NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

   Dama Bilal yana fama da sharrin cikin gidan,  sai gashi cikin ikon Allah tare da hadin gwiwa na kakan shi ya samu wannan aikin, har na tsawon shekaru.  Bayan yayi aure ya samu matsala na kashe mishi mata da ake wanda a yanzu haka yana shirin kafa hujja ne na karshe, sai aka samu matsala, matsalar da aka samu United State ta fahimci Korea da Nigeria suna da wata kyakyawar alaka, haka ta fara zargin ko akwai wani abu sa suke kullawa ne akan makamin nukiliya, sai shi da kan shi ya tura niman taimakawan kasar rasha, ita kuma jin irin lambar yabon da yake samu ta dauke shi a matsayin wanda zai bawa Agency din su horo.

   Bayan yayi aikinn tsawon wata biyar, ya dawo Hannan ta kawo mishi takardan ya basu motar kamfanin shi su fita da kaya, a cikin takardan ya sake samun karin haske akan ai za a fita da gurbatattun kaya ne, dama tun kafin tazo akwai wasu manyan jami’an tsaron yan team din Bilal din da suka samu labarin ta hanyar yan leken asiri.

    Bilal ya saka hannu tare da zab’an purple team, domin saka rai sai da aka turo mishi hoton Yaran yaga Rabi’atu, haka kawai yaji ba zai iya barin Rayuwar ta haka ba, dan haka ya samu Manyan spy din su na kasashen da ake Safaran mutane ya tura musu hoton ta.

         Ya raba abin kashi Uku zuwa hudu ne, kafin nan ya sayi Aunty Blessing, wacce asalin sunan da Mansurah Abdul Salam, ita ta kai Rabi’ah har Red line life orphanage,. Ta mika ta ga Clara, wacce sunan Tamara Smith, ita kuma ta kai ta ga Mr Andrew Cuomo, shi kuma Ya bawa mace ta karshe Jessica Simpson. Already sun san da zaman ta, sannan duk abinda aka mata an shirya shi ne, ba wai sabo bane. Juriyar ta hakurinta yasa shi kara zage dantsen bata kariya, Rabi’ah tana raye ne amma Bilal shine inuwar ta.

   Duk inda ta kwana ta tashi yana sane da ita kuma yana sane da inda zata fada, Bilal bai yi kasa a gwiwa ba,  har sai da yaji labarin Mutuwar Jessica Simpson. Dan haka ya saka aka kama Kelly Clarkson.

     Ganin itama jar wuya ce aka sake ta, dama ana niman Nicole Brohna, kuma aikin Bilal ne, sai dai idan har namiji ko jami’an sirri suka kashe Nicole America zata iya cewa ai dan kasar ta, bayan sun san irin ta’addancin da yake da safara da watsa kwayoyin da aka haramta ga jama’a. Haka bai musu ba suka kare shi domin akwai hannun wasu manyan mutane a cikin al’amarin shi.

Kwatsam sai ga rabi’ah ta kashe shi, daga haka ta gudu, anan jirgin aka yi ta ta kare domin shima yana cikin jirgin da mutanen shi. Har inda aka kuma tamkar Rabi’ah aka wurgata cikin ruwa, aikin shine bayan shima ya rufe tarihin Kelly Clarkson, da Priyanna tare da Mr Andrew Cuomo.

Domin duk wani safara da ake suna da kyakkyawar connection da shi, yana sane da cewa tana cikin Paris ya dawo gida, yana kara bibiyar ta. Gayyatar da aka yi tare da turota, duk yana sane, da tambayar ta da yayi tare da niman kwanciya da ita duk tsarin shine, sai bai tab’a kawowa tab’ata da yayi a wannan daren sai tab’a rayuwar shi ba sai yanzun da take kara shiga jikin shi, sannan yana sane da ta dauki bayanan shi, koda ya koma wurin Madam Tola ta bashi SD din da ta bata babu kome a cikin shi empty card ne.

Dan haka ya bazama niman ta, kafin nan suma mutanen da suka bada aikin sun sami labarin Bilal ya tafi gidan Madam Tola, haka ya sasu kin zuwa dan sun san zai bibiye su.

    Sannan babban dalilin da yasa yake niman Rubi a lokacin da ya koma ita daya ce,ta kutsa datar kamfanin shi, kuma daga ita sai ya kasance mutane dayawa suna kutsa  kan su, ana haka . Ta dawo bayan yasamu labarin zuwan ta, bai bibiye ta sosai ba domin ya fahimci itama tana sane da za a bibiye ta.

     Dan haka ta kuma shiga kamfanin shi har ta shiga jikin Faisal wanda yanayin kamar da take da su Rahmah ya yarda da ita, amma ko zuwan nan aikinta tazo yi ba wai wani abu ba.

