confess din?” Inji Ummin, ta dakatar da shi,
“Ina sonta ne!” Shiru yayi yana kallon kasa, kafin ta ce mishi.
“Ka ajiye maganar ta a gefe kayi yadda mahaifiyar su ta ce,, domin haka ne zai saka ya kara ganin ka a mutumin kirki, idan kuma kayi karya mata doka zata kalle ka ne a matsayin wanda bai san ciwon kan shi ba, ko ta baka mace ba zaka iya rike mata Y’a ba, amma idan kayi hakuri sai ka ga Allah ya baka ita” inji Ummi tana kallon shi yadda ya damu sosai, tasan yayi hakuri ace matashi irin shi babu mace ai akwai abin dubawa. Mikewa Nadrah tayi tana kallon, jikinta a matukar sanyayye ta ce musu.
“Zan tafi gida”
“Toh ki gaida Yaya Turai” kallon Bilal tayi da ya mai da hankalin shi kan laptop din shi.
“Oppa”
“Hm”
“Zan tafi”
“Allah ya tsare” ya fada mata ba tare da ya kalle ba, jikinta a sabule ta bar office din.
Cikin tashin hankali da damuwa, domin ta san duk abinda Faisal ya fada gaskiya ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button