WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
Dariya yayi tare da dukar kafadar Faisal, “kayi hakuri, ba zan kuma ba” ya fada tare da jan hannun Layinah suka fita, wani irin ihu ta saka tana cewa.
“Nawa ne?”
“Malama ba baki bane, sannan ina ke mace ina hawa bike nawa ne, Ya Bilal ya turo min shi tun Last week.”
“Iskancin banza” ta juya tare da barin wurin, gwalo yayi mata yana dariya. Wayar shi aka kira, a take fuskar shi ta sauya. Dauka yayi tare da shiru, idanun shi yana cika da kwalla.
  “Kana ta boya kana gudu, aiki zamu baka idan kuma ka ki kasan yadda aka yi Asthma Hajiya Atikah ya tashi, toh haka zamu maka.” Idanun shi ya rintsa kwalla ya xubo mishi, a hankali ya juya zai bar wurin ya hango Faisal, da sauri ya bar wurin, tsaki Faisal ya ja, domin ya tsani rashin hankalin Alman.
 Can bayan asibitin ya nufa, cikin muryan kuka ya ce musu.
“Waye kai? Akan me zan dauko bayanin sirrin Bilal Ahmad Jikamshi? Ina cewa kuka yi ba zaku tab’a zuri’ata ba na dauko muku bayanin JF Group, na dauko muku har da na mahaifiyata, don Allah ku barni”
 Ya fada yana kuka kamar Yaro karami, kashewa wayar yayi, tare da komawa bayan asibitin sosai sannan ya ciro wata karamar waya irin me torch din nan, ya kira wani number aka ce mishi a kashe take, kuka ya saka tare da zama a wurin. Yayi danasanin kin cigaba da aikin shi a kamfanin JF Group, dan haka ya nufi wurin famfo ya wanke fuskar shi, sannan ya shiga cikin asibitin. Wurin Ummina shi, yana shiga ya zauna shiru ba kamar dazun da yake cikin farin cikin ba, kallon shi tayi tare da cewa.
“Alman waye ya saka kuka?” Kamar wanda ta dake shi, ya fashe da kuka.
Shiru dakin ya dauka, yan uwan shi suma jikin su yayi sanyi. Kuma sun kasa magana, Wayarta ta dauka garin kiran Faisal ta danna kiran Bilal. Har ya shiga ma.
“A’a Ummin mu, karki gayawa ya Faisal, babu kome kawai ina kewar Ya Bilal ne, nasan da yana nan Allah zai bashi ikon kare mu.”
    Cikin mamaki take kallon shi bakinta a sake.
“Toh meye ya same ka? Waye ya rab’a ka?”
Cikin kuka ya ce mata.
“Babu kome”
Zai mike ta mai dashi tana faÉ—in.
“Zauna ka gaya min meye ya faru”
Idan ka sake muka ji labarin wani naka ya san me yake faruwa, har asibitin zamu zo ba Bilal ka ce yana nan ba bari muji wani abu zaka amshi kyautar da tafi kowani kyauta kyau da tsada
Da sauri ya shiga girgiza mata kai yana faÉ—in.
“A’a babu, kawai manta kawai” haka ya bar dakin yana share kwalla, a hanyar fita suka hadu da Hajiya Turai da Humaidah, sai Shuwa. Zasu shiga cikin asibitin. Cikin girmamawa ya gaishe su, sannan ya wuce su.
“Kai a wani dakin uwarka take?” Inji Hajiya Shuwa, dawowa yayi tare da musu jagora har dakin Ummin, tana zaune Layinah da Lubna suna jajjanta halin da yake ciki.
   “Assalamu alaikum, Sannun ku dai!” Suka fada lokacin da suka shigo,
“Wa’alaikumun salam, barkan ku da zuwa Mamah Humaidah, Mamah Turai. Aunty Shuwa barkanku da zuwa.”
 “Yawwa Sannun ku Yaran nan” mikewa sukayi tare da barin dakin,
“Ayya an saka ku aiki da kun zauna ina kyautatta zaton an jima zasu sallame ni” ta fada tana murmushi.
“A’a gwara musu, kar a ce muna farin cikin kina cikin wani hali” murmushi tayi sannan ta ce musu.
“Dan Adam me dai ba a iyar Mishi amma Meye abin magana, barkan ku da zuwa ya gida ya aiki da iyalai”
“Alhamdulillahi, ya naki jikin, da fatan kina lafiya” gyada musu kai tayi tana faÉ—in.
“Alhamdulillahi, sai godiyar Ubangiji. Jiki kamar ba ayi kome ba.”
“Toh Allah ya baki lafiya”
“Amin Ya Allah, ” nan suka shiga tab’a hira,
3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci ga masu bukatar su zasu iya tuntubar wannan number sai mun jiku👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697
24
Daga haka basu kuma magana ba, Asalima, shiru ne ya ratsa tsakanin su. Kafin suka mike tare da mata fatan sauki.
