WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
…
Lekki housing estates.
Tun safe ake ta fama da aikin gidan sai kawa da komawa ake kai zaka rantse da Allah baki ne daga fadar shugaban kasa. Nan kuwa ba kome bane sai na farin cikin dawowar Nadrah Ruma yar gidan Hajiya Turai Abbas Jikamshi Mrs Ali Ruma.
Wato Nadrah Ali Ruma, wacce zata dawo daga kasar waje, bayan tafiya karatunta na degree, gyaran gidan ake ko ina tsaf tsaf, wajen karfe daya na rana, motar da taje dauko ta, tayi parking a farfajiyar gidan wasu guda biyu ne suka shigo bayan nata, da sauri Aka bude mata kofar, sai da ta gama yangarta, sannan ta fito daga cikin motar tana me musu wani irin kallo kamar idanunta zasu fadi kasa,a sanyayye ta sako kafarta tana yatsuna fuskarta kamar ta ga kashi. ÆŠaukar karamin jakarta tayi, tana me tafiya a sanyayye kamar wacce kwai ya fashe mata. Har cikin gidan suke bin bayanta,.kafin ta kai hannu ta bude kofar har an bude ya cikin gidan. Murmushi tayi sannan ta shiga, tare da raba idanun ta.
“Mummy!!!” Ta kira sunan Mamarta cikin d’aga murya.
“Oyoyo Lovely Barka da hanya mutanen Holand”
 Wani irin ihu ta saka tare da fadawa jikin Mamanta tana faɗin.
“Mummy na” ta k’amk’ame ta, kafin kace me gidan ya dauki dumin ta dawo, nan aka shiga hidima da ita har ta samu suka nufi dakin ta,ta shiga wanka, tana cikin wanka taji wayar ta yayi kara, da sauri ta wanke jikinta saboda tasan waye me kiran nata.
Tana fitowa ta dauki wayar tare da sakawa a kunne.
“Honey! Na iso lafiya”
Daga can ya amsa mata, can ƙasar makoshin sa yana faɗin.
“Beb zan zo ma dauke ki an jima”
“Honey ko jiya muna tare a Abu Dhabi, sannan yau ma muna tare please kar kayi yadda za a san muna tare ka ja min matsala”
“Ok ba zaki fito bane na shigo cikin gidan. Karfe tara zan zo daukar ki.” Kashe wayar tayi tare da wurgi da shi bata san me yasa ta daukowa kanta matsala ba, amma yadda Mahaifiyar ta take Masifar kaunar ta taji wanda take tare da shi sai ta kusan cinye ta sanye, ban dakin ta koma tayi wanka. Tana tsaki, har ta gama ta fito tana goge gashin kanta, da dan karamin towel. Zama tayi tana kallon. Dakin ta ko ina tsaf tsaf, gwanin ban sha’awa, haka ta shirya cikin turkey gown, sannan ta yafa mayafi akan ta, sannan ta fito tayi kyau sosai. Sanye take da wani pink shoe, ta fito tare da raba idanun ta kan dinning table, tana murmushin jin dadi,.hango Kanwar mahaifiyar ta Hajiya Humaidah Abbas Jikamshi, tare da yarta me shegen rashin kunya. Dan hade rai tayi tana kallon inda ya dace ta zauna ta ce.
“Aunty Humaidah Barka dai”
“Barka dai Dota an dawo lafiya? Ya karatunki”
“Alhamdulillahi” ta ja kujera ta zauna tana me murmushi ganin duk abincin da suke wurin favorite dinta ne, dan haka ta fara diban abincin tana Zubawa, tare da kallon Mahaifiyar ta.
“Mummy Ina son zan fita an jima” sai lokacin ta d’ago fararren Idanunta da suke cikin Medical glass ta ce mata.
“Dan baki san yanayin da muke ciki bane yasa kike tunanin zan barki ki fita haka? Comon ci abinci bana son shirme”
“Mummy kin san dai ni ba yarinya ba ce, zan fita ne tare da Anur Magajin Zazzau, sun shirya min party ne babu wani abu” jin ta kira sunan dan gidan sarautar Zazzau yasa uwar ta zuba mata ido,.kafin ta ce mata.
“Ƙarki manta an miki miji kuma nasan kin san da haka, duk abinda zaki yi, ki tabbatar baki yi abinda zai saka ki rasa Virgin É—inki ba, ni kuma zan tabbatar da na baki shi a hannun ki be careful”
“Ok Mummy”ta fada tana cin abincin, har zuwa lokacin Yar Humaidah me suna Mimih Alfah bata d’ago kai ta kalle ba, asalima tana family GRP din su ne tana kallon yadda ake wani ribibin yin magana da Seyo Na da NaNa. Rufe data tayi tana kallon abincin gabanta duk da ba wata babba bace amma kuma ta iya kwainani da iyayi, shi yasa Uwar take Masifar kaunar ta, tafi yan uwanta su kan babu ruwan su, amma Mimih itace ake cewa gindin durumin duniya. Cikin wani irin jijji da kai ta cewa Nadrah Ali Ruma.
