NOVELS

WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL

  • Sai na ci Ubanki”
    Ta taso kan Wasailah wani kallon shekeke wasilah ta mata kafin ta ce.
    “Na rantse da ayi bikin murnar watsewar hakoranki Allah ya baki sa’a”  ita kan Ammyn abin su ya ishe ta bata iya magana sai kallo da ido,  baki daya kamar wasu kaji ko kishiyoyin juna.  Sai da Aaman yaja hannun wasilah suka fita,yayi mata magana tana d’agawa Jamilah kafa, ko bayan tafiya shi. tana komawa cikin asibitin Jamilah ta shiga kanannun magana da zagin Wasilah har da kiranta yar iska idanun ya bude. Idanun ta cike da kwalla ta kalli Ammyn su. Wani irin kalar tausayi tabawa Wasilah yasa bata kula Jamilah.

Irin wannan zaman doya da manja ba karamin d’agawa Ammyn hankali yake ba, takan zaunar da Jamilah tayi mata nasiha,amma a banza asalima kamar tinxira ta ake, dan ma Bilal yayi wani hikima duk inda zasu shiga ana bibiyar rayuwar su.

    **
JIKAMSHI HOUSE
“Ba zai yiwu ace karfi da Yaji bare shi sai cigaba da rike mu ba, taya haka zai kasance? Tsoron Jamilah kuke ji da zaku zuba mata ido” inji Hajiya Turai,

“Idan basu ji tsoro na ba, zasu ji tsoron karya su da zan yi.  Kuma tun wuri ki iya kalaman ki, ni ba Hajiya Atikah bace wanda yaga ba zai iya  zama dani ba, ya kara gaba” ta fada bayan ta zauna a kujeran ta, tana juyawa da shi.

Kamar  ruwa ya cinye su, Alhaji Adamu Abbas Jikamshi ya ce mata.
“Yarinya na”
“Rike maganar ka, karka kuma alakanta ni da kai har abada. Ina jin ka”
“Dama akwai turawan dasu zo ne domin karo”. Kallon shi tayi kafin tace mishi.
“Karon da ake samu a kamfanin nan iya tam dubu arba’in ne, shi kuma karon da MR William yake bukata dubu dari biyar ne zaka iya samo mishi a kasa da wata daya?”

   Ta fada tana gyara farcen ta, duk maganar da take bata d’ago kai ba, balle yasa ran zata kalle shi.
“Ok toh dama na zata zamu iya basu dubu arba’in din ne sauran”
Dariya tayi sannan ta kalli matan.
“Ku fahimtar da shi mana”
“Eh gaskiya ba zai yiwu ba, domin shima zai kai kasuwar duniya ce, idan muka bashi dubu arba’in ina zamu samu tam dubu dari huÉ—u da sittin? Gaskiya ko duba ban ki ba, idan za a tura JIKAMSHI MENIRAL RESOURCES BA, idan yaso sai su biya mu a cikin nasu ko Jamilah.”

“Gaskiya Hajiya Murjanatu kina da kaifin brain haka ma na gayawa Faisal kasancewar Bilal baya nan dole Faisal ne me kula da kome, idan har nace xan yi gaban kai na maybe abun ba zai min dadi ba, tam dubu arba’in mu buga lissafin shi nawa zai baku. Sannan ina ganin idan akwai me yunkurin kai min farmaki ya daina” ta kurawa Alhaji Abubakar da Ambassador Abdulkadir Idanu tana murmushi.
“Ina sane da harin da a kai asibiti, an farmake ni ne, idan kuma wani abu ta faru, kuyi tunanin abinda zai faru mana. Kowani karfin motsina yana tafiya ne da karfin bugun zuciyar ku, sannan ban sani ba amma dole ayi daya cikin biyu Imma a daina Imma na tab’a masu hannun jari a kamfanin mu, su kuma zasu iya razana su cire dukiyar su….🔥

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/5/22, 18:28 – Nuriyyat: 59
Tana gama fadar haka ta mike tare da gyara zaman rigar ta, tana kallon su, kafin ta fice abin ta. Cikin nutsuwa domin ta gama abinda zata yi duk inda zata kuma cewa wani abu tabbas ba zai musu kyau ba.

A bakin kofar fita daga cikin dakin taron suka hadu da Irfan, kallon junan su. Nuna mishi hanya tayi zata wuce. Murmushin gefen baki yayi mata.
“Oh kece Jamilah Ishaq ko? Ex girlfriend din Namir”  kallon shi tayi daga sama har kasa ta ce mishi.
“Yeap! Akwai wani abu ne?”
“No kawai gani nayi kamar zamu iya kula harkalla!”
Dariya tayi tare da kallon shi kafin ta ce mishi.
“Kai da har yanzu Mamarka take goyon ka zan yi harkalla da kai? Duba da kai, soyayyar ka da Nadrah Ruma boye shi kake ai ko? Toh tawa ce zaka iya bayyana shi?” Ta fada tana kai hannun ta habb’atar ta.
“Ko da yake naga kamar ita Mamarka bata san da haka ba”  ta fada tana wuce shi. Bin bayan ta yayi da wani irin kallo, yana jin wani abu a ran shi. Tabbas idan har ya barta ta tafi haka yayi asara. Sai yaga me yasa suke makale da juna ita da Bilal.

