WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
**
Rebecca
Tafiyar da muke cike yake da mugun mugun hatsari, domin kuwa jirgin mu tangal-tangal yake a cikin ruwan,.sai da muka shafe wuni guda a kan ruwan kafin daya daga cikin jiragen ya samu matsala, hmmmmm. Wannan itace asalin tafiyar ajali. Domin kuwa wani abu da bamu san Meye bane ya bangaji jirgin daga kasar ruwa aikuwa dai ga shi jirgin ya tafi ya kifa har da mutanen cikin, masu kokarin sunyi gudun ceton rai, domin sun samu agaji daga sauran jiragen, an dauke su duk da haka ma hatsari ne, sai dai kuma babban tashin hankalin mutanen da basu iya ruwa ba, muna ji muna gani, haka mutane ke nutsewa a cikin ruwa. Sai dai ka ga kumfar jini da ruwa ko kuma ka ga yadda kifaye suke warwason dan Adam, ban san yadda abin zan iya fadar shi ba, amma kuma nayi kuka naji wani irin tsoro a raina, wanda tunda nake ban tab’a jin shi ba, dan haka nayi kuka har kamar zan suma.
  Dakyar muka bar wurin ajiyar zuciya mutumin kusa damu yayi ya ce mana.
“Mun tsalle na farko yanzun kam sai abinda hali yayi domin nan gaba akwai wanda yafi wancan hatsari” kallon Aunty Blessing nayi tare da fashe mata da kuka, shafa bayana tayi tana faÉ—in.
“Zamu tsallaka ina jin haka a raina, dan haka karki yi kuka” haka nayi kuka tare da rungume mata, can gari ya fara duhu, anan ne muka rude wata irin fitila aka kunna wacce take haska mana gaban mu, wato lokacin da muka hau tekun lokacin ruwan ta fara ambaliya da wani irin Rimi, kafin kace me ruwan yayi sama da jiragen mu..
“Kurike katakon da kuke kai sosai karku sake.” Mutumin ya fada haka muka rike Aunty Blessing tana rike dani, kai jama’a naga Bala’in da tunda nazo duniya ban taba ganin shi ba ko ganin shi ba. Haka sauran jiragen suka yi ta kifawa, yayin da mu kuma igiyar ruwa ya kara fisgar mu, tare da cilla jirgin mu can gaba a lokacin tekun ta daina ambaliya, juyawa muka yi muna kallon yadda sauran jiragen suka zuwa wasu da mutane wasu babu mutane, gwanin ban tausayi, a cikin jerage goma sha biyar sai ga shi jirage takwas ne suka tsira suma babu mutane kamar yadda muka taso.
  “Duk akan duniya aka yi wannan tafiyar? Duk akan faffutukar abinda zaka saka a bakin ka ne dan ka rayu, duk akan abinda zaka bukata ne na yau da kullum.!” Inji mutumin yana fada yana share kwalla.
“Ya zamu yi? Kasashen mu basu tsaya mana ba, akan idanun su ake kashe mu, ake tasar mu a gidajen mu, akan idanun su ake wulakanta mu ana cutar da rayukan mu. Basu mana kome sai dai yar tallafin da bai taka kara ya karya ba.
  Haka muke rayuwa kamar marasa galihu, mun fi yarda muzo kasar waje mu bauta musu yadda zasu iya daukar nauyin mu, tir da nahiyar mu” haka ya karshe cikin kuka da b’acin rai.
   Tafiyar da muka yi har na tsawon kwanaki uku a Teku, mun galabaita ainun domin dai ruwan tekun babu dad’i, gishiri ne mun gama cire rai zamu rayu domin shi kan shi matukin jirgin saura kiris ya fadi akasa mu wani ya amshi tuka jirgin, babu me kuzari a cikin mu kowa karfin shi ya Æ™are hka sauran jiragen suma babu me karfi a cikin su. Mutumin kusa damu ya ce.
“Mun kusa” babu wanda ya kula shi haka muka mai da kan mu kasa, bana tunanin akwai me karfin zuciya a cikin mu, har dare a lokacin ne aka samu mutane biyu sun rasu, haka aka jefa su cikin ruwan aka ci gaba da tafiya babu ruwa babu guzuri kai kome ma ya kare saura numfashin mu. Wajen asuba muka fara jin kadan babban jirgi.
“Kai mun iso ga jirgin a gaji nan ya tawo.” D’ago kai nayi tare da kallon inda ake hasko mu da babban fitila.
