WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
Matar nan bata cire rai ba, a hankali ta juyawa daya yar da take buÆ™atar kulawa da soyayyar ta, ita da sauran Yaran ta basu da aiki sai na labarin wacce ta b’ata, ko kuka zasu yi babu ruwan su, akan wancan suke suka mai da wancan saniyar ware.
  A hankali ta taso bayan shima wanda yake nuna kulawar shi akan ta bai damu da ita ba. Bayan wancan tana cikin mawuyacin halin damuwa. Haka bai saka su damuwa da ita ba, uwar nan nasu sai da ta nimawa Yarta ta biyu auren dan gidan mutunci da sanin Ya kamata, suka matsa babbar ta fitar da wanda take ganin shine dai-dai da ita, shima aka yi kutun-kutun aka watsar da auren. Daga Sama Allah ya kawo Babbar Yar miji shin me kike ganin ya dace tayi akan wanda ta samu? Haka bai wadatar ba, sai da ita wancan da ta bace,tana zuwa ta dauke hankalin shi wanda Yayarta ya take haukar so. Ya zaki ji idan kece?”
Cire hannu nayi a cikin abincin, sannan na wanke hannuna.
“Me kike so na ce miki?” Na tambaye ta.
“Tambayar ki nayi”
“Ina tambayar ki ne fa? Kuma kika mai da min tambaya ta”
“Eh toh ba rabo ba dan fari ya mutu ta yiwu shi din kaddarata bane, batun abinda aka mata kuwa a bayyana take,gata ne da jin dadi yayi mata yawa, idan ba haka ba meye ta rasa?”
“Mr Jikamshi!”
“Kin kawo karshen maganarki. Sai an jima”
“Rayuwar Wasilah da ta gudu tabarki ko rayuwar Rahmah me É—auke da cikin wata shida? Ko kuma rayuwar mutane biyu masu tsada!”
Kallon ta nayi ido cikin ido.
“Me kike nufi! Ai na fasa tab’a Sisters Mr Jikamshi ko Ammyn mu..” kai mata wani irin naushi nayi, da sauri yaran suka rike ni.
“Ku cire mata kayan ta, ku dandana mata yadda ake jin zafin rape idan aka yiwa mace”
“Idan suka min ba zai kashe miki wutar da take cikin ranki ba! Meye kike so, na rantse da Abinda nake bautawa zan Miki yadda kike so” kallon tayi sannan ta ce musu.
“Ku kyale ta.”
“Ban amshi tayin dan na razana ba, ko su min fyade ko kar su min ba zaki fasa abinda kika yi niyya ba gaya min meye xan Miki”
“Sharuda uku gare ni, na daya dole ki boye kanki ga Ammyn, ai kin gane. Na biyu ki bar kamfanin Jikamshi, na uku ki dawo min da dukiyar da kika kwashe tare da durkusar da Jikamshi, zan bar kowa ya rayu cikin aminci” shiru nayi ina kallon kasa.
“Babu wani abu ne ba zan iya durkusar da shi ba, duk wani process na mika musu.”
“Bani tap din nan”
Mika mata yayi.
“Live ne, zaki ga kome daki daki.”
Karba nayi Ammyn ce a cikin asibitin, ita da Ya Rahmah. Wasilah tana tsaye zata shiga abin hawa, bilal yana kokarin shiga mota.
  “Ƙaddara tana baka wasu daman a rayuwar ka, soyayya, tattali, kiyayya, duk yadda kayi faffutukar isa wurin haka kaddaran zata cimmaka. Autar mu ta fada mana haka a lokacin tana aji uku na primary shin ba za a bani damar cimma kaddarata bane?”
Kallon ta nayi, tare da cewa.
“Ya Jamilah ba halin ki bane, wallahi nasan wacece ke, please karki bari shedan ya shiga rayuwar ki”
“Rabi’atu kina son jin bad news? Takan waye xan fara? Babu wanda ya sani sai Allah” wani irin kuka ne ya kwace min.
“Wayarki bata da network ba za a tab’a samun ki ba, zaki iya ko sai na aikata”
“Shi kenan! Zan miki duk abinda kike so, but” mikewa nayi tare da juya wuyana, hawaye na zuba min nace mata.
“Zan miki, idan wani abu ya faru da wani cikin mutane nan” dariya nayi mata.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ku bani takardun” mika mata suka yi,ta saka min a gabana.
“Saka hannu”
“Kin manta ban yi karatu, karuwanci kanwarki ta iya”
“Ok ku kawo min stamp” haka suka bata, saka babban dan yatsana nayi na mata yadda take so.
“Kin gama wannan saura wannan” ta daura min laptop din tayi akan cinyata.”
