NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

   “Kina tsammanin Jessica Simpson ta mutu ko?” Ware idanu na nayi akan shi.
“Tana nan a Russia”  ban san lokacin da na daka wani wawan tsalle na fada kan shi ba.
“Zaki kashe Dan Um Ma” ya fada tare da rungume ni, da sauri na kwace kaina ina dariya.

“Yaushe zaka kai ni kai ko gobe ka kai ni”
“Haba?” Ya tambaye ni,
Tura baki nayi ina hararan shi.
“An ce min kin kai Jamilah Rehab”  shiru nayi kafin na ce mishi.
“Eh tana can”
“Ita ta gaya Miki abinda kike tuhumata?”
“A’a!”
“Itace mana, domin ita kawai na gayawa labarin.” Shiru nayi ina kallon kasa.
“Yar uwarki ce, amma kiyi kokarin fahimtar ta. Sannan nima ki fahimci waye Bilal.  Bani da burin lalalata goben ki, sannan bana jin zan iya cutar dake else.  Kawai idan Allah ya  Æ™addara abu zai faru sai ya faru.”

“Kamar yadda ka tsara min Rayuwa ta ba?” Na tambaye shi.
“Eh mana,  rayuwar da aka tsara miki guda uku ne! Kafin zuwa na. Ko ki fada karuwancin ko ki zama Yar lesbians, ko Homo. Kina tsammanin idan ka bar gaban iyayen ka ai rayuwar da zaka gani wanda aka tsara maka ce, wanda zaka iya yi shine ka aikata abinda aka gaya maka. Malama nayi haka ne domin kanki, da yanzun kina can wannan katon ya dauka wannan katon ya hau, idan kuma mata ne kullum hannun wata yar banza yana gaban ki ana lalata Miki jikin ki, ko kuma ki wasu karti nan suna fama da duburanki, zama ma sai kin roki arzikin kiyi shi cikin kwanciyar hankali da salama.  Idan baki kwaso infection da HIV. Ba ga wasu wasu cututtukan ba, koya miki kare kanki ne ya zama laifi? Wannan haka kina ji kina gani tsutsa da kuda zasu ta bibiyar ki ana gudun ki. Ki godewa Allah da haka bai faru ba.”

         Bata rai nayi kamar zan yi kuka nace mishi.
“Yanzun don Allah haka  yaran da ake tafiya dasu suke kasance?”
“Ai kin ga ni lokacin da kuka shiga Libya, ina cewa tun a nan aka yiwa mata Fyade, a wurin kin san me cutar hanta? Kin san me cutar sanyi? Ko kin san wani cutar sida?  Saboda babu shi a rubuce mutum yana daukar magani zai kwanta da wata kuma haka zata dauka. Ke dai Allah ya kare mu”

“Taya kasa san da haka? Bayan abinda ya faru baka nan a wurin.” Jan kumatuna yayi ya ce min.
“Aunty Blessing!…….
        

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/15/22, 07:53 – My Mtn Number: 80

“Ahmmm! Da gaske ka santa?” Na tambaye ina mamaki, murmushi yayi tare da wuce yayi gaba abin shi. Da gudu na tsare mishi hanya.
“Kace me? Kace ka santa to tun yaushe ba zata kai baka san kowa ba, kawai” ai kuwa na hau zuba kamar ruwan sama rab’a gefena yayi Abin shi yayi tafiyar shi bai tsaya ba sai cikin sai wurin mutanen suke domin mun kusan isa Busan,  da gudu na nufe shi.
“Miracle moment! Kept it on your ina tare dake ba zan taba barin ki, ki fadi ba.”

       Gyada kai nayi ina murmushin jin dadi, kamar yadda muka zo, haka ya kuma bani kariya, har muka sauka. Muna fita muka hadu da Yoona.
“Barkan ku da dawowa”
“Yawwa Yoona”

    Koda muka shiga motar kwanciya nayi sosai, ina sauke ajiyar zuciya, kallona yayi ta glass dan gaba ya zauna,. Yaga ina lumshe idanuna.
“Me yasa ba zaki koma Musulunci ba?” Ya kalli agogon hannun shi karfe biyu saura,

   “Kuna zaku karbe ni ne?” Na tambaye shi,
“Me zai hana?” Ya fada min,
“Toh zaku min taron suna ne?”  Kallona yayi ya dauke kan shi bai kuma min magana ba, domin ya lura da rashin kunya a maganar, muna isa gida ya shiga wurin kakan shi sallah ya yi a can, ni kuwa na shiga cikin gidan. Nan muke hira tare da samun su kowa ya gama shirin cin abinci.
“Ummi ni kimchi soup and fried rice nake so!” Na fada ina kallon abincin gargajiya na Hausa aka yi.
“Mr Pi taimaka mana da Kimchi”  inji Umma. Hatta ma’aikatan gidan da soyayya take mu’amalar su,

