WATA ALKARYAR COMPLETE NOVEL
   Ni kuwa a dadina nayi ta shagwab’e mishi yana kara birkice min ana tab’a hannun babu wani zafi ma fasa ihu har da kamar xan fadi.
  “Ku mata hankali mana! Baku san taba jin zafi bane sannun kin ji ba zan kuma ji Miki ciwo ba kin ji” ga abin dariya ga takaici haka nayi ta bashi wahala har aka gama ya je ya biya kudin yana gamawa ya zo ya rike hannuna. Aikuwa na coge.
“Allah ba zan tafi ba sai ka É—auki Ni” haka ya dauke ni, har wurin motar ya sani.
   Koda muka isa gida hankalin su Umma ya tashi.
“Ya Bilal ma’aikaciyar ka ce ko yar reno aka baka?”
“Wayyo Allah na, Wayyo hannuna! Na shiga uku Wayyo barci Wayyo takaici” na fada ina rusa mishi kuka, dan dole ya wuce dani dakina Umma ta ce mishi.
“Kaita dakina” haka ya wuce dani dakinta, kai na sha tararrayya domin kamar ta mai da ciwon jikinta, haka take ya min hidima, dake ita ce ban wani narke ba, har nayi barci.
“Wash umma nima barci zan yi tayi nata saura nawa”
   Hararan shi tayi tana cewa..
“Fita ka bani wuri” bayan fitar shi ta dauki wayar ta, ta fita.
“Atikah yaxo da yarinyar da ta taimaka mishi da matar Faisal. Sai dai bana tunanin kome yadda ya rude akan ta ina tsoron kar wani abu ya faru da yarinyar dan dole zasu bibiye rayuwar ta.”
“Ƙarki damu, sai dai ya kika ganin shi da ita sun dace?” Inji Ummi,
“Idan nace miki wani abu nayi karya, sai dai ita din zinari ce a cikin tagula, domin ta sanya shi yin abubuwan da sauran matan basu samu ba.”
Kashe wayar tayi ta koma cikin dakin.
 Washi gari.
Kawun shi da matar shi ne suka shigo, kai naga kauna, kallona matar tayi cikin harshen turanci ta ce min.
“Rebecca ko? Ke Christ ce?” Gyada mata kai nayi,ikon Allah yaushe rabona da naje church. Jana tayi ta kai ni dakin yarta, ta nuna min har da hoton auren su da shi. Wani abu ta dauko ta mika min.
“Inji Yarinya ta tace min”
“Duk ranar da Gong Yoo yazo da mace, don Allah na bata wannan.” Amsa nayi ina kallon Abu.
“Nagode sosai”
“Ki dauka Kema Yar mu ce, da naganki sai naji ina da kwarin gwiwar da na rasa, sai naji kamar yata tana raye. Ki kula da shi, domin shi ta fara kirana da Umma”
Hawaye ne ya zubo min, ta bani tausayi.
Haka na fito har zuwa waje tana biye dani. Sai jana take.
Bayan na koma cikin gida, ina shiga na samu baya falo,ai kuwa na wuce dakin da aka sauke ni, naje na ajiye kayan. Sannan na wuce niman shi a can wajen ghdan na same shi a wani falo, me ɗauke da wasu kujeru kamar dakin taro. Yana zaune dauke da wata glass cup Amma me zubin mug, ruwan juice ne a cikin mug din.
Shiga nayi na bubbuga kofar, ina kallon shi. Ina hura iskar bakina.
“Na shigo”
“Ki koma” ya fada bayan ya janye idanun shi a kaina. Kamar ba zan shiga ba. Sai na shiga kuma na ja kujera na zauna ina kallon shi. “Nazo ne muyi magana”
     “Hmm!”
“Dazun na shiga wurin Maman Ha Na. Naga hoton ku. Amma tafi ka kyau”. A ran shi ya ce.
Trouble maker
Tashi nayi na koma inda yake tsaye, nima na tsaya kamar yadda ya tsaya.
“Kasan me?”
“Ina xan san me tunda ba akuya bane ne ni da zan san me?”
“Ai kasan muuuuu?”
Banza yayi min, na kuma ce mishi.
“Wau wau!!!”
“Zan miki duka”
“Kai a duniya akwai wanda ka rena kuwa bayan Ni? Kome sai kace zaka dake ni, toh gani nan dake ni” na fada ina muskutawa kusa da shi.
