WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
A zaman da nayi a cikin jirgin, na bawa kowa wahala, sannan suma mutane da suke cikin tankin nasaka sun cire su, domin tunda na sumar da ogan su, na samu yancin koma da yasha bakar wahala, haka yasa shi gayawa yaran shi ni ba Kanwar lasa bace.
  A hankali muka sauka sai lokacin aka fitar da Kayan da suka shigo da su, ni kuma aka hada ni da Ayelo, ya kai ni gidan marayun. Wannan shine karon farko da nazo Lagos. Na sha kallo sosai.
   Tunda na isa gidan marayun na fahimci, hannun gwamnati bai iso kan su ba, dan haka na shiga taimaka musu da abinda Allah ya bani, tare da sayar da wasu daga cikin kayan da Madam Tola ta saka min, zan iya cewa wannan shine dalilin da yasani hakura da niman ahalina. Na zauna domin suna bukata na.
   Zaman haka ba zai min ba, dan haka na shiga fita niman aiki koda shara ne, wani lokacin haka zan gama yawona na dawo, daman ma mutanen fa suke kula da marayun suma ba kanannun kokari suke ba. Kuma suna nuna min muhimmancin rayuwa da hakuri da abinda Allah ya bamu, duk da kiristoci ne kamar ni, amma ina jin kamar dacen da nayi ne na samun mutanen kirki a tare da Ni.
 Sai da na kwashe wata biyu ana cikin ukun ne ayola ya kawo min labarin gidan abincin da yake can ikeja. Kamar ba zanje ba haka na shirya muka tafi, cikin ikon Allah kuwa matar ta Kalle ni sannan ta tambaye ni.
“Kin iya abinci?”
“A’a sai idan zan koya a wurin ki ko kuma ki bani aikin shigar miki da kuÉ—in”
“Ok koyan xai É—auki lokaci, zan baki aikin kai abincin per day 2500”
“Nagode sosai”
Sannan na juya nayiwa Ayola godiya, daga ranar na fara aiki,kuma matar bata hanani shigar da nake ba, tambaya tayi suna na, nace mata.
“Rubi!”
Da yamma take tashi tana tashi na wuce gida, da niki-nikin kayan abinci, haka na kawo gida ni da Yan uwana marayu muka ci.
Washi gari.
Da wuri na iso gidan, ina zuwa na samu ma’aikata guda biyu, kallona daya tayi kafin ta ce min.
“Sunanki!”
“Rubi”
“Natasha” kallon ta nayi domin irin kamar hafcase ce, dayar kuma Bayarabiya ce, Ajide sunanta babu laifi duk sun fini shekaru.
Ganin yadda ya tara musu a cikin gidan abincin yasaka gidan abincin ya kara samun albarka domin kuwa, dukkan mu babu na yarwa.
 **
“Ki nimo min ita nayi Miki alkawarin zan baki kyauta na musamman don Allah ki nimo min ita” ya fada kamar zai yi yayya.
Kashe wayar yayi tare da dafe gefen kirjin shi.
“Lafiya?” Inji Jamilah,
“Lau” ya ce mata, domin yanzun shi da Jamilah sun fi dinke kamar saurayi da budurwa, abinda ya haifar da ganin kamar budurwan shi ce ita, a hankali ya fitar da ita kowa ya santa uwa Uba yadda take wanka da kwalliya ba zaka tab’a yarda Jamilah ce da kazamin nan Yayan Ubanta yayi mata fyade ba, karfi da yaji sai da ta shiga jikin Mr Jikamshi,.ta yadda take sayan hannun Jari a kamfanin shi sai da ya mata fada, sannan ta koma sai da ta saye na kamfanin JF Group.
  Haka ba karamin d’aga musu hankali yayi ba, domin daga waje take lokaci guda ta saye kome na su, Kudinta yafi nasu yawa, a wannan lokacin aka fara niman tsayar da sabon Chairman a kamfanin, idan tayi ruwa tayi tsaki tace ita zata tsaya, cike da Mamaki suka saka aka fara bincike akanta, anan suka samu ai suna da kyakkyawar dukiya tun daga london har Nijeriya, wannan yasa jikin su yayi sanyi suna ji suna gani kuma Bilal ya kara goya mata baya, haka yasa baki daya yarinyar ta kuma haukacewa.
  Ita kan Ammyn Addu’a take mata domin tasan Jamilah ba jamilarta bane da ta sani, wannan bata jin magana bata jin kome sai abinda ranta yake so, ta kwashe rabonta ta zuba a hannun jari tana kuma harin na kannen ta, da ta mata fada fushi tayi ta bar gidan, abin yayiwa Ammyh ciwo haka yasa jinin ta yayi mugun hawa, daga Rahmah da take Abuja sai Wasilah sune Ammyn take samun sawaba a gare su.
