BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Wani tausayinta ne ya dirar mata da tunanin magangannunta na asibiti,

To ko dai tun a lokacin aka ce za.a yi masu aure? Ko me fushi Walyn ke nufi a lokacin? 

Kafadunta ta daga tana fadin” damanfa ba kaunana take ba, ba fadan wannan take ba, me yiwuwa na mata wani abin ne dan ni banma san me take fada a fadan nata ba????????‍♀️,

Ya jima tsaye kofar gidan nasa,

Ba wata anguwar manyan masu kudi bace , aman anguwar sai ka shigeta zaka ringa cin karo da gidaje na alfahari,

A boye take , gashi a bakin gari take, bai jima da gama gine gine a anguwar ba, inda tuni an fara kama hayar gidajen,

Tankamemiyar vila din da daman can ya ginata ne dominsa ya danna horn inda mai gadi ya bude masa dan ya san shi ne kawai mai zuwa,

Gidan du shukoki ne an yi tsari da su an masu kwaliya waje waje, sai wajen ajiyar motoci can kasan wata runfa, 

Kana shiga zaka ga kanka a ciki, ko.ina madubi ne gaka tun daga kanka har kafarka,

A hankali ya sauka inda yaronsa ya dauko jakar da ya zo da ita yana biye da shi har suka sadu da accenseur din gidan ,

Shiga ya yi ya dana number etage hawa na shida wanda yake na karshe inda dakinsa yake, 

Su ya ajiye su suka sauka, sai da ya kai masa jakar har kofar dakinsa sannan ya juya ya tafi,

Panneau  solaire ne le aiki a gaba daya gidan, sai katon inji irin na ma.aikata dake boye nesa da dakunnan dan zafinsa ko kara kar ya damu kowa,

A hankali ya shiga da adu.a, dan bai taba zuwa ya kwana gidan ba, 

Dakunnan dake bangaren nasa ya leleka, komai ya yi masa kamar yanda tsarin rayiwarsa yake, mutun mai son farin abu, sai dan maroon da aka sirka dan kar farin ya yi yawa,

Dawowa ya yi  dakin da ya fi girma wanda shi ne dakin bacinsa ya shiga ya bude wajen kakinsa, domin a gidan nan abinda babu kawai mutane ne, mutanenma masu gidan, dan kuwa du abin bukatarsa ya saka, sannan gidan a boye yake bayi niyar zama cikinsa kwana kusa ba, kai shi ya yi niyar ya ringa sauke mutanensa idan zasu yi baban meeting da sojoji na harkar aikinsa dai da sauransu, ya so gidan ya zama na sirri, aman baki daya walyn ta fitar masa da wancen gidan a ransa, baya jin zai kuma rayuwa cikinsa domin ta fitine shi a gidan nan, 

Ya yi masa tsarin da zasu rayu tamkar soyayar fari, tsaftataciyar soyaya sai dai bata zauna bama bale ta gina hakan ,

Wannan gidan ya yi shi da wani irin gini ne mai dakuna barkatai, sannan du wani bangare akoy hanyar da zata sadaka da bangarensa, inda maduban bangarensa bulet ba zai ratsa su ba, 

Kai an fa zuba nema a gidan dake anguwar da ba wanda zai hasaso irin gida tamfatsetse haka a wajen  ba wato *AEROPORT*,

Sai da ya gama uzuririkansa, kafin ya zauna ya hada wayoyin da ya shigo da su da layikansa ya jona ya haye saman bed dinsa domin zuwa lokacin dare ya yi sosai,

*idan kana fada, tsoro nake ji, dan Allah ka daina*, shine abinda ya fado masa, na daina fada?

Ya fada , to ni mafadaci ne ? 

(Fans wardugu ya ce wai shi mafadaci ne ?)

Haka ya juya ya kuma juyowa yana duban memory card dinsa, wace a cikinta akoy hotonta da ta juya da niyar zuwa wajen zama a wajen diner Alhinayett,

Alhinayett, sai da ya ambaci sunnan ta fado masa a rai, aminiya, na san kin neme ni,

Kwonciya ya yi da tunanin a gobe gobe ba sai an kai nesa ba zai yiwa Ayya dukan abinda ta bukata a kawo yarinyar nan kowama ya huta, domin duda tace ba zata fita haka ba, shi kam ta dawo kusa ya fi, 

Idannuwansa ya lumshe, yanda da ya rungumeta ta kwonta a jikinsa ya fado masa a rai, 

Mikewa ya yi yana tsaki, a kasan zuciyarsa ya furta ba dole ba ita da ta taba aure! Malama ki bar min rayuwa na huta hakannan! 

