WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
Yaja tsaki tare da wucewa cikin motar shi. Bude motar yayi cikin wani mugun yanayi ya wani irin kutsa cikin motar kafin ya dakatar da ita ta fada jikin shi.
“Wallahi idan zaka kashe ni, idan zaka yi kome da ni, na yarda kawai ko min kashin sa kaso Ni, duniya tasan cewa kana sona, don Allah Gong Yoo ka soni”
Ture ta yayi tare da dafe goshinsa, yana faÉ—in.
“Ke wacce irin mutum ce? Ban gaya Miki bana son ki ba? Bana son ki, bana kaunar ki, kawai nayi haka ne dan tausayin ki”
“Bilal kaso ni kome kashin sa zan tafi farin ciki. Kai ko a karuwanka na yarda ka É—auke ni. Wallahi na san nayi rayuwa a bayan abinda ya faru dani, amma na rantse bayan abinda ya same ni, ban tab’a hada shimfida da wani namijin ba, ka yarda dani ita kuwa nasan maza babu iyaka sun yi yadda…”
“Ko itace gidan karuwai haka nake jin xan zauna da ita, balle babu wani aibu akan abinda kake so maza fita min a mota kafin na miki dukar rashin arziki.” Ya fada yana nuna mata hanya.
“Ina son ka Bilal” ta fada cikin shashekar kuka.
“Wallahi ko zaki mutu bana sonki, kai ko a sahun karuwai na ba zan dauke ki ba balle a cikin sahun mutanen da nake so”
“Bilal karka mai wanke muguwa” ta fada cikin matsanancin kuka.
“Dama can da muguntarki, bana sonki” ya fito daga motar ya bude mata motar yana kallon. Haka ta fita tana kallon shi ya tafi ya barta.
“Wallahi billahi azim dai na raba ka da Rabi’ah” ta fada da Æ™arfi, tana kuka kamar yarinya karama,
….
Daga nan gidan Ummin ya wuce, tun daga bakin get kowa yasan ran shi a b’ace yake, yana shiga cikin falon bai damu da suwaye a falon ba, ya shiga kwallon da Alman, daga Ummin har Faisal babu wanda ya ce mishi Meye ya faru, abin dariya Shi kan Faisal matar shi da take tsakiyar falon yayi kokarin janyowa, kar su taka mishi ita, cakumar kwalar rigar Alman yayi yana huci.
“Ka sake na kuma gamuwa da kai, a tare da Rubi sai na karya maka kafarka wallahi billahi azim, duk wani namijin da zai kuskure ta sai dai Uwar shi ta haifi wani ba dai shi ba….
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/11/22, 23:48 – Nuriyyat: 70
“Sai da na gargade ka, karka yarda wani ya hada kai da kai a cuci wani amma kai yi kunnen uwar shegu ka amshi tayi Jamilah ka san wacece ka cutar? Wallahi daga yau kayi na farko kayi na Æ™arshe” ya fada da Æ™arfi, komawa gefe yayi ya zauna sai huci yake.
“Sau biyu na mare ta, akan giyar da ka bata, dubi jikina?” Ya fada da Æ™arfin gaske, kafin ya mike ya fita bai kula kowa ba, haushi yake ji kamar ya daki kowa.
 Ko inda yake babu wanda ya kalla.
“A ba yau nake gaya mishi ya fitar harkan Rubi ba, amma ya ki ji. Duk abotar mu da Bilal kiri kiri ya ce min baya son ya kara gani na da ita, kasan ba Æ™aramin matsayi ya bata ba, amma ina dakikin Æ™waÆ™walwar ka bai baka haka ba.” Inji Faisal,
“Allah ya shirya ku” inji Ummin dan takaicin su ya cika mata rai
“Jamilah!!” Rahmah ta kira sunan ta a hankali, kafin tayi shiru bata kuma magana ba.
**
Tunda ya fita gida ya nufa, yayi wanka sannan ya tafi masallaci, bayan ya dawo ya nufi gidan su Rubi, tun karfe tara na dare yake Unguwar har karfe biyu na dare sannan ya bar unguwar.
…
Washi gari da ciwon kai na tashi, shiryawa nayi cikin Arabia gown, na rufe kaina. Kowa na gidan kallona yake,ban wani samu ba, na wuce aiki.
Ina shiga cikin kamfanin, na hango shi shima ya sauka a motar shi.
“Mr Jikamshi!!” Na kwala mishi kira, tsayawa yayi,da sauri na isa wurin shi.