*
” Ki dawo gida, kin ji ina kewar ki auta na” mika mata hannu nayi xan tab’a matar ba farka, ina jiyo kiran sallah daga can nesa, kai na ne ya sara min…
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/4/22, 08:27 – Nuriyyat: 55
Safe kaina nayi tare da jin kamar zai fashe na kurawa dakin da nake Idanu, sakamakon hasken da yake shigo min.
   “Auta?” Na tambayi kaina, tashi nayi tare da kallon waje, zama nayi a wurin har gari ya fara wayewa. Kafin na fita na ja ruwa a cikin rijiya, sannan na wuce kitchen na hada wuta na daura tukunyar abincin safe, na wuce ban daki nayi wanka.
 Mama ta fito ta cigaba da aikin.
“Rebecca kin tashi lafiya!”
“Lafiya lau mama” na fada ina wucewa daki na shirya tsaf, sannan na nufi wurin aikina, a da ina cikin fargaba dawowa na, amma a yanzu ba na jin kome, asalima kokari nake na zauna da mutanen da suke tare dani.
   Musamman da na fahimci nice sa ran su, domin a da sai matan da suke gidan su fita tare da niman taimako a church, amma yanzu nice kawai zan fita na kawo abinda zamu ci.
 Haka na shirya na tawo har wurin aikina, na kama abinda ke gabana.
  A hankali kome yake tafiya,ita kanta matar da take da gidan Abincin tana matukar mutuntani sakamakon yadda nake da sakin fuska, wasa da dariya haka ya janyo masu sayan abincin sosai.
 Ga alkhairin da nake samu abu daya naki yarda shi,duk da ina shigar banza,toh ya zanyi kananun gown ne sai riga da wando sune kawai abinda nake iya sakewa a cikin su,dan ko skirt takura min yake, haka yasa maza dayawa suke amfani da damar su dan su shigo min da shirme rayuwata.
**
Tunda Rahmah ta koma Abuja, Malam Faisal yake wanke kafar shi ya tafi can yayi budirin shi, abin tausayi yarinyar Allah ya daura mata hakuri akan shi, duk da gidan shi ne,an saka kome har da Security. Sannan a gidan Layinah itama tana can da mijinta dan Gombe,ya makale mata.
   A yau asabar tun safe ta tafi makarantar, bata dawo ba sai karfe biyu na Rahmah. Tana shigowa gidan ta hango motar shi.
  Gabanta ne ya fadi, wayarta ne yayi kara ta ga number Wasilah. Dauka tayi bayan ta bude kofar ta shiga da sallama. Murmushi ta sakar mishi, sannan ya amsa maganar Wasailah.
“Ya kike ya Ammyn mu”
“Muna lafiya ya kike, dama Ammyn ce ta ce na kira ki ku gaisa” zama tayi tare da cewa.
“Wasilah Jamilah ko?” Domin tasan matukar Ammyn ta saka a kirata zata kawo karan Jamilah ce. Cikin karfin zuciya wasilah ta ce mata.
“Eh gata nan”
Muryan Ammyn taji zuciyar ta, tayi wani irin rauni.
“Rahmah ki kula da Yan uwanki, karki bari suyi maraici, ina jin kewar ku, ina kewar ku. Ina ga rokon Allah ya bani aron numfashi ko muryan Auta naji”wani irin kuka ne ya kuma kama ta, haka ta ja hancinta kafin ta ce mata.
“Ammyn kin manta kiyi min alkawarin ba zaki kuma min irin wannan maganar ba? Kin manta kin ce ba zaki kuma maimaita min irin wannan maganar ba. Ammyn kiyi hakuri”
Tana jin muryan Wasilah na kuka, domin tasan Ammyn na kuka ne yasa itama Wasilah take kuka, a hankali ya amshi wayar tare da kashewa fadawa kirjin shi tayi tare da fashewa da kuka, tana wani irin kuka me ban tausayi.
“Ya isa haka”
“Idan ta mutu waye zai kula da mu? Bamu da kowa sai Allah, sai ita amma a kullum burin ta Jamilah da Rabi’ah, kullum kuka take akan su Ya Faisal gaya min ya zanyi? Kasan yadda nake jin kuncie? Kasan yadda nake jin tashin hankali? A duk lokacin da Ammyn tace tana jin kewar mu a tare da ita ina shiga tashin hankali domin..”
D’ago kanta tayi tare da hade bakin su, ya jima kwarai yana lallubeta, kafin ya dauke ta zube dakin su, ya gwangwaje matar shi kamar ba gobe, kafin ya samu nutsuwa, kara rungume ta yayi yana jin wani irin kaunarta a ran shi. Hakurin da take yi dashi yayi yawa, duk yadda ya biyar da ita haka zata biye shi kuma duk abinda zai yi da ita bata musu,haka ta gama murza yar matar shi kafin ya koma gefe ya barta tayi barci.