NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

   Takowa suka yi tare da kai hannu zasu taba ni, na fasa ihu tare da kiran wani suna”Ammyna!!!” Da sauri ta ture laptop din, tashi nayi zaune lokacin gari ya fara duhu, matsawa nayi jikin shi tare da daura kaina a kafadar shi.
“Am scary”
“Babu abinda zai faru, gani nan” ya fada tare da shafa kaina, ajiyar zuciya na sauke tare da komawa jikin shi na kwanta ina lumshe idanuna. Cikin damuwa ya ce min.
“Ke damunki?”
“Wacece Ammyn?” Kallona yayi yana nazarin abin zai ce min kafin ya dauke kan shi ya mika min ruwan da yake dagen shi.
“Maybe someone else” ya fada yana kallon yadda nake shan ruwan,
“Kina son wani abu ne?”
“A’a” ya kuma tambaya na a karo na biyu,
“Zaki ci abincin ne?”
“Hm” mikewa yayi tare da nufar cikin gidan, ya xubo min abincin da yanzu Maman shi ta sauke.

“Steven” maman shi ta kira sunan shi, juyawa yayi yana kallon ta.
“Yes Ma”
“Ina son ka shirya jibi ka tafi ka duba min Uncle din ka Emeka bai da lafiya.”
“Amma Mah taya zan tafi na bar Rebecca babu lafiya?”
“Ok kana son na hana ka tafiya da ita kenan America?”
“Ok” ya fada bayan ya dangwara mata abincin ya fita daga cikin gidan, ya nufi part din shi, key ya dauka, har zai fita ya dawo ta dauke ni da kayan shi ya kai falon shi.
“Ki zauna yanzun zan dawo ko” gyada mishi kai nayi ya fita, ashe ya rufe kofar, ina ji tana bugawa tsoro ya kama ni, tayi kiran duniyar nan amma fir naki amsawa dan nasan idan na amsa laifi nayi,.kuma zata dake ni. Tana wurin har ya dawo, juyawa tayi ta kalle shi. Hannun shi dauke da ledar abinci. Shiru tayi tana kallon yazo ya shige bai mata magana ba.

A ranta taji zafi sosai, amma sai ta share bata kula shi ba, tasan dai dole yayi mata abinda ya ce ne,.

*
After two days

Yana tsaye da Obinna, sai kallon Rebecca yake, kamar ya hakura da tafiyar amma haka ya shiga motar, a hankali na juya zuwa bayan gidan na zauna ina jin lokacin da ya tafi, ba zan manta da Shi ba.

      Ina jin motar su ta su, kwalla ne ya xubo min. Dan haka bayan tafiyar su na fita waje ina kallon kofar gidan su Sabrina bata nan, karasawa nayi wurin me gadin gidan na gaishe shi sannan nace mishi.
“Ina Sabrina?”
“Sun yi tafiya” shiru nayi sannan na juya a hankali, hawaye na zuba min.
“Rebecca” juyawa nayi na kalli Madam Fate ce da Mama a matukar tsora ce na isa wurin su, cikin gidan muka shiga, tunda na shiga babu wacce tayi min magana.

Har Obinna ya dawo shima, sannan ya fita. Kallon juna suka yi tare da mika min juice, amsa nayi na sha ina kallon su, sannan na ajiye musu kofin ba koma can gefe na zauna. Bayan minti goma sai na fara jin wani irin barci yana dauka ta, sulalewa nayi a wurin..

   **
1:59am
Suleja.

“An gama harkalla ta fada.” Bayan an gama rufe kafuwar motar É—aukar kaya irin wacce take É—aukar kwantena manya manyan nan,  a cikin shi kuwa akwai wutan lantarki, sai fanka, sannan akwai matrest, sannan akwai takeaway da ledar pure water, mata ne yan mata wadanda ba zasu wuce shekaru goma sha zuwa talatin, sai harkokin su suke ana hira.

A cikin gidan nan kuwa Madam Hanan ce zaune da wasu manyan mutane. Tana zaune kafarta akan daya, tana zukar shisha.
“Amma kin san duk harkan nan kowa yasan ni nake É—aukar kalar purple shine aka bawa wani!” Ya fada a fusace.
“Ka daina min haushi Kamar kare, tun Last month nake niman hanyar da zan fita da kayana, amma dan iskanci aka ce min ba zan fitar da su ta jirgi ba, ko bamu yi haka da kai ba Minister? Ai gashi nan ku tambaye shi.

    So dan haka kar wani ya d’aga min murya domin na gama abinda zan yi kuma purple din Matashin dan kasuwan nan ne ya dauka domin duk motoccin da zasu kai mana kaya har Libiya motar shi ce, domin shi daya yake da lasisin fita kasashen Afrika da motar shi, mun gama magana so kowa ya kama gaban shi.”