     **
Yau kan da wuri na fito, ina sauka a bus shagon abincin na shiga tare da cewa.
“Natasha ku bani wani abu na ci mana”
“Trouble marke Barka da zuwa” ta fada bayan ta kawo min abin karyawa, soyayyan kwai da dankali sai shayi me kauri, na zauna na fara ci ina. Bata amsa duk abinda ta faÉ—a. Ina gamawa na ajiye mata kuÉ—in daidai shigowar Hajiyar da take da shagon tare da alaja.

   “Ina kwana alaja bari na shiga wurin aikin” na fada ina kokarin barin shagon.
“Baki ga mutane bane!” Inji ita me gidan Abincin.
“Kiyi hakuri” na fada ina fita, baki daya na kasa gane inda na san fuskarta amma tabbas nasan fuskar matar.  Haka na fita na shiga kamfanin a duniya ka zauna lafiya da kowa yana da dad’i, abinda ya faru kenan.

Domin baki daya zaman lafiya muke da kowa na kamfanin. Idan da ma me wani damu su, suka sani amma daga matan har mazan basu da matsala.

   Yallabai Faisal kuwa yadda nake addaban Rayuwar shi da fitina yasa shi daina zuwa office din a gidan shi yake aikin shi, har muka samu wata biyu. Ana shirin shiga na uku.

   **
Abuja.

Da wuri suka gama jarabwar su, karfin hali ne kawai da na zuciya, musamman da ya rage mata saura shekara daya ta gama karatu, ga Wasilah itama an turo ta Law School da yake nan Abuja.

   A gajiye ta shiga cikin gidan, bayan ta fito a motar da yake kaita makarantar. Ta bude ta shiga falon.
“Sannun Ya Rahmah ya jikin ki?”
“Da sauki mun kammala ai, yau zan koma lagos, ba wani kulawa Ammyn take samu a wurin Jamilah ba”
“Hmm”wasilah tace bayan ta tabe bakin ta.
“Zoki hada min kayana”
“Toh” ta shiga kitchen ta zuba ruwan zafi domin tafi gane shan shi,akan cin abincin domin wani irin laulayi take yi, idan ba ruwan tea ba, bata cin kome.

   Haka ta gama hada mata kayan ta, sannan ta kalli agogon dakin, itama ta had’a kayan ta. Sai da suka yi sallah azhar a gidan kafin suka wuce airport, suna zuwa Allah ya taimaka suka samu jirgin lagos. Suna biya duk abinda zasu biya suka biyo jirgin.

   **
Yau jumma’a an tashi da ruwa garin, dan haka ana tashi a aiki na nufi wani mall na mana sayayya tunda na samu albashi.

      Ina shiga cikin mall din naga wata mata zata fadi, da sauri na isa wurinta na rike ta.
“Sannun keda waye kike zo? Kinsan baki da lafiya ai zaman gida zaki bai dace kizo nan ba”  na fada mata, rike ta nayi ta zauna a kujeran da aka tanadarwa sabida irin haka.

   Durkusawa nayi a gaban ta.
“Keda waye kuka zo? Ban ga wani ya nuna alamun shi naki ne ba? Waye ya zo tare da ke?” Na fada ina waige waige.
Har lokacin bata yi magana ba, kallon juna muka yi, gabana ya fadi sunkiyar da kai nayi jikina yana rawa.
“Hmm! Hmm! Ina ne gidanki yake na kai ki”

    Mikewa tayi zata tashi na rike ta, muka fita tana ta dube dube, tare taxi nayi sannan na sakata,sannan na koma cikin mall din na gaya musu tare da basu number wayata koda dan ta zai zo, na dawo wurin motar muka wuce Dakyar ta gaya min inda suke zaune, aka kai mu. Na biya kuɗin muka shiga cikin gidan. Har lokacin bata yi min magana ba, sai kallo na sa take time to time.
“Zan sha ruwan?”
Ta fada min, kallon ta nayi kafin na kalli kofar da nake da yakinin kitchen ne, na shiga tare da dube dube har na sami ruwa na kawo mata. Waya ta ce tayi kara na É—auka.
“Ok gani nan zuwa”
“Mama zan tafi ana nima na a gida” na fita bayan na mata sallama.
“Baki gaya min sunanki ba?”
Murmushi nayi tare da cewa.
“Rebecca”
Sannan na fita da sauri, haka kawai nake jin bugun zuciyata tana yawan karuwa idan naji muryanta, har na fito bakin get din gidan, ta burge ni ba laifi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button