WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
  Kai ko Dinner ban samu zuwa ba, haka aka min wani mahaukaciyar gyara idan na zauna nayi ta diga kenan, ai kuwa ranar da aka kai ya Jamilah gidan ta da yake lekki, daga can Bilal yayi gaba dani, domin yayi kewata Allah sarki dan Maraya mijina, aikuwa muka gurza soyayyar mu da shi, ina manne a jikin shi yana waya da Faisal. Kamar ba zai yi ba.
Sannan ya kashe, wayar muka cigaba da barci.
**
A daren Faisal da Rahmah suka nufi gidan su, itama da nata tsohon ciki sai Nadrah itama tana gab da haihuwa, Ya Wasilah ma bakwai ni ta haifa sabida bala’in jarabar Alman.
 Ya Jamilah itama a ranar ta fahimci Aaman bai yi aure ba, Husnah ma gajiya da jiran shi yasa tayi aure shi kuma yana jiran ta, a ranar bai d’aga mata kafa ba, ya goge mata wancan haddar baba Haliru ya kafa mata nashi da soyayyar shi ne gardi. Sannan ya shiga nuna mata shi dama can ita yake so.
  A can gidan Alhaji Muhammad Lawal Dambatta kuwa Alkasim ne a gaban Mammy yana rokonta.
“Don Allah Kice ya sake Wasilah wallahi ita nake so ban san me ya faru ba”
“Zaka sani lokacin da idanun ka suka bude” inji Mommah.
“Karimah da kin kyale shi ya gama haukar shi ita gwanjo ne da Alman zai sake mishi ita ni da kai muka yi magana kace ai Aalimah kake so va Wasilah ba, TOH Meye?”
Kamar mahaukaci haka ya koma domin sai yanzun yake danasanin rabuwa da Wasilah mugun sonta yake, kamar zai mutu.
  **
Washi gari ya gama iya yin shi ya dawo dani gidan Mammy, cikin jin dadi ta shirya mana abin karyawa da shi Bilal din, muna ci muna hira, kwarewa nayi baki daya ya birkice yana shafa bayana.
“Sannun kin ji!”
“Yawwa” hakan muka gama cin abincin sannan muka musu sallama bayan ya musu alkhairi itama Mammyn jaka ta bani shake da kayan gyara, sannan muka nufi gidan Ummyn a nan wasilah take wankar jego.
 Jikin Ummyn na koma na kwanta, tana hiran Ammyn mu, sai kuka nake musu. Haka duk ya d’ago ni muka je dakin shi na kwanta a jikin shi barci yayi gaba dani, kwanan mu biyar muka tafi DaÆ™ayyawa muka sha hutu gidan mu aka buge aka yi flat hudu,. Sannan Bilal ya sauka haya baki daya yana cewa.
“Idan muka zo baki dayan anan zamu sauka kowa da part din ta da mijinta daga karshe mu hadu a falo.
  Daga nan Daƙayyawa mun wuce garin Kano idan muka sauka a gidan Abba musu shima satin nan za ayi bikin Junainah da Muhammad Aliyu Assadullah Aliyu, dan haka muka tsaya domin mune kawaye,. Haka muka yi ta kaiwa da komowa ga Sabrina da tazo, a ta dame ni da abdurrahman abin ya dame ni sai da na gayawa Bilal ya ce min.
“Ke Steven ne ya musulunta kuma Dr Hayat ya bashi auren ta” toshe baki nayi na daka tsalle na fada kan shi.
Anyi bikin Junainah muka je har Maradi, sannan muka dawo. Bikin Junainah da Sabrina sati biyu a tsakanin aka yi bikin itama mun sha hidima. Sannan nake gaya mishi labarin Muhiyuddin.
Jan hancina yayi tare da cewa.
“Mahaifin shi ya dauke shi daga kasar baki daya, domin sun tafi zubda cikin yarinyar da take aiki a gidan su ta rasu. So babu wani magana.”
 Tausayi yarinyar ta bani, nan muka wuce lagos kwanan mu tara,muka samu labarin rasuwar Baba Malam Allah yasa mu nan dole muka je baki daya har da wasilah da Ya Jamilah. Burin Ammyn ne ta ganmu kan mua hade Alhamdulillahi. Bayan mun dawo daga ta’aziyar ne muka nufi inda muka fi wayo.
Bayan tafiyar mu ne aka samu labarin Khalil bai da lafiya, Faisal ta je ganin shi a asibiti inda ya samu ganin shi ya koma kamar lomar tuwo, ya kare tass ga Cancer dubura da yake damun shi bawan Allah nan yaso batawa Bilal suna.
