NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

“Kina son shi ne?” Na tambaye ta,
“Eh toh ba zan ce ba, amma kuma ina jin haka a raina. Shi din ne ba kamar sauran mutane bane zai iya boye abinda yake ran shi,. Sannan yayi ta baka wahala, ko kanin shi Haydar ban isa na kula ba.”

“Hmm! Toh ai ke zaki kwaci kan ki, yana son ki yana masifar kishin ki, sai ki nuna mishi ba a rayuwa haka, idan ma auren ki zai yi babu laifi idan yayi kishin ki amma babu wani wanda zai saka ta yayi kishin ki bayan bai aure ki ba, haka kawai ya shiga rayuwar ki maza taka mishi burki” na fada ina fada,
        Sam na manta tare da mutumin muka zo, sai da muka wuce shiga motar ne na tuna shi ya tuko mu.
“Ki dawo gaba” share shi nayi naki tanka mishi,
“Ki dawo gaba nace” ya fada a tsawa ce.  Tura ni Junainah tayi wai na fita duk ta tsorata.

      “Ni ba yarka ba ce, ba zaka min ta tsawa yadda ranka yake so ba, kawai ka kai mu gida” na fada ina me saka earpies a kunnena,  kallona yayi ta madubi yana hango É“acin rai da nake ciki, haka kawai ya sha jinin jikin shi ba wai fadar bane ya sani Fusata akwai abin a kasa. Muna isa gida ya ce min.

“Ki zauna zamu fita”. Kamar zan ce babu inda zani sai na fasa, na zauna ina kallon har Junay ta fita, jan motar yayi da karfin tsiya. A raina na ce.
Kai ka sani

  Haka muka yi ta tafi har muka bar busan, muka nufi railway station. fitowa yayi, ya kira Yoona ya gaya mishi abinda yake bukata,. Can kuwa sai gashi ya kawo mishi har a taxi, sannan ya amshi key motar da ya dauko mu.
“Muje” kallon shi nayi kamar zan yi magana, shima ya kura min ido kasa nayi da idanuna bayan shi na bi,.ina jin kamar na rufe shi da duka,. yana zuwa abinda ya fara yi ya saya mana ticket din tafiya Seoul. Kamar na ce mishi ba zan samu zuwa ba, sai na zuba mishi ido. A hankali yake tafiya cikin wani irin iko da ji da kai, muna isa cikin jirgin kasan muka zauna, bayan wani lokaci jirgin ya cika. Sai dai masu tsayuwa a tsaye.  Wata mata ce ta shigo da tsohon ciki, tana ta niman inda zata zauna babu, tashi nayi zan kirata ya ce min.
“Zauna bari na mata magana” magana yayi mata, aikuwa tazo ta zauna tana godiya. Jirgin na dab da tashi wata me Æ™aramin Yaro ta shigo.

    Bata wurin zaman nayi sabida yadda yaron yake mata rikici duk ta rikice itama,sai ta bani tausayi na bata wurin zaman tare da amsar yaron ina jijjiga shi ita kuma tana gyara rigarta zata ciro mishi abincin shi.  Gashi wurin pubic ne. Cikin turanci na ce mata.
“Bari na baki Jacket dina sai ki lullube ai nan yayi fuskar jama’a”
” Nagode” ta fada min tana dan dukawa kaÉ—an. Ina cire rigar shima ya cire nashi har da  scarf din shi ya mika min. Kallon mu dayawan mutane da suke cikin jirgin suke. Har muka fara tafiya, toh an cika ga yan iska, dan dole ya kai ni jikin kofar, ya tsaya a gabana, tare da manna ni da kofar jirgin. Da wani dan banzan ture turen da ake idan aka turo shi sai ya matse ni da kofar,  karshe ganin haka kawai sai ya saka hannun shi ya tokare kofar yadda ba zasu iya turo shi ba. A hankali muke har muka yi tafiyar awa biyu da rabi kafin muka iso Seoul. Muna isa station din yayi maza ya dawo dani gaban shi, sannan aka bude mana kofar, muna fitowa matar nan ta mika min Jacket dina, ni Kuma na cire mishi na saka nawa, haka muka nufi hanyar fita.  Kallo daya nayi mishi na dauke kai, haka ya kuma hawa wata motar da ta wuce damu huso Women University,

   Lokacin da muka isa jami’ar na sha mamaki, haduwar shi da kuma yadda yake. Har cikin makarantar muka shiga. Kallona yayi sannan ya kira wayar daga yadda yake maganar na fahimci da mace yake, can kuwa sai gata. 

“Gong Yoo!!” Ta wani tawo da gudu ta rungume shi, dauke kai nayi naki kallon su,. Daga nan suka wuce office din Director, itama tana ganin shi ta mika mishi hannun, ya mika mata sukayi kome a gabana. Da Yaren korea ya ce mata.
“Ita ce yarinyar da zan aura, na tura Nam Ra takardun ta, ki duba da kyau zaki gani, idan ta cancanci shiga Jami’ar sai a turo min sakon ta email sai na kawo ta su interwien din.”