“Umma bari na amso” na fada ina nufar kitchen din, shaÆ™ar kamshin nayi me dad’i, na hango chocolate ake had’a, hàdiye yawu nayi nace mishi.
“Mr Pi zuba min nawa ina son ci, na fasa cikin Kimchi”

   Na fada ina mika shi wani dan ƙaramin, kallona yayi kafin ya zuba min saka shi nayi a frig, na zauna ina jiran shi. Sai da yayi dauri na ciro, na zauna na fara hankali kwance. Ina cikin ci Umma ta shigo.
“Rabi’ah! Waye ya ce kici chocolate din? Kinsan na meye?” A tsorace na kai lomar karshe.

“Mr Pi me yasa ka bata kasan bana Yan mata bane na yayarta ce fa me aure yanzun don Allah ya zan  da ita” mikewa nayi ina kallon su. Bakina yana rawa nace musu.
“Wani abu zai same ni ko?” Zaunar da ni tayi ta shiga hada min wani irin juice. Ta markade shi sannan ta tacce min sannan ta mika min.
“Maza shanye ki bani kofin” ina sakawa a bakina bauri naji. Cirewa nayi kamar zan yi kuka. Haka na shanye tass sannan na mika mata, kallona tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya.
“Gobe idan kin ga ana irin wannan abin babu ruwan kin kinji ko?”
Gyada mata kai nayi.

Wuce su nayi na nufi dakin Yasu Ya Wasilah,. Na same ta tana karatu.
“Sannun”
“Yawwa, Autar Ammyn mu” ta fada min tana kallona.
“Akwai magana ne?” Ta kuma tambaya na,
“Hmm! Dama ina son na gaya miki ko zaku samu damar mu duba Ya Jamilah a Rehab ne?”

    “Ok kin gayawa Bilal?” Girgiza mata kai nayi.
“Ok is better ki gaya mishi ko?” Ta gaya min.
“Bana son zuwa da shi ne, sabida har yamzun Ya Jamilah bata nutsu ba”
“Toh gaskiya sai dai mu hakura tunda idan ya gan shi bata da hankali.”
“A’a zamu tafi da shi ma babu abinda zai faru, bari na tafi wurin Junainah” na bar dakin da sauri ban san me yasa bana son maganar Ya Jamilah da sauran Yan uwa na ba, amma na ajiye haka a raina zan gyara alakar mu baki  daya.

   Na shiga wurin Ya Rahmah tana sallah zama nayi inawasa da Deedat, har ta idar. Na gaya mata yadda muka yi da Ya Jamilah.
“Ke ni tsoron Allah nake ina tsoron Ya Jamilah. Kawai ki bar ta idan ta warke ta dawo.”

      “Babu damuwa, zamu je haka” na fada ina kallon ta. Fita nayi a dakin, na gaji ina shiga dakin mu na kwanta,
“Ina kika shiga ne yau baki É—aya”
“Tafiyar awa hudu nayi hutun minti talatin”

Cire min Safar kafana tayi tana faÉ—in.
“Umma tace wai zaki fara huso Women University?” Juyawa nayi na Kalle ta.
“Eh, Kema ai naji kina karatu ne a jami’a” xama tayi muka sha hira abinda ya wuce, wani kuma muyi kuka sannan mu cigaba da hira.
**
Anambra

G.R.A new side.

   A hankali motar da ta je daukar shi a tashar jirgin sama, ta kunna kai babban katafaren gidan su, shiga Driver yayi da hancin motar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, suka shiga cikin gidan, da yake share kwal-kwal,, tsayawa yayi a parking lot, sannan ya fito yana kallon yadda aka kara gyara gidan yayi kyau ga wani daukar idanu da yake yi.

       Nufar cikin gidan, yana me murda handle din kofar, ya tura a hankali.
“Steven!” Mamar shi ta kira sunan shi kamar zata yi kuka, cikin sassarfa ya isa wurinta ya rungume ta, kuka ta saka abin tausayi.  Sun jima kafin Matar kawun shi ta fito,.
“Aunty” itama ya rungume ta, sannan ta shiga basu labarin abubuwan sa suka faru. Tare da gaya musu Rabi’a tana nan ai kuwa murna a wurin  matar kawun shi.
“Tana ina yanzun?”
“Tana korea, gata nan” ya nuna musu hotanta da Bilal.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button