Haushin kansa yake ji irin yanda ya zauna tunanin wannan yar yarinyar! Dan haka ya mike ya saka kakinsa na aiki, ya dauki karamar wayar da ya saka layinsa na aiki ya yi kiran commisariar da ta fi kusa da gidansa ya tambaya wa.inda suka fito raful da hanyar da suka bi,

Haka ya fito a katon babut dinsa dake gidan ya tarbe su, daya daga cikinsu ya sauka ya dauki  babur din dan kai shi ma.aikata su kuwa suka shiga bin anguwa anguwa sunna kama du wani mai laifi, da wanda ya cika dare kuma bashi da takarda, inda su ne har su plastomo, su rond poind 6em, du wani lungu na yan duniyar da basu da damar zama wajen sai da suka durfafa aka riga tserere da sojojin da masu laifi……

                       Chaina

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣0️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Tunda Gukunni ya fara bata labarin abubuwan da suka faru ita da jikokinsa wato yayan Anna kuma yayun Agaishat daidai lokacin da aka tafi massage din jikin Anna wace yanzu sosai jikin da sauki , suke dubansa da mamaki, 

Dama akoy mutane irin haka? 

Anmi, wato mahaifiyar Anna ta ce” wai kana nufin , Wardugugu dai general Wardugu ne ya auri Agaishat din,? Kuma ka ganta da idonka?

Gukunni ya yi murmushi ya ce” a irin halin da na ganta, ko mu iya walwalar da zamu iya bata kennan, 

Fatimata ta ce” wai wai wai rayuwa, yanzu Agaishanmu ce ta yi aure har ya rabu har ta kara samun wani da gagawa haka? Ku a birni ba ruwanku da kalar fatar mutun kennan?

Gukunni ya ce” wanninma da ta samu ko a cikin mutanen baban mutun ne, ba kun ga sojan da ya je tare da mahaifiyar tasa ba? Uwar rikon Agaishat din?

Gaishat ta zaro ido ta ce” eh eh, wani irin mutun mai cika waje da ido, tunda aka je da shi bai cika magana ba aman idan ya dago ya yiwa mutun duba daya sai ka nemi kallon me ya yi maka ka kimtsa zamanka,

Gukunni ya saki murmushi ya ce” to ko a ma.aikata haka yake, shi dai ne ya biya sadakin auren Agaishat million Arba.in!

Gaba dayansu sun girgiza, sun ji dadin lamarin kuma sun kara yarda Allahn da ya yi bawa, shi ya san me ya kunshe tatare da shi, Wai Agaishat dai Agaishat, itace haka ya sameta, abun alkhairi da kaf timiya ba.a taba kawowa wata y’a haka ba, kai ko a cikin agadez sai yayan sarke ke samun haka, 

Anmi ta ce” damuwana daya, ka ce bai jima da aure ba , kuma matarma batuba ce, fatan dai ya isa da gidansa, yana iya sakawa ko hanawa, 

Gukunni ya girgiza kansa kafin ya ce” ban ce ba idan baya nan, 

Idan kuwa baya nan ita jikar taki idan ta zauna kishiya ta cin mata ita ta gano,

Maganar idan yana nan da nake maki, ni na ga a idon jarumin ba lale ne ya yarda kuda ya taba fatar jikinta ba, 

Zai iya da su!

Ai kuwa Mariama ta mike ta aniya kada harshenta ta rangada budar buzaye, inda Anmi ta yi gagawar tarota tana tina mata asibiti suke fa, kar a zo a yi waje da su,

Mariama kuwa dariya kawai take, ta zauna tana duban yan uwanta ta ce” ban taba sannin inada kaka mai kudi ba, da yan timiya sun gayawa yan garinsu! Ban taba sannin Bakar Anna zata yi kudin aure ba , da na koya mata fito na fito!

Yanzu ko yaya? Ko ta bar rabewar idan an tabata? Ko ta bar lafewa ta dora kanta inda ta samu ta yi hawaye? Ko ta gane Allah kawai zata kaiwa kukanta, du ubanda ya tarota ta taro shi?

Gaishata ta kai hannunta ta buge bakin Mariama kafin ta girgiza kanta ta ce” Allah ya shirye ki, gwarama wannan likitan dake bibiyarki a bashi mu tataraki mu bar masa a nan mu daga abinmu dan har yanzu baki shiryu ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button