NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

“Zaki tashi ki tafi makarantar ko sai na sab’a Miki” ta daka mata tsawa,da gudu ta nufi ban daki tayi brush, sannan tana fitowa ta samu sun kusan tafiya, a gurguje ta saka kayan gida da jakarta ta fita.

   Har zuwa wurin bus din ta shiga, Yaran manyan mutane ne, wasu ko yarbanci basu ji, sai turanci. Kallon ta wata tayi kafin tace mata.
“Rahmah Ishaq ko?” Gyada mata kai tayi, sannan ta ce mata.
“Baki gane ni bane? Shuhudah AbdulRazaq Babatunde. Munyi gasan Hallmark college, gasar fidda wani”
“Na tuna, ya kike toh” Rahmah ta kuma mika mata hannu, haka suka isa makarantar, kowa yana son yayi abota da ita, office din shugaban makarantar aka kaita, tana shiga ta same Hajiya Humaidah Abbas Jikamshi. Cikin girmamawa ta gaishe ta.
“Kece Rahmah Ishaq DaÆ™ayyawa?”
“Yes Ma nice”

“Muga sakamakon ki na wancan makarantar” a hankali ta bude jakarta ta cire ta mika mata.tana gama dubawa ta ce mata.
“Class captain ko?”
“Eh”
“Ok bari a kai ki ajin ku” kiran wani number tayi sannan ta ce mishi.
“Ga sabuwar daliba nan, a bata unifoam da materials din”

     “Ok” kiran masijanta tayi sannan ta mika mishi wasu takardu da ta cika, sannan ta ce mata.
“Allah ya bada sa’a”
“Amin Ya Allah” ta fita a hankali, office din store aka Kai ta, aka bata unifoam da kome, sannan suka nufi aji, kitsonta da suka sauko tayi kokarin mai da shi, amma yaki komawa, dole ta daura hular unifoam din a kan shi.

Kafin ta nemi wuri ta zauna, malamin ajin ya gabatar da ita, sai gashi yan aji suna kallonta, lokaci guda suka fara magana kasa ƙasa.

  Haka malamin ya cigaba da da koyarwa har lokacin shi ya cika. Mikewa dalibai maza suka yi tare da nufar wurin ta, kanta a sunkuye suna dauki book ɗin.

Daya a cikin su ya ja mata gashin kanta, sai da hular kanta ya zame, kamar zata yi kuka, ta dauka. kai hannu bayanta class captain din tayi tare da jan bra dinta, yan ajin suka kwashe da dariya. Ita kan tsoro ya bata motsi, kamar daga sama suka ji ihun yaron da yake mata tsiya, yana kai hannun shi lap dinta.

Wani irin shake mishi dokin wuya Faisal yayi, tare da juyar da shi ya kifa mishi mari sai da ya fadi.

“Meye haka? Wato abinda kuke aikatawa kenan ga dalibai ake zargin makarantar mu ana lalata Yara?” Fitar da shi yayi tare da dauke shi da wani wawan mari, sannan ya kore shi a cikin class din, ba iya shi ba hatta sauran yara Mazan haka ya kore su a cikin ajin. Inda ya kai su har office din Humaidah. Ganin ba zata kore Yaran a makarantar ba, yasa da kanshi ya kore su, sannan ya gaya mata idan ya kuma ganin su, sai ya kashe su.

Yasan Yaran zasu iya aikata sama da haka, kafin ya dawo ajin ya ce musu.
“Daga yau kar na kuma ji ko na gani wani ya tab’a wata mace, idan ka gadama kaje kayi a gaban iyayen ka,amma ba a cikin makarantar mu ba.”

      “Yes sir”

Ita kan Rahmah kanta a sunkuye, bata iya d’ago kai ta kalle shi ba, har ya gama ya fita.
**

Tafiyar kwana da wuni muka yi kafin muka iso babban border kasar Benin da Nigeria. Tashi nayi sakamakon jin ana buga jikin motar da abu, bude ido nayi ina kallon yadda kowa na cikin motar yake zaune.

Abinda ya faru(Flash back)

Bayan sun bata lemon tasha,  ta kama barci,shine suka dauke ta, tare a niman buhu, suka sakata a cikin.

Da farko Maman Steven taso zuba mata maganin bera ne, taci ta mutu, amma daga baya Kawarta ta ce mata.
“Idan mutum ya zage ki, haushi kike ji idan kika kashe ta za a san cewa mutuwa tayi akwai wata Hanan tana sayan Yara, ko zaki kai ta can sai a sayar da ita, idan yaso sai kice ta fita baki sani ba”

Da wannan shawaran suka tsayar da magana aka bata maganin barci, suka kuma kaita gidan Hanan,suka sayar da ita dubu dari bakwai.

