WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
“Ok gani nan”
**
A cikin office din Yan sanda, Ammyn ce zaune da su Wasilah, ran Rahmah ya gama b’aci. Muna shiga ta kafe mijin ta da ido.
“Ba sai ka had’a kai da wasu kunci mutuncin mu, Yar uwata ce fa, Faisal Yayata ce fa? Ita kuka wulakanta a nan dubi yadda ta kome saboda dukar da aka mata! Faisal duk lalacewar Jamilah ba zaka yarda a wulakantata ba, domin Yayar matar ka ce. Ai ku masu arziki haka kuke”
“Ya Rahmah karki fadi maganar da zaki yi kuka baya. Fitar ta Ya Faisal bai yi kome ba.” Na fada, kauuu Wasilah ta mare ni, juyawa nayi na kalli Jamilah, da take murmushi tana matsar kwallar karya.
“Ammyn waye bai san Bilal muna soyayya ba, Ammyn kin ga ko damuwa da Ni bai yi ba, dake Ita wannan ta gama zubda mutuncin ta a waje ta kwace min shi Ammyn kin san wacece ita?”
“Rabi’atu nace! Itace ta girma haka har tana son ganin bayan yar Uwarta, tuntuni nasan ke ce. Meye shaidana akan kece? Zuwa sau biyu. Kina gyaran farce kina kuka. Ban ga laifin ki ba, ban damu da halin da kika shiga ba. Don Allah ki koma inda kika fito. Idan har haka zai wadatar da Jamilah.” Tashi tayi zuwa gabana sannan ta Kalle ni hawaye na zuba akan fuskar ta.
“Adawiyya da na sani tana da kome da kome wannan da na gani a gaban tsoro nake karta kashe kowa da kowa dan ta zama Abin tsoro”
“Ammyn!” Bilal ya kira sunanta.
“Idan har kana son na amsa maka, ka cika maganarka da kayi a gaban kowa na nunawa kana tare da Jamilah”
  “Kiyi hakuri muje gida” Faisal ya faÉ—a.
“Ban tab’a son Jamilah ba, kuma na gaya mata gaskiya tayi hakuri bana sonta.”
Cikin wani irin kuka da ihu, ta ce mishi.
“Meye ban sallama saboda kai ba, Bilal na baka har rayuwata.”
“Kiyi hakuri, tunda baka son Jamilah meye alakar ka da RABI’ATU? Dan haka ita ma sallama maka ka rike ta, Jamilah kuma Allah zai bata wanda ya fika”
Bude Jamilah aka yi, ta fito, Wasilah ta ce mata.
“Kinyi iya buga wasa, kin raba Ammyn da Auta karfi da yaji, yanzun kuma kin rasa Bilal meye ribarki? Domin ina tare da Rubi” ta fada Æ™asa-kasa.
Murmushi tayi tare da nunawa Wasilah waje.
“Zaki ga abinda zai faru, Bama fadar shirin mu aikin mu kawai ake gani Barista”
  Tunda aka fara maganar ban yi magana ko sau daya ba, haka suka fita har Rahmah.
Har Ammyn ta kusan fita,ta juyo a hankali ta ce mishi.
“Allah sai ya saka mata ita kanta Rabi’atu lalata mata rayuwa da kayi ta hanyar turata kasar waje karuwanci! Kukar da ka sani,Ina da Yara ba zan maka dogon addu’a akai ba, hakkin Rabi’ah ya ishe ka” ji nayi kaina yayi wani irin sarawa, motsa kafana nayi naji zan fadi. Rike ni yayi yana kallon yadda na kafe shi da ido.
“Kasan kome a kaina?” Na tambaye shi muryana yana rawa.
“Ba yadda kika zata bane? Tunda kika fita an yi wani abu dake?”
“Bilal kai da Jamilah kuke game din ku me yasa har dani a cikin shi? Ka lalata min kome ko? Bilal Meye nayi maka? Duk duniya ka rasa wanda zaka yiwa haka sai ni? Kasan.”hannun shi yasaka a bakina.
  “Ya isa haka, zan iya jure duk abinda zaka gaya min karki tambaye ni me yasa ke?” Ya fada min, bayan ya d’aga ni.
Fita muka yi an jarida suka mana caaa wasu tambayoyin kamar da gayya suke mana, ban iya ganewa ba, daga nan muka wuce gidan Marayu. Anan ne na ga asalin tashin hankali, domin babu gidan babu alamar shi an tashi gidan an ruguza shi, sai ya na ne a can gefen gidan. Kafana yayi nauyi na kasa fita a cikin motar ma, shi ya dauko min kome nawa ya saka motar shi.
“Muje gidana” ya fada min, haka muka wuce, koda muka isa gidan na nan babu kowa a cikin shi, haka na zube a falo, ina sauke ajiyar zuciya.