Wannan kenan. A dawo labari ( karku girgiza akwai wasu bayanai gaba 🤣🤔 kusan dukkan inda na tafi zan dawo)
“Kin zata haka kawai take yawo bata da galihu. Tana sane da ke Yar uwarta ne domin tun a roma ta samu lafiya. Bayan tayi fama da cutar Phobia. Idan har a yadda take duniya tasan tana raye, ke baki isa ki rayu cikin salama da kwanciyar hankali ba. Ni kaina dole nake koran kowa a jikin ta.

  Domin a jikinta akwai na’uran da yake bayyana motsinta, dan haka ki kiyaye kan ki da shiga harkanta. Idan kina ganin kamar karya ne bata san wacce ke ba. Kalli Wannan abin” ya daura mata tap akan cinyar ta. Fitowar Rabi’ah daga gidan su tana kuka. Bayan ta durkusa a bakin get.

“Ranar da aka kawo miki hari a cikin asibitin ba jikamshi GRP bane kadai ke son ganin bayan ki, akwai wani da yake son ganin bayan ki me ya haÉ—a ki da  Alhaji Yau Me Nasara? Kinsan waye shi?  Toh da harsashin kanwarki ta nime shi kalle shi duka daya ta mishi yana cikin coma.

     Idan ina kallon kiriniyar ta burge ni yake domin ta iya fuska biyu,  Yaron da kika turo ya firgita Rahmah ta karya shi yana nan sai dai mu mishi fatar sauki, Ke hatta kudin Yan uwanki da kika tab’a duba asusun ki. Ruwanki ki kama Aaman ruwanki ki zauna ki kare rayuwar ki ita kuma ta rayu. Wannan matsalarki ce ba ta kowa ba, amma ko kwarzane kika mata wallahi ke da kanki zaki roki a kashe ki domin Yarinyan kowa yana da saka rai akan ta. Kinsan ni da Alman cousin ne, shine mika saka shi ta bata giya. Wannan ya zama last warning tsakanin mu idan kika kuma, da kaina zan baki abinda ya dace dake, na hore ta yadda ni daya zan sarafata karki sake raina ya b’aci da abinda kike shirin aikatawa ki tauna harshen ki”

   Daga haka ya bude mata kofar, kallon shi yayi ta fita.
“Ina son ka” ta furta a hankali, hawaye na zuba mata.
“Wallahi gaskiyar ka ya kuma kara min jin kaunarka” wani irin tausayi ta bashi yana kallon ta. Yayi sannan yace mata.
“Ban tab’a kaunarki ba, nayi miki kome ne Sabida Allah da kuma Rabi’atu,  tun daga lokacin da aka sayar da ita har zuwa yau ban daina duba al’amarin ta ba. Domin Æ™arancin shekarunta ya sani bibiyarta.  Ita kanwarki ce amma kiyi kokarin kyautatta mu’amalar ki da ita, dan tana sane dake.”

“Kana son ta ne?” Kallon ta yayi tare sake wani malalacin murmushi ya ce Mata.
“Daga ranar da na fara sonta, ba iya kariya zan bata ba rayuwata idan ta bukata zan bata, karki kai ni ga aikata haka”

“Toh me yasa? Meye haka? Meye ta fini da shi?” Ta tambaye shi a masifance.
“Sabida baki da ce dani ba, baki da ce da kowa ba, Idan har Aaman zai auren ki yayi babban kuskure da zai aureki dan baki dace da shi ba, kina da mugun son kai da zuciya! Fitar min a mota.” Ya daka mata tsawa, a hankali ta fito.
“Zan fita, amma na rantse da Allah sai dai dukkan mu murasa. Kuma ka saka Idanu sai na baka mamaki”
“Kina wasa da rayuwarki.” Ya fada lokacin da ya fito daga motar.
“Ba xan reni akuya ta dawo min a matsayin zaki ba, idan har zan iya tsayawa a gaban yan uwan Ubana domin kare kaina who are you da zan ji tsoron kashe ki, daga yau har zuwa ranar da zaki fara haukarki na baki damar janye kome naki a cikin Jikamshi Group idan kuma kika sake na waiwaye ki, abin ba zai mana kyau ba, mahaukaciyar banza kin zata ita Rabi’ah irin ki ne da zatabawa namiji jikinta, shima Alman din ya kuka sa sanin sai na ci Uban shi dani take zancen. Hannun da ya tab’ata da shi sai na karya mishi ita kuma ki kiyaye ni Karamar karuwa kanwarki ma hanaki magana tayi da kika je rusa mata gidan da take basu ruwarta ki yarda ki min Iskanci na take banza irin ki. Na take banza.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button