Abinda ya faru kenan.


Daga can waje driver ya mikawa sojojin da suke bakin bodar wasu takardu,amma suka nace sai sun ga abinda yake cikin motar, dole suka bude musu aka ga kaya ne da na sawa, anyi blocking inda Yaran da matan suke.

“Ba zaku wuce ba sai mun san meye a cikin motar nan” inji wani Jami’in tsaro,
“Amma ya mun nuna muku, kuma ka gan shi da ido ka babu kome idan kana son muyi magana ne muje gefe” driver ya shiga motar ya dauko wata kwali ya mika mishi.
“Ba zamu karbi cin hanci ba meye a cikin motar da zaku wuce da shi”
“Yallabai ka saurare ni.”
“Ba zan saurare ka ba, sai ka gaya min me ye a cikin motar?….

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:56 – Nuriyyat: 36

“Sanin abin ciki ba zai amfane ka da domin ba sai b’acin rai, dan haka kayi muyi magana irinta manyan masu mutunci da kima” inji driver,
“Matsa ka bani hanya”jam’i’in tsoron ya ture shi, komawa gefe tayi ya kira Hanan.
“Gamu jami’in tsaron kasar Benin sun rike mu” kashe wayar yayi yana murmushi, suna cikin duba motar sai ga kiran shugaban su a wurin.
“Yallabai yan fasa kori ne fa?” Inji Jami’in tsaro, kome aka gaya mishi, dole ya sauka tare da nuna musu hanya.
“Sai ku wuce” ya fada yana huci,
“Ai da ka amshi abinda na baka da bamu yi haka ba, domin na gaya maka cewa wannan kayan akwai masu shi” yayi ga gayawa mutumin maganar banza bayan ya rufe motar,.ya shiga tare da jan motar ya bar wurin.

“Thank God we leave this place,” inji wani mutum da yake kusa da mata, kallon shi tayi, sannan ta ce mishi.
“Baka jin Hausa ne?” Da sauri na lalle ta, sannan na ce mata.
“Kina jin Hausa ne? Domin dan zaman da nayi a Abuja yasani jin turanci. Dukda ba wani jimawa nayi ba, da Sabrina muke Hausa.
“Kema kina jin Hausa kenan?”
“Eh” na fada ina matsawa kusa da ita, kallona tayi tana cewa.
“Meye ya kawo ki nan kina yar karama dake.?” Idanu na ne suka cika da kwalla.
Na kalli kasa kafin nace mata.
“Ban sani ba” daga haka na koma gefenta ina kuka.
“Ya isa, tafiya ce dai bamu sani ba ko zamu isa italiya lafiya ko ba zamu isa ba.”
Shiru nayi ina jin kamar na tab’a jin irin sunan,.amma ban tuna kome ba, shiru nayi tare da jingina da jikin motar, jifa jifa ana hira a cikin motar har aka kwashe awa uku cif sannan aka tsaya, bude motar aka yi tare da bamu abinci me rai da lafiya. A wani tasha,

    Nayi kaɗan murmushi matar tayi sannan ta kawo wani leda ta juye min tana cewa.
“Gashi na zuba miki abincin ki anan ledar, nima na bar Yarinyata kamar ki karama. Gashi tafiya ta had’a ni dake ina iyayenki suke?” D’ago kai nayi tare da sunkuyar da kaina.
“Ban san inda suke ba”
“Toh aka yi kika je suleja har aka yi tafiyar nan dake?”
Hawaye ne ya xubo min sharr, share min tai,.sannan ta ce min.
“Daga nan zamu shiga Nijar ne ta baya, idan ta arewa ne, sai sun kashe kudin da basu mamaki”

Kallon ta nayi ina son nayi magana aka fara kiran mu, haka muka taso. Wani mota aka saka mu a cikin shi. Kallon ta nayi sannan nace mata.
“Yanzun ina zamu?”
Jan numfashi tayi tare da cewa.
“Nijar”

Haka muka shiga motar, ana waka ana addu’a, dake mafi yawan mu a cikin motar kiristoci ne, muna dayawa sai addu’a muke.

Haka muka kwana a hanyar,nayi barci har na godewa Allah, sai da asuba, muka iso border kasar Nijar, tun kafin mu isa sun san da isowar mu, dan haka suka shiga bude mana hanyar da zata shigar da mu Nijar, nan ma sai da muka shiga Nijar jami’an tsaron kasar suka shiga cewa basu yarda damu ba, haka muka sauka tare da barin su da Driver din suna magana, domin motar da ta kwaso mu ba daya bace tana dayawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button