 Hajiya Humaidah sun hadu da Hajiya Shuwa suka jangwalo Rigima karshe aka musu dukar mutuwa, Shuwa a take tace ga garin ku a cikin gidan yarin Humaida ne tayi Hauka sosai. Alhaji Adamu kan ba lafiya. Hakq Abdulkadir, shima ba lafiya.
Hanan kuwa ta zama kamar karya, domin kowa a cikin yarin bibiyarta yake ba mata ba ba maza ba, haka ta zama kamar me za ace dai ta gama. Shina Hilal dakin wasu yan fashe aka kai shi suka yi ta gana mishi azaba tare da kwanciya dashi ta dubura dai da suka ga yana zubda jini suke kalle shi.
  Allah kasa nufi karfin zuciyar mu, ya kare.mana zuri’ar, ka rabamu da son zuciya da son kai..
Bayan shekara uku na gama Huso Women University, inda Ya tattara ni muka koma Madinah, amma sai da aka yi bikin NaNa da wani actor na Kdrama, gaye me masifar kudi. Seyo Na kuma ta auri wani Baban Mayor a nan korea, aka sha baki. Tun kafin mu tafi madinah Umma take cewa.
“Dota baki da lafiya ko? Domin kin rame ko hidimar bikin ne”
“Umma bata barci kullum da zazzaÉ“in dare take kwana.” Ya fada yana kallon yadda nake tsakuran abinci.
Da kanta ta kira likitan su ya duba ni, sannan ya saka min ruwa sai da ya gama duba kome sannan ya dawo yana farin ciki, yana gayawa musu cikin wata daya ne dani. Bilal ya shigo ya zauna a gabana, har na tashi.
“Mr Perfect! Baka fita bane?” D’aga rigana nayi yana kallon mara na!
“A’a my Adorable Queen, Ashe babyna ya zauna anan” ya shafa cikina.
  Mika mishi hannun nayi ya kwanta a jikina na ce mishi.
“Allah ya inganta mana, dan sosa min”. Na fada kasa kasa. Dama me shirin kuka ne aka wurge shi da kashin awaki, ya gurje ni har ya gaji dan kan shi ya bar ni, a tare muka yi wanka.
  Hmm ciki kamar jira yake duniya ta san da zaman shi, na fara laulayi haka muka isa madina, da gidan da ya kama mana, dan shima yace yana son yayi diploma a hadisi yana da shi a Alqur’an. Haka muka sha laulayi tare kuma bamu hakura da juna ba.
 Bayan wata takwas Junainah ta haihu, tsakanin da ta Sabrina sati Daya itama sunan Madinah haka nayi ta zirga-zirga sabida Abdurrahman yana karatun shi akan Alqur’an shima da addini, ana hakan bayan sunan ta Faisal ya kwaso matar shi da Dan Yar su me sunan Ammyn muna kiranta Nuwairah.
  Sai yar wurin Sabrina da aka saka mata Ummul Ruman,. Muna kiranta da Widad, Faisal ya fara shima diplomar shi a Alqur’an Ni ne Yace ba zai yarda Bilal ya nime lahira ya bar shi da dakon duniya ba.
Ranar wata juma’a na tashi da nakuda, tun safe nake fama har na tafi makaranta, a can ciwo ya tarke ni aka wuce dani asibiti. Tun karfe tara har aka sauko Jumma’a nayi laushi sosai har an fara tunanin min aiki, ana kiran Sallah La’asar a masallacin Manzon Allah, ina sauke nauyin da yake kaina, katon jinjirin Yaro sak uban shi.
“Alhamdulillah” inji Nurse din ta mika min shi, kafin na masa wani Katon ya kuma saukowa.
“Masha Allah” ta kuma furtawa bayan ta yanke cibiyar ta kifa min su a kirjina, ta kai hannun ta wani ya kuma sauka.
“Allahu Akbar!” Ta kuma fada, haka ta yanke cibiyar. Ta daura min bata kuma yunkurin ta bani ba, a hankali baby na huÉ—u ya kuma saukowa.
“Alhamdulillahi a’a kulli ahalin!” Ta fada tana kallona.
“Cikin kina zuwa awo amma bai taba nuna mana hudu bane mun fi tunanin biyu ne ashe Allah me kyauta da kari hudu ne” murmushi.nayi domin ban san me zan ce ba, ya bani cikin mara dogon laulayi. Sai jarabar uban cikin.
Haka aka shirya su, sannan aka shirya ni, sannan aka gaya musu na sauka. Farin ciki ba a magana. Haka aka fito da mu baki daya, kallona yayi yana murmushi, dakin Hutu aka kai ni. Sannan suka min alluran barci.