“Nayi mafarkin ja mare ni jiya Meye gaskiyar al’amarin?” Na fada a fusace. Dauke kai yayi tare da kallon gaban shi,. Gaban shi na sha tara da cewa.
“Gaya min gaskiya ka mari ni ko?”
“Kin ga bani hanya na wuce” ya fada, leka fuskar shi nayi tare da cewa.
“Sai ka gaya min gaskiya”
“Bani hanya na wuce” ya fada a tsawa ce.
“Toh” na fada a hankali, wucewa yayi har sai da na bari ya kusan kurewa gani na na isa wurin shi da gudu na bangaje shi.
“Ohhh” ya fada.
“Ke” na juya ina kallon shi.
“Meye hadina da kai?”
“Zo nan” ya fada min, tsaki yayi na bi bayan shi, har office din shi, na shiga. Tunda na shiga masifa yake min kome na tab’a sai ya min magana, haka ta sashi magana. Karshe da ya gaji, bude kofar yayi tare da nuna min hanya.
“Babu inda zani.”
Tsawa ya buga min, na tashi a inda nake zaune na koma saman table din shi na zauna, irin zaman Yogo. Dafe goshinsa yayi.
Baki daya na hana shi aiki, ina yi ina tsokanar shi, karshe da ya gaji fita yayi ya bar ni a office din, Ashe sallah ya tafi, yana dawowa bai tsaya a wannan office ba, suka shiga meeting.
 Koda ya shigo ya same ni ina barci, coat din shi ya cire, ya daura min, gyara kwanciyata nayi ina jin wani irin dadi, tsayuwar yayi na bude idanuna.
“Karka sace min kyauna” na fada cikin barci, tab’e baki ya cigaba da aikin shi.
  **
Zan iya cewa bani da wani dogon matsala, sai ta wasu mutane da kullum nake gani suna bibiya ta.
Ranar Talata ina bakin hanya, ban san ya akayi ba kawai na tsinci kaina da kiran Yallabai Faisal.
“Sir akwai wasu mutane da suke bibiyata, so ban san ya zan yi ba”
“Ok ok” ya fada a rude, kallon su nayi lokacin da dayan ya zagayo, saka min tsinin wuka yayi,
” Meye kuke so?” Na tambaye su.
” Shiga Bus din can” babu musu na shiga motar muka bar unguwa ganin ina kallon hanyar, kawai sai ji nayi an watsa min hoda, kwanciya nayi tare d jin ba zan iya kome ba.
“Ok Madam gata nan”
Haka suka isa wani gida, daga nan suka dauke ni zuwa cikin gidan. A hankali aka shiga dani.
  Kwantar dani suka yi a tsakiyar falon.
Kafin suka zuba min ruwan sanyi, bude ido nayi a hankali , ina kallon su. Jamilah ce zaune, ta shi nayi itama ta taso zuwa gabana.
“Auta kin tashi?” Da sauri na kura mata ido murmushi tai tare da cewa.
“Daniel bani abincin nan”
Abincin ya kawo mata, ta saka mana ni da ita.
“Zuba mana ruwa kunce ta kafin na ci Ubanka” da sauri ya kunce ne, sannan ya kawo mana ruwan,kallon ta nayi bakina yayi nauyi.
“Ki ci abincin, tare zamu ci” ta fada min tana murmushi. A hankali na fara ci, kamar yadda take ci itama.
“Da fari Baba Haliru, sai yan uwan Abba suka kai ki karuwanci.” D’ago kai nayi da sauri.
“Rabi’atu Ishaq DaÆ™ayyawa, yar shekaru goma sha shida da watanin, ko? Rebecca Uchanna a bayan barinki gida.
    Nasan abubuwa dayawa Kan ki, after Long journey kin sake Show up again. Inda kika nisanta kanki daga kowa, har uwar da ta haife ki” dunkule hannuna nayi, idanuna sun yi matukar jajjur.
“Kina jin hausina ne? Ko kin san waye ya saka hannu aka lalata tarbiyyar ki? Mutumin da baki zata ba, koda yake ba zaki gane waye Jikamshi ba, amma ba damuwa sai dai Na kawo ki ne dan mu ci abinci. Akwai wata mace me Æ™oÆ™arin inganta rayuwar Yaran ta mata. Bata burin da ya wuce suyi farin ciki. Sai dai kashe sanadin mutuwar mahaifin Yaranta nan da kaddaran da ta fadawa Yarta babba mace, da fitar da Yarta karama da akayi karuwanci,yasa tana rayuwa kamar a duniya biyu mabanbanta. Kullum burin ta,shine taga yarta da ta b’ata bayan an ce ta mutu.