   “Mr Gong Yoo, ka yi abinda ya dace, karka damu zamu duba idan lokacin da aka bukace ta zamu gaya maka.” Sun jima suna magana kafin ya mike, tare da musu sallama, muka fito.
“Me zan yi anan?” Banza yayi dani,
“Malam ina magana kayi banza dani” ya fada tare da wuce ni, har muka bar makarantar yaki min magana, sai da ya gama jin kanshi da shan kamshi kamar ba zai yi magana ba ya ce min.
“Makaranta na kawo ki”  kura mishi Idanu nayi.
“Kamar Ya makaranta ka kawo ni? Nayi maka kama da me bukatar zaman aji ne? Ba zan yi karatun ba. Malam ka kama gaban ka.” 

“Au haba?” Ya fada yana kurb’an Coffee, haushi ya sani mikewa zan bar wurin ya saka min kafa dole na koma na zauna,  haka ya gama shan Coffee har muka tawo bai kuma ce min cikanki ba, Ni kuwa a cike nake kamar na fashe,. Muna isa railway station.

Ganin yadda nake niman abokin fada, yasa shi kin biye min tun a tashar jirgin kasa ya kira Yoona ya gaya mishi gamu nan. Tunda yaga yadda nake kin magana ya kara gane akwai abu a raina. Dan haka ya ja ni har inda babu jama’a ya Kalle ni.
“Meye matsalarki?”
“Kai zan tambaya Meye hadinka dani?   Dama kai ka saye ni ka saka ni a cikin masifar Rayuwa? Bilal Meye nayi maka da na cancanci azabtawa daga gare ka?  Ina kallon Æ™addara a matsayin abinda ya zame min wani abu daga Allah ashe kai ne kayi sanadin fadawa ta wannan masifar ina Sauran Yaran suke? Ina Chioma Abigel Tara ina suke? Bilal kai mugu ba da imani, Allah ba …” Hannun shi ya kai kan bakina.
“Kome na rayuwa yana da makasudin shi, ban É—auke ki na kai ki inda za a tozarta ki ba, sai dai nayi hakan ne kawai as abinda ya dace”

Zama yayi tare da jan hannuna na zauna ya cigaba da bani labarin abinda ya faru.
“A lokacin da ta kawo takardun, da naki hada kai da ita izuwa Yanzun babu labarin ku, tun kafin tazo na samu labarin zuwan ta, bayan ka cika mata burin ta, sai na fara kokarin bibiyar daga ina kuka fito, Alhamdulillahi  na samu bayanin dukkan ku, domin ke na tafi har gidan su Steven muka gaisa da Mahaifiyar shi sannan na mata bayanin abinda ya kawo ni, bata boye min ba, ta gaya min daga inda aka kawo ki, anan na koma Jos, na nime gidan marayun su kuma suna gaya min ai a hanya aka tsinto ki, suka min kwantaccen wurin Mss Folina ta bani file É—inki da cikakken sunan ki. Da wannan na zo inda aka gaya min, na saka yan sanda aka yi ya bin dajin har zuwa gidan Dr Musa. 

       Ban yi mamaki ba, amma ban samu wani abu ba daga gare shi sai wannan abin wuyar” . Ya ciro ya ajiye min. Akan cinyata, da sauri na dauka. Ina kallon shi.
“Nawa ne ya tsinke a lokacin da muke kokarin tsallaka katangar da aka daura ni.” Na fada Idanu na yana cika da kwalla.

      “Sai da na duba sai naga flash ce, dan haka nayi fix din shi ga jikin laptop dina, sai ga video Dr Musa da garin ku da kika fito tare da wasu bayanai na iyayen ki sun bar DaÆ™ayyawa, sannan yana da yakinin akwai yan mata dayawa da aka fitar da ku. Tun anan na kuma bazama niman iyalin ki, domin sauran Yan matan na samu nasu, kuma Alhamdulillahi na musu adalci inda ba basu abinda ya dace yaran su, kuma nayi kokarin dawo dasu cikin shakara biyu, sai dai ke tun lokacin da na ganki naga hoton ki na zame miki inuwarki, ban tashi sanin Ammyn ba sai bikin Faisal da Rahmah. Idan nace a lokacin zan bayyana mata inda kike zata iya mutuwa da ciwon zuciya kafin ki iso gare ta, idan kuma nace zan dawo dake karfi da yaji za a miki kisar wulakanci. Amma dake Allah ya haÉ—a mu sai gashi kin biyo ni.  Gaya min gaskiya abinda na miki ne ya kawo ki na kara Miki kome?” Ya tambaye ni cikin zolaya.
“Tir bashi ya kawo ni ba.” Na fada tare da mikewa daga gefen shi, kunya yana kama ni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button