Komawa jikin aunty nayi na suma, domin wannan shine mafarin zuwa na WATA ALKARYAR…
BAYAN AWOWI SABA’IN DA BIYU. (72 HOURS)
  A hankali na bude idanuna da nake ganin dishi dishi, sake lumshe idanuna nayi domin hasken inda nake yayi yawa,
“Kee!!” Naji ana min magana kamar daga sama, lumshe idanun nayi akaro na uku, na kuma ware su akan su. Mutane biyu ne daya sanye da farin riga da madubi, macen gefen shi tana sanye da riga blue.
“Dr an gama binciken kome akanta saura a mai da ita dakin da zata zauna, sannan a yadda muka samu sakamakon Æ™waÆ™walwar ta akwai dan jinyar da aka yi domin jinin ta akwai sauran kwayoyin sinadirai na lodine.” Inji Nurse Clara, wacce sunanta yake manne a bajin rigar ta,
   “Toh yanzun ya zamu yi da ita, tunda babu abinda zata yi mana, sai dai a kaita Red House ba mamaki akwai shashin da zata zauna. Yanzu ki mata allura sai ki mika musu wannan report din.” Ya fada cike da takaici me kunshe da bakin cikin, domin Dr Austin Francis, ya tsani a Sara, a duniyar shi.
  Abinda ya faru kuwa ana kawo musu dauki bayan ta suma, Aunty Blessing ta mika takardunta, da na Rebecca, dama aikin ta kenan tayi supervisor din wadanda aka dauko su daga Nigeria, musamman yan mata, dan haka tana mika Rebecca ta wuce Abu Dhabi na kasar Dubai, a cikin teams din da aka shigo da su Italia yan mata goma cib suka yi survive, kuma baki daya team din Purple ne wato Jikamshi.
Abu Dhabi 0:9pm
Taro ne na manyan fitattun yan kasuwa, a cikin su kuwa har da Hanan. Dan haka a zuwanta Abu Dhabi tazo amadadin jikamshi.
  Yadda kasuwancin yake, da kuma yadda duniya da United Nations suka dakatar da shi a idanun duniya ba karamin al’amari bane, domin kasuwanci ne da tafi kowani kasuwanci kawo kudi. A zahirance kudi ake Zubawa tare da zabar each colour na abu, sannan idan aka zab’a. Za a dibi yan mata za a saka idanu akan su, sannan kuma idan aka dauko su, za’a ta bibiyar al’amarin su har a ga nasarar su, lokacin da Hanan ta bawa jikamshi ya zabi purple wasu yan mata uku ne a cikin su.
  Maman Steven da Kawarta sun kai Rebecca, kallonta Hanan tayi sai ta karawa jikamshi ita a cikin yan mata uku nan, sai dai ba a son a barsu a wuri guda, domin idan suka fahimci akwai dalilin haka zasu iya zama yan tawaye, koda sun shigo italia ba zasu yi abinda da ce ba. Dan haka aka rarraba su a jiragen ruwan kuma ikon Allah baki daya nashin sun tsira. Sai dai akwai kasada ko wani hatsarin da zasu kuma fuskanta.
Musamman ana shigowa da yan matan gamayyar kungiyar karuwai ba cikin kasar italy ta kwashi yan mata biyu. Daya kuma wata kungiyar Model sun dauke ta, sakamakon tana da tsawo kuma bata da jiki haƙa zai taimaka musu, sai ita kuma Rebecca kungiyar Red line life orphanage sun dauke ta. za ayi iya cewa yan matan da suka kasance. Tarah, Rebecca, Chioma, Abigel, sune cik da aka dauke su sannan idan har suka bada kai ga yadda ake bukata za su iya tsira a ce shekara biyu masu zuwa.
 Sannan duk kudin da za a tura dole za a turawa jikamshi ne, sai dai da alamu shi kanshi Mr Jikamshi bai san da wannan badakalar ba, kuma taya zai sani.
  Sannan asalin taron ana yi ne a mugun tsirace, domin kuwa ba a son duniya ta fahimci halin da ake ciki, sannan manyan kasashe gudu biyu na duniya suna jagorantar wannan yanayin. United States, sai France. Sune suke jan ragamar, a gefe akwai hadin guiwar kasashen nahiyar Afirka, da gamayyar daular Larabawa, wadannan sune mutanen fa suke daukar manyan kasadar.
Murmushi Hanan tayi lokacin da ta isa gaban Mr Ardu.