“Zan Miki duka wallahi”
Hade rai nayi ina hararan gefe, sai kanannun magana nake yana jina, bai da lokaci na, ya jima yana nazari amma sabida fitina irin nawa da Rigima Sai saka shi magana nake, kamar wata yar yarinya. Kallona tayi lokacin da na dauki juice din shi zan sha daidai ana kiran shi a waya..🔥
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/8/22, 08:24 – My Mtn Number: 64
Shi kansa bai san kudirina ba,ina dauka na kafa kaina, sai da na shanye tass yana can yana waya.
      Juyowa nayi naga yana rarrabe min gida biyu, sake kallon shi nayi lokacin sa naji yana faɗin.
“Banza ka gaya min reno kuka bani dama haka take addabar rayuwarka muna dawowa zan sallame ta ba gaji wallhi.”
“Rigibbbb” yaji kara a bayan shi, juyawa yayi tare da cewa.
“Na shiga uku! Ta shanye?”
“Me fa?”
“Soju mana!”
“Uban me kake da giya?”
“Ina dakin walima ne na tuna da Ha Na, shine Nazo da shi ba wai na sha bane”
“Sai ka san yadda zaka yi da har mutane dan kasan tasha kuma ta bugu hala babu sirki ma a cikin shi kawai zallar shi ne”
“Ai kamar ka sani” haka ya d’ago ni, sannan ya kwantar dani a saman table din hall din, ya jima a wurin zaune tun hantsi har karfe uku saura na farka ina Kalle kalle, ina tashi amai ya taso min sai da na amayar da shi, kallona yayi tare da girgiza kai ya ce min.
“Kazamar banza” shafa cikina nayi na ce mishi.
“Kai ka ji wurin” fita yayi abin shi na bi bayan shi ina tambayar shi.
“Wai hala zaman gadina kayi? Lallai kana da kirki. Gaya min me kake so na yi dan na biyaka da kirkinka” juyowa yayi da kyau sannan ya ce mishi.
“Ki ja bakin ki nan Kiyi shiru”
“Duk yadda kace Mr Tall” buge min baki yayi cikin takaici yana me min mugun kallo.
  “Hakuri” na fada ina kallon hannuna, cikin gidan muka nufa. Kallon mu Mahaifiyar shi tayi tare da cewa.
“Na damu da ban ganku ba”
“Auta muna can bayan gidan can, na ga Mr Jikamshi yana kwalbewa shi ne..” buge min baki yayi.
“Wayyo Allah” na rike bakina,
“Bana son cin zali, ka saka yarinya a gaba da mugun ta, Jeki huta” da sauri ba wuce sai da na juya sannan na mishi gwalo.
…
Sai da muka yi kwana uku, kullum sai na takale shi da tsokana ko da magana, tun yana murde min kunnen yana buge min baki ya hakura, sai dai yar Black Beauty din nan ne take dan jin haushi na.
   Yau tun safe na tashi naji labarin ya yi tafiya, naji babu dad’i ai ko ba kome zai gaya min zai tafi ban ce kome ba, can yamma Umma da Kannen shi suka saka ni a gaba muka fita, kaya ne irin na yayi lastest aka saka ni nayi ta zabe masu mugun kyau da sweater coat na kwalliya. Sai wurin kaya makeup, na kwashi kayan sosai. Amma ban san yadda ake amfani da shi ba, dan dole na kalli Kanwar shi yar Autar su.
  “Zaki koya min yadda ake amfani da shi?” Na tambaye ta.
“Me zai hana”
Gyada min kai tayi muka cigaba da diban kaya, sai da muka gama na ce mata.
“Bamu biya kudi ba”
“Shagon Oppa ne”
“Kai Haba? Shagon shine?” Na tambaye ta, ina dariya.
“Eh da gaske”
Mikawa masu aikin shagon kayan nayi na nade hannun rigana, nayi wani kass da hannuna, dama na zata kudin Umma ne zai yi ciwo ashe na yallabai ne. Kawai na shiga duban kaya kamar ban san inda ke min ciwo ba, Mimih zata min magana, Umma ta hanata, haka na kwashi kaya na fitar hankali. Ina nishi na fitar da su. Tare da taimakon masu aiki takalma kuwa tsabar Zalama har da jaka na dina.
Sai da na zauna Umma ta ce min.
“Sannu kin ji sun ishe ki ko zaki kara?” Kallon shagon nayi naga kar nayi rashin hankali na ce.
“Sun isa”
Haka muka dawo gida da kaya niki-niki, na shiga tunda na shiga cikin gidan na wuce dakin. Da kayan na had’a su baki daya na saka a drower na kwanta sai barci.