“Zamu tafi, Allah ya baki lafiya kuma ya kamata ki kula mana”
“Allah yana tare da ni ban isa na kula da kaina ba, duk abinda mutum ya shirya akwai Allah shi ya riga shi na shi shirin.”
   “Lallai toh Allah ya taimaka” daga haka suka fita, mamakin yadda akan wani karamin abun da bai kai ya kawo ba, amma suke niman rayuwar junan su, tasan basu da niyyar alkhairi akan su, shi yasa suke irin wadannan abubuwan.
Tun daga lokacin ta kasa gane kan Alman baki daya ma kamar wanda ya b’ata, sun yi niman duniyar nan bashi babu labarin shi. Cikin jin haushi da gundura akan hiran shi da ake ya ce musu.
“Don Allah ku daina cika min kunne da maganar Alman duk inda taso ya tafi mana, waye ya damu ace mahaifiyar ka tana cikin rashin lafiya ka tafi sabgar gaban ka! Tir”
Kallon shi Hajiya Atika tayi tare da cewa.
“Ba kin zuwa yayi ba, dauke shi aka yi” a matuÆ™ar razane ya juya yana kallon ta.
“Kamar Ya?” Ilahirin jikin shi rawa yake, zunzurutun tashin hankali.
“Ban sani ba, amma dazun an turo min da wannan sakon.” Ta mika mishi wayar hannunta, bude sakon yayi tare da kallon shi. Ya karanta da karfi.
*Dole ki saka dan Yayanki ya janye zaben da za a yi a JF Groups matukar haka ya faru! Danki zai biya kuskuren da kuka yi, koda yake koda mun mishi wani abu ba zaki damu ba, amma zamu tab’a ki ta yadda zaki ji kome”
Shiru yayi yana kallon mahaifiyar shi.
“Meye mafita?”
“Mafitar É—aya ce a soke zaben domin mu samu dawo da Alman” ya fada tare da turo kan shi cikin dakin.
Sanye yake da wani sweater coat, brown sai white jeans na K7, sai rigar Nike black har saman wuyar shi rigar tayi mishi kyau, asalin shigar na baki daya, gashin kan shi har gaban goshin sa, kura mishi idanu suka yi.
  “Yaushe ka dawo?”
“Tun juya” ya fada bayan ya isa gaban Ummi da idanunta ya cika da kwalla
“Meye na kuka? Bayan kina da Allah” gyada mishi kai tayi tare da rungume shi.
“Bilal me yasa suke son ganin ka durkushe? Me yasa suke son ganin bayan ka? Me yasa suke da burin raba ka da duk wanda yake tare da kai?” D’ago kai yayi yana murmushi kafin ta cf mata.
“Wai? Damuwa kike a kaina, manta kawai”
“Amma kasan halin da muke ciki Meye na wani zama ka daura daya akan daya?”inji Faisal,
“Jin dadi”
“Banza wato ni kake yiwa iskanci na b’ata lokaci ina zuba ka gaya min magana daya” inji Faisal,
“Toh Alhaji Ahmad Abbas Jikamshi” inji Bilal,
Dafe goshin sa yayi, tare da komawa ya zauna ya ce mishi.
“Toh me zan ce musu?” Inji Faisal, ciro wayar shi yayi yana latsata, kamar ba zai magana ba, kuma can ya ce mishi.
“Ce musu su kashe shi!”
“Amma kai dan iska ne! Taya zaka ce a kashe shi? Idan suka kashe shi da? Banza wawa kawai”
Mikewa yayi tare da rike hannun Ummin ya ce mata.
“Uwata ina tare dake, zasu kuma turo miki sakon ki gaya musu na janye kuma yanzu haka a hadu a board meeting.” Ya fada tare da sosa goshin sa.
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
“Allah yayi maka albarka” daga nan ya kalli Faisal da ya sake baki,ganin ya suma ba zaune ya sa shi murmushi yana d’age mishi gira, fita yayi Faisal ya bi bayan shi.
“Amma kuma kana ganin akwai abinda za ayi bayan an dakatar da zaÉ“en Æ™asan dai dole sai da taimakon ma’aikatan kamfanin”
“Eh mana na sani, Alman nake bukata” daga haka suka fita duk inda suka wuce gaishe shi ake, sakamakon shine shugaban kamfanonin Jikamshi baki daya. Suna fitowa Namir shima ya fito zai tafi nashi sabgar. Kallon juna suka yi da Jikamshi a matukar razane ya koma office din shi jikin shi yana rawa.
“Akwai abubuwa a hannun shi amma dan iska yaki bani ko zamu shiga cikin office din.”