“Hanan amma ki gaya musu kar su kuskura su taÉ“a green domin zan iya kashe kowani dan iska, sannan kwana nawa zasu isa dubai?”

    Tashi tayi tsaye tare da kunna wani majigi ta fara bayani.
“Daga nan zasu isa bodar Benin, a cikin awowi saba’in da takwas, sannan zasu sauke wannan motar farkon domin na rigada na tura drivers da motar ji kamshi zasu shiga Nijar shi zai kai su Libiya a cikin mako biyu, wato weeks sannan zasu hota kafin su yi tafiyar da zata kai su Algeriya. Daga nan zasu bi jirgin kasa da zai kawo su gaÉ“É“ar teku shi zai kawo su Dubai”

     “Toh mun yarda an gama” inji Alhaji Nura Me Kudi shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na Nijeriya. Da manyan masu rike da mukamin gwamantin kasar, haka gama had’a kome, sannan suka watse tare da fita waje.

*
JF Groups.

Yana zaune Faisal da ya dawo kwana biyu da suka wuce daga Japan ya kalle su.
“Gashi nan, ka duba sosai kafin ka saka hannu a cikin shi”

Karar alerm din gobara ya katse musu aikin da zasu yi, suka fito da sauri wuta ce ta tashi a cikin kamfanin. Haka ma’aikatan kamfanin suka yi ta gudun. Can sai ga yan fire Services. Suka shiga aikin su, cikin ikon Allah wutar ta mutu, kuma aka rasa ta ina Wutar ya tashi, duk da anyi asara amma wannan ba shine abin dubawa ba,  musababbin gobaran ne suka shiga dubawa, dake Ranar Hajiya Atikah bata so office ba. Bilal da Faisal ne suka mata kome, dan haka sai gashi Yayunta maza sun fara korafi. Wanda ya haifar da shigar media al’amarin domin yadda suke maganar akan cewa bata san aikin ta ba, dan haka a sauke ta.

Kwana biyu da faruwan al’amarin aka, Bilal yayi hira da yan Jarida.
“Mr Jikamshi shin rashin kwarewa ne xa Kuma rashin sanin makaman aiki yasa Hajiya Atikah barin gobara ya tashi a cikin JF Group?”

“Ko daya, asalima Hajiya Atikah tana fama da ciwon Asthma yanzu haka tana garin Seoul na kasar Korea, tana jinya shin haka rashin sanin Darajar aikin tane ko rashin lafiya?” Shiru suka yi da ya tambaye su.

Mika hannu wata yar Jarida tayi,.ya mata alama ta mike.
“Mr Jikamshi, shin babu CCTV ne a cikin kamfanin da ba za a iya bibiyar al’amarin?”
“Eh toh maganar gaskiya akwai su, amma ban san taya aka yi haka ba, domin mun samu dukkan kamarorrin  tsaron kamfanin sun lalace, kuma authority na cikin kamfanin basu sanar ba kun ga kenan Hajiya Atikah bata da laifi”

“Mr Jikamshi! Ko kana da labarin, motocin ka da aka samu sun ketara kasar waje? Shin sabon kasuwanci ka fara ko kuma wani abu ne da ba’a son a duniya ta sani. Domin muna da hujjar an ganka tare da Madam Hannah kowa yasan Madam Hanan akwai cases a kanta na Safara da fataucin Yara da mata, sannan a wani gefen an ganku a tare ga shi nan dai Jaridar Defense.” Ta mika mishi jaridar. Sosa goshinsa yayi a ranshi yayi godiya ga Ubangiji da sunan Ummin su bai fito ba.

Sannan ya sake murmushi ya ce musu.
“Gaskiya dan jaridar da ya dauki hoton nan ya kware, dan haka ba zan iya cewa kome akan maganar nan ba”

   “Mr Jikamshi! Watanin shida baya an samu labarin baka kasar nan shin ko akwai inda ka tafi” ran shi ya b’aci dan haka yayi shiru kafin ya ce musu.
“Ina da ikon na tafi duk inda yayi min bai sama dole sai duniya tasan abunda na zab’awa kaina ba, nagode” ya fada bayan ya mike daga kujeran yayi fitar shi.

    Motar shi ya shiga, Faisal ya juya tare da kallon shi.
“Me za ayi yanzun?”
“Na rigada na yi magana akan masu aiki zasu zo daga kasar waje, babu abinda zai faru. Nan da sati Uku inshallah kowa zai dawo bakin aikin shi” ya fada yana me kwanciyar shi a jikin motar, driver ne ya ja motar Mika mishi wayar shi Khalil yayi tare da cewa.
“Sir gashi nan ana son magana da kai” amsar wayar yayi yana faÉ—in.
“Baby kayi kyau a hiran da aka yi da kai, gaskiya ka burge ni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button