**
A can gidan Ammyn Faisal dakyar ya samo kan Rahmah, suka dawo gida, sai dai taki yarda su yi magana, haka taki sauraron shi.
  Har kwana uku, ganin ba zai iya hakuri ba zata cuce shi da safe zata tafi wurin Practical din ta ya ce mata.
“Ina adalci na miki, kuma ba biki dan a zauna lafiya kin ki fahimtar haka, ki tafi gida, Nagode zaman da muka yi dake. And idan Allah ya sauke ki lafiya abin cikin nake bukata ba sai kin shayar min da shi ba, zaki iya tafiya shima cikin idan ba zaki iya dauka ba ki gaya min zan kai ki inda za a cire a saka a wani wurin ya rayu ko babu soyayya Uwa zai rayu da soyayyar Uban shi.”
  Kasa furta kome tayi tana kallon farin takardan da ya ajiye mata.
“Faisal”
“Ki min shiru, Allah ya bamu dukiya da nasaba bawai mu cutar da kowa ba, ke wacece da zan bi ina baki hakuri? Ke har kin isa ki yi gaba dani,fita ki bar min gidana”
“Amma Faisal wannan ba adalci bane, wannan ba.”
“Wato ga dan babyn wasan yara bari ki ta buga ni son ranki Dan kina matar da nake tsananin So? Ba haife ki ba wallahi” yadda ta fita mata a hankali yasata kiran Ammyn tana kuka, Faisal ya sake ta,kuma yana shirin koranta a gidan shi.
  Babu shiri Ammyn ta kira Ummin, Tare da gaya mata magana.
“Hajiya Harirah! Yaranki ba zababbu bane, sannan basu fi sauran Yaran ba, har gwara namu yaran da Suka taso cikin wadatar arziki, ke da Arzikin daga sama kika same shi, ban gaya miki haka domin ki ji haushi ba, sai dai ina kara gaya miki. Bani da ikon saka Bilal ya so mahaukaciyar Yarki da take niman Rayuwar ki, Kin zata kawai haka kome yake faruwa? Shirin babbar Yarki ce ta samu taimakon ki, ita kuma Rabi’atu da kika ce kin yafe mana,mun gode zamu rike ta hannu bibbiyu. Duk da muna da matsala da Alhalin mu, sai dai kyma bamu yarda a tozarta mu ba. Dan haka ki gaya mata ta kiyaye abinda zai biyo baya dan muma bamu da dadi, shi kuma Faisal domin na nuna miki na haife shi bari na saka ya dawo da Yarki, karki damu muna son Yaran mu amma haka bai hana mu idan suka yi kuskure mu takasu ba.”
Kashe wayar Ammyn tayi,sai yanzu ta fahimci, idan ta gaza wato babban kuskuren ta,Jamilah! Ta bata mugun damar da take abinda take so.
“Ammyn kina tunanin abinda ta gaya Miki ne?”inji Wasilah.
“Meye na aikata?” Inji Ammyn, ta fada cikin matsanancin kuka.
“Kuskure me girma, kin yi abinda take so ba tare da kin bi kome a sannu ba Jamilah ta gaya miki kin hau kin zauna, duk abinda ya faru da Rabi’ah laifin waye? Da ace Ƙaddara bata fadawa Jamilah ba babu ne rabaki da ita, ban tab’a sanin cewa kina masifar kaunar Jamilah ba sai da ta gaya miki karya da gaskiya”
  Daga haka ta bar falon, idanun ta ya cika da kwalla tana hango kuskuren ta.
Ummin kuwa ta kira Faisal ta mishi fada, sannan ta kira Rahmah ta mata nasiha, kafin ta kashe wayar.
Duk abinda ya faru a gaban Rubi da Bilal ne.
“Karka damu ta zauna a nan ta cigaba da zuwa aikin ta. Ko Adawiyya” gyada kai tayi.
“Batun ta koma addini, karka matsa mata kq barta da kanta zata zabi abin take ganin shine dai-dai ko Adawiyya” gyada kai nayi ina me wasa da yatsuna.
  **
Haka na cigaba da zaman gidan ina tafiya aiki na, hankali suka daina kirana Rubi, a wurin aikin ma ba laifi ya mai dani office Dina ina aiki da kamfanin shi, sai dai na daina sakarcin da nayi a bayan haka ya kafamin sharuddan da yake ganin haka zai saka na daina shiga cikin su, sannan Ummin ta rushe maganar auren Hucin gadin dan tace sai na kawo wanda nake so da kaina ,na kome wata irin salaha, dama aikin na shiga jikin shi ya sani shahshanci. Yanxun kuwa babu wannan yanayin, na kama kaina sosai. Shigar da nake na daina shima.