“A ina zaku yi party ko babu gayyata ne?” Cikin wani irin takaici da yadda take jin Haushin Mimih ta ce mata.
“Kiyi hidimarki malama”daga haka ta cigaba da cin abincin, tana gamawa ta mike tare da nufar falon, tana zaune aka danna Bell na kofar gidan.
 Yar aikin gidan ce ta bude kofar ta ga securityn gidan ya mika mata wani kwali wanda aka yi nad’e shi sa leda me kyali alamar kyauta ce.
“Ki bada Madam yanzun aka turo mata,”
  “Ok”
Juyawa yar aikin tayi tana kallon Nadrah da ta hard’e kafa,.tana kallon tv, cikin girmamawa ta isa gaban ta, tana faÉ—in.
“Ma’am gashi nan yanzu Paul ya bani na kawo Miki”
Karar da Wayarta yayi ne yasa ta duba.
Wannan karamin kyauta ce, please ko zaki iya fitowa na ajiye Miki wani karamin please karki rena shi wannan kayan kuma shi zaki saka an jima me makeup zata zo please
Cikin wani irin tsimma ta warware kayan wani, shegen gown ne iya kwannji sai me hannun Armless, gaban shi an zuba wasu irin stone masu daukar idanu, cikin kwalin wani karamin box ne, dauka tayi tare da budewa,key mota ce me dan banza kyau.
     Da sauri ta fito daga cikin gidan fa fito waje tana ihu, da wasa ta ga motar ana lunch din shi ta ce mishi.
I Man wannan motar yayi min kyau! Da zan same shi sai na fasa gari da da garari
Wani kuka ne ya taso mata, yasan ba zata same shi ba, kuma koda zata same shi bai zama dole a zauna lafiya ba, tunda daga ita har shi sun san matsayin su ba mamaki zargi ya dirsu a ran su.
“Wow wani banzan ne ya baki motar nan? Naga zata yi kyau bani key din na fara danna ta, domin nasan kin bada kyautar pussy aka baki wannan.” Inji Mimih,
“Kome aka yi da jaki sai ya ci kara!” Ta fada tana buÉ—e motar a hankali.
A cikin gidan kuwa,.kallon Juna suka yi cikin tsananin mamaki.
“Me kika ce Turai? Bayan shirina ya tafi zaki bijiro min da wannan zancen? TOH wallahi ko ni ko ke, na rantse da Allah ba zan yafe ba,.shege ka fasa dan halak sai yanka….300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: Albishir ku.. kuce min goro...ko kusan S.squar Fashion &More Sun kuma kawo muku ingantattun kayan su masu kyau da rahuwasa... Turaren wuta na zamani. Milk candy Hijabs da gowns tare da kayan Yaran ku masu kyau da inganci zaku iya tuntubar wannan number👇ðŸ¾ðŸ’ƒðŸ¼Http://wa.me/+234 703 003 7697
30
“Kiyi duk abinda zaki yi amma babu fashi, kuma wallahi a tafin hannuna kike matukar wani shirme ya faru zan nuna miki ratar shekarun da yake tsakanin mu ba na wasa bane,ke wallahi zan batar kuma zan saubatar da duk wanda ya shiga tsakani na da muraduna.”
  Cikin tsananin mamaki ta zuba mata ido, kafin ta sake murmushin takaici tana faɗin.
“Wani dare ne Jemage bai gani ba, da har zaki iya min barazana da tsoro,ina ma da zan buge kirji nayi tabbas da duniya sai ta miki tofin alatsine.” Ta fada tare da juyawa abin ta.
“Hhh! Toh mu zuba mu gani duk wanda ya fasa ya rena abu kazar kazar uban shi”
“Sai dai na Ubanki” ta fada tana barin falon a harabar gidan ta same su,.suna tsaye sai gayawa Juna magana suke.
“Mimih zomu tafi”
“Ok Mamie” tabi bayan uwar tana murmushin mugunta, har ta shiga motar su, ta kalli Nadrah Ruma ta ce mata.
“Mss Ruma zan bincika sai ta tabbatar miki da na zo” sannan suka bar gidan, da wani matsiyacin kallo tabi motar su, tana jin wani irin haushi a ranta.