“Saura kaÉ—an ki tafi” kallona tayi tana d’age min gira.
“Dawo min da kudina.”
“Kudin su Ammyn ne kuma tuni na tura musu kowa a cikin account din su.” Kura min ido yayi, kafin tace min.
“Maza kiyi hacking din kamfanin shi.”
 Amsa nayi tun da na fara aikin ban tsaya ba, sai da naga nayi rugu-rugu da kamfanin shi, kafin na tura mata. Murmushin farin ciki tayi, sannan ta ce min.
“Sakamakon rashin mutuncin da kika min na rasa kudina, zan biya akan dayan su.”
“Don Allah kar ki musu kome” haka nayi ta rokon ta, amma bata kula ni ba, har kuka kamar wata mara gata da galihu nake rokon ta, amma ina bata bi ta kaina ba.
“Ku fitar min da ita.”
Baki daya na rikice, Bilal ne ko yan uwana Mahaifiyar mu, har inda suka dauke ni suka dawo dani. Baki daya kai na ne ya sara, kome ya tsaya min Bilal ko Ammyn? Da farko nasan Bilal yana da tsaro, su Ummin basu da me kare lafiyar su da rayuwar su. Dan haka abinda na fara tunanin Ammyn da kawai ita ta dace da kulawa yanzun dan haka na tsari abin hawa tare baki daya na dauke shi drop.
   *
“Madam kamar yadda kika fada gidan Ku ta nufa.” Ya fada mata hankalin shi yana kan laptop.
“Ka gama min da kome? Daga nan har Abuja ka gama kome?”
“Madam an gama kome babu abinda ya rage saura ke.”
“An gama Madam koma kome zai tafi yadda kika tsara” lumshe idanun ta tayi Sannan tace…..
_Kuyi hakuri a weekend nake samun barcin safe wallahi sauran ranaku bana iya barci sabida rubutun ku… Amma inshallah gobe zaku ganni kamar yadda na saba
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/11/22, 23:48 – Nuriyyat: 71
Lokacin da na isa gidan, suma suna isowa. Har suka shiga cikin gidan, waya ta ce tayi kara, dauka nayi na saka a kunne.
“Ai yarinya ba zan tab’a yan uwana kai tsaye ba, Bilal shine abin harina. A ina yake? Waye ya san inda yake? Babu sai ni”
Ta fada tana dariya, murmushi na mata, sannan na ce mata.
“Wow haka ma yayi daidai, kafin nan muyi wani magana mana, Yaranki da kika turo su kama ni, ai yanzu zasu nuna miki wacece. Sannan an ce miki dakikin Æ™waÆ™walwar ki zata iya kama Bilal ne, kiyi lissafi ai mun gama shirin mu kece kika fada cikin tarkon mu. Kwanaki uku da kika basu su nazarce ni, a cikin shi na tattara su na biya su.
Ya Jamilah ba zamu miki kome ba, amma zuwa yanzun ki bude idanun ki domin yan sanda zasu miki sallama the game is Over”
Na fada ina dariya, a hankali hawaye ya sauko daga idanuna, a hankali na bar unguwar, kiran Bilal ne ya shigo min.
“Kizo”
“Ok”
Karfe sha biyu na isa kamfanin, ina shiga suna fitowa. Bude min kofa yayi na shiga. Kallon gefen hanya nake har muka isa office din Yan sanda.
Kallon shi nayi kafin nace mishi.
“Ina niman Alfarmar ka don Allah, ka kyaleta ya tafi”
“Zan barta da sharadin zaki koma musulunci” d’ago kai nayi ina kallon shi.
“Toh na Amince, amma don Allah kar ka mata kome don Allah”
“Ki ajiye maganata ba zan karya ba, babu abinda xan mata, amma zamu yi auren hucin gadi” da mugun sauri na Kalle shi.
“Please babu wani aharadin ne?” Na fada hawaye na zuba min,
“Ok kinsan abinda tayi? Gidan Yari za a kaita bayan kotu ta yanke mata shekara goma a can! Idan yayi miki toh”
  “Toh ka bani kwanaki mana”
“Daga nan har wata uku na baki” gyada mishi kai nayi, tare da fita. A tare muka shiga office din Yan sanda.
  **
Namir.
Kallon File din yayi, sannan ya saka a jakar shi, wayar shi ta ciro. Ya shiga kiran Bilal. Sai da ya kusan tsinkewa sannan ya dauka.
“Kana ina?”
“Gani nan,a office din Yan sanda”
“Ok ma biyo ka ne wurin?” Inji Namir,
“Eh idan ba zaka takura ba”